An samu wata mace da laifin kai wata yarinya 'yar Birtaniya zuwa Kenya don yi mata kaciya.
Amina Noor, mai shekara 39 ce, mutum na farko da aka samu da laifin taimaka wa wani wanda ba dan Birtaniya ba, don a yi wa mace kaciya.
Noor, daga yankin Harrow a arewa maso yammacin London, ta dauki yarinyar ne inda ta kai ta wani gida don yi mata irin wannan aiki na kaciya a 2006.
Ta fada wa babbar kotun hukunta manyan laifuka ta Old Bailey cewa, ana yin kaciyar ne saboda dalilai na al'ada kuma ita ma an yi mata kaciya lokacin da take karama.
Sai ranar 20 ga watan Disamba za a yanke wa Noor hukunci, wadda haifaffiyar Somaliya ce amma tana da shaidar zama 'yar Birtaniya.
Sai a shekara ta 2015 ne yarinyar - wadda a yanzu ta kai shekara 21 kuma ba za a iya fadar ko wace ce - ta shaida wa malamar makarantarsu cikin sirri cewa an yi mata kaciya, abin da ya sa aka sanar da 'yan sanda.
Bayan gudanar da gwaje-gwaje ne a asibitin koyarwa na University College a 2019, aka gano cewa gaba daya an cire wa yarinyar dan tsaka.
Da take bayar da shaida a zaman sauraron shari'ar, Noor ta yi ikirarin cewa ta fuskanci matsin lamba ne na ganin an yi yarinyar kaciya saboda al'ada.
Ta ce ita da wata matar ne suka dauki yarinyar a babur mai kafa uku, kuma aka ce mata ta tsaya a kofar wani gida.
Ta yi ikirarin cewa tsammaninta kawai shi ne za a dan rede gaban yarinyar ta yadda za ta dan zubar da jini.
Sai dai, masu shigar da kara sun ce masu taya alkali hukunci na iya tabbatar da cewa wadda aka yi karar ta kwan da sanin cewa kaciya za a yi - kuma ko dai hakan ya kunsa ko bai kunshi cire wa yarinyar dan tsaka ba ko haddasa mata wani nau'in rauni, wanda ba shi da wata manufa a likitance.
Mai shigar da kara Deanna Heer KC ta ce Noor ta sha musanta cewa barazana aka yi mata don lallai ta amince da yi wa yarinyar kaciya.
-
Mece ce kaciyar mata, a ina ake yi kuma me ya sa?
-
Wata likita na son a halatta kaciyar Mata