Sunak ya goyi bayan kiran a dakatar da rikicin Gaza don nuna jin ƙai

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, musamman kan yaƙin Isra'ila da Hamas.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma yanzu a madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Amurka ba za ta sauya matsayinta kan 'yancin 'yan Isra'ila da Falasɗinawa ba

    s

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Joe Biden ya ce Amurka ba za ta canza matsayin da aka san ta a kai ba, game da Isra'ila da al'ummar Falasdinawa, tun kafin 6 ga watan Oktoba, ranar da Hamas ta kai hari cikin Isra'ila.

    Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a gefen Firaministan Australia Anthony Albanese, Biden ya ce dole Isr'ila ''ta yi duk abin da za ta iya yi domin kare fararen hula''.

    Shugaba Biden ya ce ya kaɗu da jin rahotonnin yadda wasu da ya kira ''Yan kama-wuri-zauna masu tsattsauran ra'ayi'' ke far wa Falasɗinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    "Suna kai hare-hare kan Falasɗinawa a wuraren da suke da 'yancin zama. Ya kamata a dakatar da wannan", in ji Biden.

    Ya kara da cewa Amurka na goyon bayan Isra'ila wajen kare kanta daga hare-haren Hamas, kuma "za ta tabbatar Isra'ila ta samu abin da take buƙata don kare kanta daga waɗannan 'yan ta'adda. Wanna tabbas ne."

    Mista Biden ya ce Hamas ba ta wakiltar "mafi yawan Falasɗinawan Zirin Gaza ko ma a wani wuri da suke".

    Ya ci gaba da cewa "Hamas ba za ta ci gaba da fakewa a bayan Falasɗinawa fararen hula tana kai wa Isra'ila hare-hare ba".

  3. Wani hari ya faɗa kusa da asibiti a yanki mai aminci na Gaza, Rahoton wakilin BBC Rushdi Abualouf daga Khan Younis a Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An sha kai hare-hare ta sama a Khan Younis, da ke kudancin Zirin Gaza

    An kai wani gagarumin hari ta sama da misalin karfe 7:30 na yamma agogon Gaza a kan wani gini mai hawa uku, da ke da ratar mita 200 daga asibitin Nasar a Khan Younis.

    Harin ya ritsa da mutum 50 - wasu a ciki sun mutu, wasu kuma sun ji raunuka. Motocin daukar marasa lafiya da dama sun garzaya wurin don kai dauki.

    Khan Younis na cikin wuraren da rundunar sojin Isra'ila ta nemi mutane a Gaza da kuma arewacin zirin su fice zuwa kudanci.

    Wannan na nufin zai kasance da aminci amma a yau hukumomin yankin sun ce wani hari na uku cikin hare-hare ta sama da ake kai wa cikin dare ya far wa wurin.

    Kuma fiye da rabi na mutanen da aka kashe na wurin da ake kira "amintaccen sashe".

    Asibitin na faman ganin yadda zai kula da yawan mutanen da ke jinya. An rufe yankunan da aikinsu bai zama tilas ba ciki har da dakin wankin koda, a kokarin ganin an ririta man fetur din da ya yi saura.

    Ba mu da masaniya kan yaushe za a bari karin man fetur ya shiga Gaza. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa muna bukatar manyan motocin agaji 40,000. Zuwa yanzu mun samu kasa da mota 50 ne kawai.

  4. Udinese ta naɗa Cioffi sabon kocinta

  5. Barca ta haɗa maki tara a wasa uku a Champions League

  6. An kashe iyalan ɗan jaridan Aljazeera a Gaza

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    An nuna wakilin tashar Aljazeera kai tsaye a talbajin rungume da gawar matarsa da 'yarsa da kuma ɗansa a abin da tashar ta ce sun mutu ne sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza.

    Wa'el Al'dahdud ya ce iyalansa sun bar arewacin Gaza inda suka koma kudancin yankin domin cika umarnin da Isra'ila ta ba su na ficewa daga yankin.

    Abokin aikinsa Hoda Abdel-Hamid ya bayyana shi a matayin ɗan jarida mai bayar da bayyanai kan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza.

    Kawo yanzu da rundunar soji Isra'ila ba ta ce komai ba game da kisan iyalan ɗan jaridan.

    Tun da farko, jami'an lafiya a Gaza sun ce fiye da Falasdinawa 750, ciki har da ƙananan yara 344 ne suka mutu cikin kwana guda, sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza.

  7. An rantsar da sabon shugaban majalisar wakilan Amurka

    ,

    Asalin hoton, Reuters

    An rantsar da Mike Johnson, a matsayin sabon kakakin majalisar wakilan Amurka.

    A yau ne aka zaɓi mista Johnson mai shekara 51, wanda ɗan jam'iyyar Republican ne.

    Ya samu ƙuri'a 220, inda ya doke babban abokin karawarsa na jam'iiyar Demokrat Hakeem Jeffries, da ya samu ƙuri'a 209.

    Zaɓen ya kawo ƙarshe kwanaki 22 da majalisar wakilan ƙasar ta ɗauka ba tare da shugaba ba, tun bayan da aka tsige Kevin McCarthy mako uku da suka gabata.

    A siyasance ana kallon mista jihnson a matsayin cikakken mai ra'ayin riƙau, kuma mai goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Donald Trump.

    'Yan jam'iyyar Republican masu matsakaicin ra'ayi na ganin sa a matsayin mai ra'ayin tunkarar al'amura gwargwadon halin da suka bayyana kuma jagora mai nutsuwa wanda zai tabbatar da aiki da akidojin 'yan mazan-jiya a lokacin da yake ci gaba da zartar da dokoki

    "Yana ɗaya daga cikin mutanen da ke tare da kowa, kuma ana girmama shi" kamar yadda wani ɗan Republican a Colorado,Ken Buck ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta CNN.

    A gefe guda kuma 'yan jam'iyyar Dimokrat na fargabar cewa ya cika tsaurin ra'ayi.

    Sun kafa hujja da tarihin Johnson na kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a 2020.

  8. Za mu yi duk abin da ya dace don kuɓutar da mutanenmu - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, via Reuters

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasarsa na yin duk abin da ya dace domin kubutar da mutanenta da Hamas ta yi garkuwa da su.

    Mista Netanyahu na jawabi a wani taron manema labarai a birnin Tel Aviv.

    Ya kara da cewa Isra'ila na shirin mamayar Gaza ta ƙasa, to sai dai bai bayyana lokaci da yadda mamayar za ta kasance ba, yana mai cewa za a cimma hakan ne bayan tattaunawa.

    "Mun riga mun kashe dubban 'yan ta'adda, kuma yanzu muka fara," in ji Netanyahu.

  9. An rantsar da sanatan da ya maye gurbin Elisha Abbo

    s

    Asalin hoton, Amso Yahanna/Facebook

    Bayanan hoto, Sanata Amos Yohanna na jam'iyyar PDP ya maye gurbin sanata Abbo na APC

    Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da Amos Yohanna a matsayin sabon sanatan da ke wakiltar Adamawa da Arewa.

    Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin - wanda shi ne ya jagoranci zaman zaman majalisar na ranar Laraba - ne ya rantsar Yohanna mako guda bayan da kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke nasarar da Sanata Elisha Abbo na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen watan Fabrairu.

    Kotun ta tabbatar da nasarar Amos Yohanna na jam'iyyar PDP a lokacin da take yanke hukuncin.

    Yayin yanke hukuncin ranar 16 ga watan Oktoba, kotun ɗaukaka ƙarar ta umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC ta bai wa Yonanna takardar cin zaɓe a matsayin halastaccen zaɓaɓaɓen sanatan Adamawa ta A tarewa.

    d

    Asalin hoton, Amos Yohanna

    Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ne ya rantsa da Yohanna

    Kotun ɗaukaka ƙara ce ƙarshe a shari'ar zaɓen 'yan majalisar dattawa da na wakilai, saɓanin shari'ar gwamna da shugaban ƙasa da take ƙarewa a Ƙotun Ƙoli.

    Jim kaɗan bayan hukuncin na kotun ɗaukaka ƙara, Sanata Abbo ya zargi shugaban Majalisar Dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akpabio da hannu a soke nasarar tasa.

  10. Hotunan yadda mutane ke neman 'yan uwansu a Gaza

    Hotunan da muke samu daga Gaza a yau na nuna yadda mutane ke ci gaba da neman 'yan uwansu a cikin ɓaraguzan gine-gine da Isra'ila ke yi wa luguden wuta a Gaza.

    Tun da farko ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce fiye da Falasɗinawa 750 aka kashe ta hanyar hare-haren a cikin kwana guda.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    .

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Falasɗinawa na girka abinci a wata cibiyar hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Khan Younis
    ..

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wani mutum ke neman gawarwaki da mutanen da suka maƙale a cikin ɓaraguzan wani gida
  11. Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Bayanan hoto, Shugaba Tinubu ya buƙaci sabbin kwamishinonin su gudanar da ayyukansu bisa doka

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe a wasu jihohin ƙasar tara.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ta ce Tinubu ya amince da naɗin sabbin kwamishinonin na tsawon wa'adin shekara biyar.

    Sanarwar ta ce naɗin kwamishinonin sai ya samu amincewar majalisar dattawan ƙasar, bayan tantance su.

    Sabbin kwamishinonin sun haɗar da:

    Mista Isah Shaka Ehimeakne - Kwamishinan zaɓe na jihar Edo.

    Mista Bamidele Agbede - Kwamishinan zaɓe na jihar Ekiti.

    Mista Jani Adamu Bello - Kwamishinan zaɓe na jihar Gombe.

    Dakta Taiye Ilayasu - Kwamishinan zaɓe na jihar Kwara.

    Dakta Bunmi Omoseyindemi - Kwamishinan zaɓe na jihar Lagos.

    Alhaji Yahaya Bello - Kwamishinan zaɓe na jihar Nasarawa.

    Farfesa Mohammed Yalwa - Kwamishinan zaɓe na jihar Niger.

    Dakta Anugbum Onuoha - Kwamishinan zaɓe na jihar Rivers.

    Mista Abubakar Fawa Dambo - Kwamishinan zaɓe na jihar Zamfara.

    Shugaba Tinubu ya yi kira ga sabbin kwamishinonin da su nuna ƙwarewa a aikinsu tare da bin doka da oda wajen gudanar da ayyukansu.

    Domin tabbatar da shirya sabbin sahihai kuma ingantattun zaɓuka da ba su da rikici a jihohinsu.

  12. An yi jana'izar uwa da 'ya'yanta mata biyu da Hamas ta kashe

    Sisters Yahel and Noiya with their mother Lianne
    Bayanan hoto, 'Yan'uwan juna biyu Yahel da Noiya tare da mahaifiyarsu Lianne

    Wannan rana ce ta makoki.

    A gefen wasu bishiyoyin ruman cikin wani lungu mai shiru wanda ya saba da yanayin makokin rasuwarsu, an haka kaburbura guda uku na mahaifiya Lianne da 'ya'yanta mata biyu: Noiya and Yahel Sharabi.

    Dangin da Hamas ta yi kokarin shafe su daga doron duniya.

    Sabani tsakanin wannan muhalli da wani hoto na mahaifiya Lianne da ke murmushi lokacin da ta sa hannuwa ta dafa kafadun 'ya'yanta 'yan mata biyu, wanda aka dauke watanni kalilan da suka wuce lokacin da suke murnar bikin Kibbutz Be'eri, a kudancin Isra'ila, ba a rufe yake ba.

    Hatta gawawwakinsu, ba su iya komawa gida ba. An daidaita Be'eri - wurin da aka yi kisan kiyashi. An kashe dumbin mutane, duk da haka wadanda ke raye ba za su iya binne makusantansu a can ba.

    Don haka ake binne wadannan dangi, 'Yan Isra'ila daga asalin Birtaniya a wata makabarta da ke da nisan kimanin kilomita 40 daga iyaka da Gaza.

    Ahalin Sharabin, ba su iya samun kwanciyar hankali ba. Mahaifin 'yan matan Eli har yanzu ba a gan shi ba. An kuma sace kawunsu, Yosi. A nan yara ba za su iya kukan rashin mahaifansu ba. Iyaye ba za su iya makokin 'ya'yansu ba.

    A Isra'ila, daruruwan mutane ne suka taru don jana'izarsu inda masu makokin da yawa suka sanya riga mai tambarin: "An yi wa Lianne, Noiya da Yahel kisan gilla. A dawo mana da Eli da Yosi yanzu."

    'Yan mata suna kukan rashin kawayensu Yahel da Noiya, sun ma kasa fahimtar abin da ya faru da dangin nan.

    Mutuwa da bata da kuma sacewa. Mugun al'amari a wannan rana, ga wannan kasa, da kuma wannan dangi.

    Israel victims funeral
    Bayanan hoto, Mahaifin Noiya da Yahel har yanzu ba a gan shi ba, an kuma sace kawunsu Yosi
    Israel Funeral
    Bayanan hoto, Masu makoki da dama sun sanya riguna dauke da sunaye da hotunan dangin Sharabi
    Israel casualities Funeral
    Bayanan hoto, Daruruwan mutane ne suka taru don jana'izar Lianne da Noiya da kuma Yahel Sharabi
    Israel casualities Funeral
    Bayanan hoto, Kawun 'yan matan ya bayyana kalamin "karyewar zuciya" da dangin ke amfani da ita wajen bayyana mutuwar

    Lianne ta je Isra'ila ne daga Bristol tun tana 'yar shekara 19 don aiki a kibbutz. Daga nan ta gina rayuwarta a can kafin Hamas ta yanke shawarar kwace hakan daga gare ta da kuma 'ya'yanta.

  13. Ana gudanar da zanga-zangar neman agajin girgizar ƙasa a Morocco

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Ɗaruruwan mazauna garin Amizmiz na ƙasar Maroko sun yi zanga-zangar adawa da hukumomin yankin, makonni bayan da wata mummunar girgizar ƙasa ta lalata gidajensu.

    Amizmiz, mai tazarar kilomita 55 daga kudancin Marrakesh, yana ɗaya daga cikin yakunan da girgizar ƙasar 8 ga Satumba ta fi muni.

    Girgizar ƙasar dai ita ce mafi muni da ta afku a Maroko cikin sama da shekaru 60, inda ta kashe mutane kusan 3,000 tare da jikkata wasu dubbai.

    Mazauna yankin na zargin hukumomin yankin da jinkirta agaji da kuma yin watsi da su.

    Bayan girgizar ƙasar, hukumomi sun sanya iyalai da suka rasa matsugunansu a sansanonin tantuna, tare da alkawarin ba da tallafin kuɗi don taimakawa wurin sake gina gidajensu.

    Sai dai a yanzu masu zanga-zangar sun ce ba za su iya ci gaba da zama a sansanonin ba ganin yadda yanayi ke ƙara taɓarɓarewa, inda ruwan sama da iska suka afkawa yankin da kuma lokacin sanyi da ke gabatowa.

    • Malamar da girgizar ƙasa ta halaka dukkanin ɗalibanta a Moroko
    • 'Kowane dare sai na yi mugayen mafarkai kan girgizar-ƙasa'
  14. An yi wa Robertson tiyata a allon kafaɗa - Klopp

  15. Sunak ya goyi bayan kiran a tsagaita saboda jin ƙan ɗan'adam a rikicin Gaza

    UK lawmaker Mhairi Black
    Bayanan hoto, Mhairi Black ta ruwaito Majalisar Dinkin Duniya na cewa "cikin dare za a dauke" lantarki kuma ta sabunta kiraye-kirayen a tsagaita wuta

    Firaminista Rishi Sunak ya nuna goyon bayansa ga "taƙamaiman tsagaitawa" a yaƙin Isra'ila da Hamas, inda ya jaddada kiraye-kirayen ƙasashen duniya na neman bari a kai ƙarin kayan agaji zuwa Gaza.

    Rishi Sunak ya fada wa 'yan majalisar dokokin Birtaniya cewa akwai buƙatar wani "yanayi amintacce" a yankin don kai kayan agaji da kuma fitar da 'yan Birtaniya daga Gaza.

    Sai dai Firaminista bai goyi bayan tsagaita wuta ba, don kuwa hakan zai amfani ƙungiyar Hamas ne, kamar yadda mai magana da yawunsa ya ce.

    Kalamansa sun zo ne bayan kiraye-kirayen a dakata bisa dalilan jin ƙai daga Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma Kanada.

    Firaministan ya ce Birtaniya ta tattauna batun da abokan ƙawance a Majalisar Dinkin Duniya, yayin da ya ba da sanarwar cewa jirgin rundunar sojojin saman ƙasar ya tashi zuwa Masar da tan 21 na kayan agaji.

    Kiraye-kirayen ƙasashen duniya da ke neman hanyar kai kayan jin ƙai Gaza na daɗa ƙarfi, yayin da hukumomin agaji na Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin cewa suna daf da "durƙushewa".

    Israel ta ƙaddamar da luguden bama-bamai ne a kan Hamas - wadda Isra'ila da Birtaniya da Amurka da sauran manyan ƙasashe masu ƙarfin iko suka ayyana ta a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda - don maida martani ga wani harin tsallaken kan iyaka da ba a taba ganin irinsa ba ranar 7 ga watan Oktoba.

    Akalla mutum 1,400 ne aka kashe yayin da aka yi garkuwa da mutum 222 a harin na Hamas.

    Ministan lafiya na yankin Gaza da kungiyar Hamas ke gudanarwa ya ce an kashe kusan mutum 5,800 a yankin tun daga wancan lokaci.

  16. Dattijuwa 'yar Isra'ila da Hamas ta saki ta yi musabaha da wadanda suka kama ta

    Bayanan bidiyo, Dattijuwa 'yar Isra'ila da Hamas ta sako ta yi musabaha da wadanda suka kama ta

    Wata dattijuwa wanda Hamas ta rike tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, ta yi musabaha da daya daga cikin 'yan bindigar da suka kama ta, kuma ta ce masa shalom - ka zama lafiya a harshen Hibiru.

    Yocheved Lifschitz, mai shekara 85, mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya ce. Ita da mijinta Oded, wanda har yanzu Hamas ke ci gaba da rikewa, sun shafe tsawon shekaru suna taimakawa Falasdinawa marasa lafiya a Gaza wajen kai su asibiti.

  17. Shugaban MDD ya ce an yi wa kalamansa 'mummunar fassara'

    Shugaban MDD Antonio Guterres

    Asalin hoton, AFP

    Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi ƙarin haske kan kalamansa da suka janyo ce-ce-ku-ce kan rikicin da ke gudana tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa.

    Ya bayyana cewa 'mummunar fasarar' aka yi wa kalmansa.

    Guterres ya ce ya kaɗu matuka da yadda ake bayyana kalaman da ya yi a kwamitin tsaro, inda ya ce yana da muhimmanci a gane cewa harin da ƙungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba ba 'haka kawai' ne ya faru ba.

    Ya ce kalaman nasa ''ba su halasta ayyukan ta'addancin da Hamas ta aikata ba, kuma ya yi Allah wadai da "mummunan ayyukan ta'addanci" na Hamas a Isra'ila.

    Ya kuma yi magana game da korafe-korafen al'ummar Falasdinawa, amma ya ce ba za su iya ba da hujjar munanan hare-haren Hamas ba.

    Ya ce yana da muhimmanci a daidaita lamarin saboda mutunta waɗanda suka rasa rayukansu da kuma iyalansu.

  18. Najeriya na fuskantar ƙarancin malamai 950,000 - Tahir Mamman

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Najeriya na fama da ƙarancin malamai 950,000 da kuma ƙarancin azuzuwa 20,000 daidai lokacin da ƙasar ke shirin yin nazari tare da inganta manhajar karatu na manyan makarantu domin bunƙasa fasahar ƙere-ƙere na yara da kuma shirya su don shiga harkar kirkire-kirkire a nan gaba.

    Ministan Ilimi, Tahir Mamman ya bayyana haka yayin wani taro kan walwalar yara a wajen taron tattalin arzikin Najeriya karo na 29 a ranar Talata.

    Mamman ya bayyana cewa a halin yanzu ilimin lissafi da sauran darussa da ake koyarwa a makarantun firamare ba su isa shirya yaran Najeriya kan abubuwan da suke faruwa a yau ba.

    Mamman ya jaddada buƙatar samar da ingantattun hanyoyin koyo da ababen more rayuwa a makarantun firamare, da kuma shirin gwamnati na haɗa kai da gwamnonin jihohi waɗanda da ke da alhakin samar da kuɗaɗe don cimma wannan burin.

    • Ranar Malamai ta Duniya: 'Darajar malanta kullum zubewa take a Najeriya'
    • Kotu ta dakatar da El- Rufai daga korar malaman Firamare
  19. Birtaniya ta tura jirgi ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin saman Burtaniya ɗauke da tan 21 na kayan agaji zuwa Gaza na kan hanyarsa ta zuwa Masar, kamar yadda ma'aikatar tsaron ƙasar ta sanar.

    Jirgin na Royal Air Force C-17 yana ɗauke da akwatin bayar da agajin gaggawa 76,800 da aka bayar da gudummawa daga tarin magungunan ƙasar, da kuma na'urorin tace ruwa 1,350 da fitulu masu aiki da hasken rana 2,560.

    Kayan agajin na cikin wani ɓangare na tallafin fan miliyan 30m ga al'ummar Gaza wanda Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya sanar a farkon wannan makon kuma ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta Masar za ta rarraba a cewar ma'aikatar tsaro na Burtaniya.

    • Musulmai da Yahudawan Birtaniya na fargabar alaƙarsu saboda yaƙin Gaza
    • Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza
  20. 'Isra'ila za ta daina bai wa jagororin Majalisar Ɗinkin Duniya biza'

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Tun daren jiya ake ta ce-ce-ku-ce, bayan da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya ce harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba wanda aka kashe sama da mutane 1,400 a Isra'ila 'ba haka kawai' ya faru ba.

    Kalaman sun jawo tsauraran kalamai daga ministan harkokin wajen Isra'ila, wanda ya ce "babu dalilin da zai haifar da irin wannan kisan kiyashi".

    Yanzu Isra'ila ta ce za ta ki bayar da takardar shiga ƙasar ga manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya.

    Jakadan Isra'ila a Majalisar Gilad Erdan ya shaida wa kafafen yaɗa labaran Isra'ila cewa "Muna bukatar mu bai wa MDD mamaki."

    Ya ce shugaban Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kai Martin Griffiths ya so zuwa Isra'ila - kuma an hana shi.

    "Ba zai iya zuwa nan yankin ba, kullum hukumominsu na buƙatar kawo sabbin mutane, musamman a irin wannan lokacin, ba za a amince masu ba."