Najeriya ta yi nasara a ƙarar da ta ɗaukaka kan wani hukunci da ya nemi ta biya diyyar dala biliyan 11 ga wani kamfanin ƙasashen waje, bayan rushewar wata kwangilar shimfiɗa bututun iskar gas.
Kamfanin P&ID mai hedkwata a Virgin Islands na Birtaniya ne ya kai Najeriya ƙara, a kotun sasanta rikicin kasuwanci, inda ya nemi diyyar kudin da suka kai kashi ɗaya cikin uku na asusun ajiyar ƙasashen wajen Najeriya.
Mai shari'a Robin Knowles ya ce ya karɓi bahasin ƙalubalantar hukuncin kotun baya da Najeriya ta yi, a wani hukunci da ya yanke ranar Litinin.
"Ban amince da dukkan zarge-zargen da Najeriya ta yi ba," alƙalin ya faɗa a hukuncin nasa. Sai dai ya ƙara da cewa hukuncin kotun sasanta rikicin kasuwanci "an same shi ne ta hanyar damfara, kuma hanyar da aka bi, ta saɓa da manufar aikin gwamnati".
A shekara ta 2010 ne, Najeriya ta bai wa kamfanin Process & Industrial Developments (P&ID) kwangilar aikin ginawa da gudanar da wata tashar sarrafa iskar gas tsawon shekara 20 a kudancin kasar, a wani ɓangare na wani babban shirin haƙo ɗumbin arziƙin iskar gas da Allah ya hore mata.
Sai dai bayan rushewar yarjejeniyar, kamfanin P&ID ya garzaya gaban kotun sasanta rikice-rikicen kasuwanci da ke London a 2017, wadda ta yanke hukuncin cewa Najeriya ba ta da gaskiya a batun, kuma ta biya kamfanin dala biliyan 6.6 na asarar da ya yi.
Kuɗin dai ya yi ta ƙaruwa har zuwa sama da dala biliyan 11, saboda kuɗin ruwa.
Kiyasi na cewa kuɗin ya ninka har sau 10 a kan kasafin kudin Najeriya na fannin lafiya na 2019.
Lauyoyin Najeriya sun ce ƙasar ta tsinci kanta ne a cikin "wata maƙarƙashiyar cin hanci da damfara" daga kamfanin P&ID, wanda suka ce ya bayar da toshiyar baki ga manyan jami'an gwamnati don samun kwangilar.
Daga nan kuma sai ya riƙa bayar da rashawa ga lauyoyin ƙasar don samun takardun sirri na hukuma a lokacin shari'ar.
P&ID ya musanta cewa ya samu kwangilar ta hanyar ba da toshiyar baki, ko ya yi ta bayar da cin hanci ga lauyoyin Najeriya a lokacin sauraron shari'ar, inda ya ɗora alhakin rushewar yarjejeniyar iskar gas ɗin a kan rashin ƙwarewar hukumomi da ke da alhakin tafiyar da shari'ar.
-
'Ba mu ci nanin ba, saboda haka nanin ba za ta ci mu ba'
-
Sabuwar gardama ta kaure tsakanin PDP da APC kan hukuncin kotun zaɓe