Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hari kan asibiti ya kashe ɗaruruwan 'yan Gaza, Isra'ila ta musanta hannu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage, Umar Mikail, Mukhtar Adamu Bawa and Haruna Kakangi

  1. Da gaske ne gwamnatin Abia za ta tayar da kasuwar dabbobi ta Lokpana?

    Gwamnatin jihar Abia da ke kudancin Najeriya ta musanta zargin da aka yi mata na kokarin korar al'ummar arewa daga jihar bayan yunurinta na sauya fasalin kasuwar dabbobi ta Lokpana da ke kan hanyar umuahia zuwa Aba, a jihar.

    A ranar Litinin ne shugabannin kasuwar ta Lobbanta da ke ƙaramar hukumar Umunneochi suka gana da manema labaru a birnin Kaduna, inda suka buƙaci shugaban ƙasa da mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya su tsoma baki domin dakatar da gwamnatin jihar daga shirinta na tayar da kasuwar.

    Sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta ba su mako biyu su tashi daga kasuwar duk kuwa da cewa sun kasance masu bin doka da oda.

    Sai dai a cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun sakataren yaɗa labarun gwamnan jihar, Kazie Uko, ta ce batun sauya fasalin kasuwar ya taso ne bayan wasu rahotannin tsaro da suka tabbatar da cewa kasuwar ta kasance maɓuya ga ƴan fashi da masu garkuwa da mutane a cikin shekarun da suka gabata.

    A cikin wani bayani da ya yi wa manema labaru ranar Litinin, mai bai wa gwamnan jihar shawara kan tsaro, Navy Commander Macdonald Ubah, mai murabus, ya ce sauran ayyukan laifi da ake zargin ana aikatawa a kasuwar sun haɗa da sayar da sassan jikin bil'adama da kuma faɗace-faɗace.

    Ya ƙara da cewa ana amfani da kasuwar wajen karɓar kuɗin fansa na mutanen da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Uturu zuwa Umunneochi.

    Ya ce wannan lamari ne ya sanya gwamnatin jihar ta ɗauki matakin rushe gidajen mata masu zaman kansu da rumfunan da aka gina ba bisa tsari ba a kasuwar.

    Sanarwar gwamnatin jihar ta ce matakin da ake son a ɗauka shi ne kawar da wuraren kwana a kasuwar tare da mayar da ita wadda za ta rinƙa ci da rana kawai.

    Ta ƙara da cewa kuma gwamnati ba za ta janye aniyar tata ba ta sauya fasalin kasuwar.

    Sanarwar ta kuma musanta zargin da ake yi na cewa gwamnatin jihar na ƙoƙari ne wajen korar al'ummar arewa daga jihar.

  2. Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza

  3. MDD ta gargaɗi Isra'ila kan yiwuwar aikata laifukan yaƙi

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake yin kiran cewa a bai wa ƙungiyoyin agaji damar shiga Gaza, tare da gargaɗin cewa akwai yiwuwar aikata laifukan yaƙi.

    Mai magana da yawun hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Ravina Shamdasani, ta ce ƙungiyar ta damu matuka kan umarnin da sojojin Isra'ila suka bayar na cewa Falasɗinawa su fice daga arewacin Gaza zuwa kudanci, inda ta ce hakan zai iya zama kamar 'tirsasa' fararen hula - wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

    Idan aka yi imanin cewa wata ƙasa ta aikata laifin yaki a lokacin rikici, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) za ta iya duba lamarin - FalasƊinawa mambobi ne a kotun, amma Isra'ila ba ta ciki.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, Shamdasani ta ƙara da cewa dole ne a yi bincike kan hare-haren da ake kai wa fararen hula - yayin suke ƙoƙarin tserewa daga yankunan Gaza.

    Ta kuma yi kira da a saki dukkan mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su cikin gaggawa ba tare da wani sharaɗi ba, inda rahotannin daga Isra'ila suka nuna cewa ana tsare da kusan mutum 199.

    • Mene ne laifukan yaki kuma ko za a iya tuhumar Putin kan Ukraine?
    • ICC ta bukaci a binciki laifukan yaki da ake zargin Isra'ila a Gaza
  4. Najeriya ta kaddamar da shirin ba da tallafin kudi ga magidanta miliyan 15

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15, wanda hakan na cikin manufofinsa da aka yi wa laƙabi da 'kyakkyawan fata'.

    Tinubu ya kaddamar da shirin ne a yau Talata a bikin ranar kawo karshen talauci ta duniya, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Tinubu ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin kaddamar da shirin.

    A jawabinsa na bikin samun ƴancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 2023, shugaban ya sanar da cewa shirin ba da tallafin kuɗin, zai fi mayar da hankali kan taimakawa marasa galihu.

    Magidantan da iyalansu sun kai yawan ƴan Najeriya miliyan 62, a cewar ministar ba da agaji, Betta Edu.

    Ta ce za a bai wa kowane magidantci naira 25,000 har na tsawon wata uku, wanda ya kai naira 75,000.

    Ministar ta kuma ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da wani tsarin ba da tallafi mai suna 'Iya Loja Funds' wanda zai samarwa masu ƙananan sana'o'i bashin naira 50,000 kowanne.

    Waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da ministar ma'aikatar ba da agaji rage talauci Dr Betta Edu, ministan kuɗi, Wale Edun, wakilin bankin duniya na ƙasashe, Shubham Chaudhuri, shugaban ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale da sauran manyan baki.

    • Tambayoyin da aka fi yi game da shirin rage raɗaɗin talauci a Najeriya
  5. 'Zimbabwe na rasa malamai 300 a kowane wata'

    Babbar ƙungiyar malamai a Zimbabwe ta yi kiyasin cewa ƙasar na rasa malamai 300 a kowane wata yayin da suke balaguro zuwa ƙasashen ketare domin samun rayuwa mai inganci.

    Shugaban ƙungiyar malaman, Sifiso Ndlovu, ya ce babban dalilin da ya sa malaman ke barin ƙasar shi ne rashin albashi mai kyau idan aka kwatanta shi da na takwarorinsu a kudancin Afrika.

    Ya faɗa wa shirin BBC Newsday cewa albashin da ake biyan malamai bai taka kara ya karya ba, musamman ma idan aka duba halin matsin tattalin arziki da ƙasar ke fama da shi, sai dai ya ce ƙasar za ta yi duk abin da ya kamata don janyo hankalinsu su dawo gida.

    Ya ce abin da ake biyan malami bai fi $350 ba a wata.

    "Masu karatu a Zimbabwe na rasa ƙwararrun malamai waɗanda za su koyar da su don samun makoma mai kyau," in ji Sifiso.

    Ya kuma ce tsarin da kasafin kuɗin ƙasar ke da shi bai ba da damar a ɗauki malamai da yawa ba da ƙasar ke buƙata.

  6. Sabbin hotunan halin da ake ciki a kudancin Gaza

    Mutane a kudancin Gaza na ci gaba da sake neman waɗanda ba a gani ba cikin ɓaraguzan gini a yau Talata, bayan hare-hare ta sama na cikin dare da aka kai biranen Khan Younis da Rafah suka faɗa kan wasu gine-gine.

    Hukumomin bayar da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce yankin na cikin buƙatar agajin jin kai, a daidai lokacin da ake samun ƙarancin kayayyakin amfani na yau da kullum. Ga wasu sabbin hotuna na yadda yanayi yake a can.

  7. An gano gawawwaki 47 a hatsarin kwale-kwale a Kongo

    An gano gawawwaki 47 a kogin Kongo, yayin da ake ci gaba da aikin ceto bayan kifewar kwale-kwale a karshen mako, a cewar Marc Ekila, ministan sufuri a ƙasar.

    Ministan a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, ya ce hatsarin kwale-kwalen ya faru ne sakamakon ɗaukar mutane fiye da ƙima da kuma tuki cikin dare, wanda dokoki suka haramta.

    Ya yi wannan jawabi ne a karon farko a wani taron manema labarai da aka watsa ta gidan talbijin a daren ranar Litinin, kwanaki biyu bayan kifewar jirgin ruwan.

    Jirgin ya taso ne daga birnin Mbandaka da ke yammacin ƙasar inda ya kara gaba zuwa cikin dajin ƙasar ta Kongo a lokacin da lamarin ya faru.

    Mista Ekila ya ce ana gudanar da bincike kuma za a hukunta waɗanda aka samu da hannu a kifewar jirgin.

    Zuwa yanzu, ba a kama mai kwale-kwalen ba - wanda ba ya cikin kwale-kwalen a lokacin da ya kife - da kuma wani mutum guda.

    A cewar ministan, a wannan shekarar kaɗai an samu aukuwar kifewar jiragen ruwa 88 a ruwan ƙasar ta Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

  8. Shugaban gwamnatin Jamus na kan hanyarsa ta zuwa Isra'ila

    Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, na kan hanyarsa ta zuwa Isra'ila a yau Talata, domin ganin an tattauna wajen shawo rikicin daga yaɗuwa.

    Daga bisani kuma zai wuce zuwa Masar a cikin makon nan.

    "Yana da muhimmanci nuna goyon baya ta ga Isra'ila," in ji Olaf Scholz a wani taron manema labarai a lardin Jordan.

    Ya kuma ce akwai buƙatar a samar da wata kafa ta kai taimakon agaji a Gaza.

  9. Me ya sa Masar ta ƙi buɗe mashigar Rafah ga Falasɗinawa?

    A tsawon shekaru Masar ta sanya dokoki masu tsauri kan shige da fice ta mashigar Rafah da ke kan iyakarta da Zirin Gaza.

    Lamarin ya kai ga cewa Falasɗinawa da yawa na zargin Masar ɗin da iza wutar ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa Gaza tun bayan da Hamas ta karɓi iko da yankin a 2007.

    Sai dai lamarin ya fi alaƙa ne da batun tsaro a yankin Sinai na arewaci, inda dakarun Masar suka daɗe suna artabu da mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda.

    Sai dai jan ƙafar da Masar ke yi wajen buɗe mashigar a wannan lokaci ba tare da bayar da tartibiyar hujja ba da alama saboda guje wa tuɗaɗar Falasɗinawa masu ɗinbin yawa ne, waɗanda ke son ficewa daga Gaza.

    Masar ba ta so ta taka rawa a wani mataki da zai iya haifar da mazauni na dindindin ga dubban ɗaruruwan Falasɗinawa da ke son barin Gaza.

    Sai dai akwai yiwuwar za ta ƙyale ƴan ƙasashen waje da kuma Falasɗinawa masu takardar zama ƴan wasu ƙasar damar ficewa, bisa sharaɗin cewa za a bar kayan agaji su shiga Gaza.

    Idan har ana buƙatar wani abu fiye da haka, da yiwuwar Masar ta sa ran samun la'ada domin tallafa wa tattalin arziƙinta wanda ke cikin ƙangi.

  10. Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar halasta auren jinsi a Indiya

    Kotun Koli a ƙasar Indiya ta ki amincewa da buƙatar halasta auren jinsi ɗaya, sai dai ta amince ƴan luwaɗi da maɗigon su yi tarayya da juna.

    Alkalin alkalan ƙasar ya ce dokokin da suka shafi daidaiton haƙƙi ne na majalisar dokoki. Sai dai kotun ta buƙaci gwamnati ta sake duba dokar domin masu aure jinsi su samu ƴancin yin tarayya.

    Masu auren jinsi da dama ne suka shigar da ƙara a gaban kotun inda suka ce rashin yin aure ya keta ƴancinsu da tsarin mulkin ƙasar ya ba su.

    Masu fafutuka da dama (da suka taru a wajen kotun) sun ce sun ji takaicin hukuncin.

    Gwamnati karkashin jagorancin jam'iyyar BJP mai kishin addinin Hindu, da shugabannin addinai suna adawa da auren jinsi ɗaya.

    Sun ce ba za su amince da auren jinsi ɗaya ba saboda ya saɓa wa al'adun Indiya.

  11. Gwamnatin Sokoto ta kafa kwamitin samar da ƴan sintiri

    Gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya amince da kafa kwamitin samar da ƴan sintiri a jihar.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abubakar Bawa ya fitar, ta ce kwamitin mai mambobi 25, za ta ba da shawara kan yadda za a ɗauki ƴan sintirin da kuma ba su horon da ya kamata.

    Sanarwar ta ce kwamitin zai kuma wayar da kan al'ummomi a ƙananan hukumomi 23 na faɗin jihar kan batun ɗaukar ƴan sintiri don taimakawa wajen samar da tsaro.

    A makon da ya gabata ne, gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da rundunar ƴan sintiri da ta yi wa laƙabi da Community Watch Corps a turance domin magance matsalar tsaro a sassan jihar.

    Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya dai na ƙara dugunzuma al’ummar yankin, al’amarin da ya tilasta wa hukumomi suka fara ɗibar matasa domin yin aiki tare da jami’na tsaro wajen yaƙi da ƴan bindiga.

    • Katsina ta ba wa ƴan banga makamai don yaƙi da ƴan bindiga
    • Yadda ƙungiyar Ansaru ke jan matasa a Birnin Gwari
  12. MDD ta yi watsi da shawarar Rasha na kiran a tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Falasɗinu

    Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi watsi da shawarar Rasha na kiran a tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

    Jakadan Rasha a Majalisar, Vassily Nebenza, ya ce ƙasashen yamma sun dakile yunkurin ƙasarsa na kawo karshen zub da jinin da ake yi.

    Ya ce “ina mai takaicin cewa kwamitin sulhun ya yi watsi da shawararmu sannan kuma ya nuna son kai wajen yanke hukunci a kan abin da ya kamata ayi domin shawo kan rikicin da ake tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Jakadiyar Amurka a Majalisar, Linda Thomas-Greenfield, ta ce kin sukar Hamas da kudurin ya yi munafunci ne kuma abin ban haushi ne da bashi dawata madogara.

    Sannan kuma an jinkirta duba wani kudurin mai adawa da haka wanda Brazil ta gabatar har zuwa yau Talata.

  13. Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Najeriya

  14. Ba ni da hannu a ƙwace nasarar Sanata Ishaku Abbo - Akpabio

    Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi watsi da zargin da Sanata Elisha Abbo ya yi cewa yana da hannu a ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara ta yi a ranar Litinin.

    Da yake magana da manema labarai, mai magana da yawun shugaban majalisar ta dattawa, Eseme Eyiboh, ya ce ba shi da hannu a hukuncin da kotun ta yanke.

    Eyiboh ya ce "Abin takaici ne idan Abbo ya yi zargin cewa da hannun Akpabio a ƙwace nasararsa. Yana neman wanda zai ɗora wa lafi ne kawai.

    "Kotun Ɗaukaka Ƙara a ƙasar nan na yanke hukunci ne bisa tanadin dokar zaɓe da kuma irin hujjojin da masu ƙara suka gabatar. Shugaban majalisar dattawa ba shi da wani dalili na yi wa wani ɗan majalisa bita-da-kulli."

    Tun da farko dai, bayan ƙwace nasararsa da kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta yi, Sanata Abbo ya yi zargin cewa Godswill Akpabio na da hannu a lamarin.

    Hukuncin na nufin Mista Abbo ya bar Majalisar Dattawan Najeriya ke nan kasancewar ita ce kotun ƙarshe da ke da hurumin sauraron ƙorafin zaɓen 'yan majalisa - ma'ana babu sauraron ɗaukaka ƙara.

    • Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ƙwace kujerar Sanata Ishaku Abbo
    • Wane ne Godswill Akpabio, sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya?
  15. Ƙungiyar ƙasashen Musulmai za ta yi taron gaggawa kan rikicin Gaza

    Ƙungiyar ƙasashen Musulmai za ta yi taron gaggawa kan rikicin Falasɗinawa.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce za a gudanar da taron ne ranar Laraba a birnin Jeddah.

    Taron zai kuma tattauna kan irin barazanar da rikicin yake da shi ga fararen hula a Gaza.

    Ƙungiyar ta OIC za ta duba buƙatar ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin rikicin bai yaɗu zuwa makwabta ba, da kuma tabbatar da ganin cewa zaman lafiya ya ɗore a yankin.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza
  16. Sojojin Isra’ila sun ce sun kai harin sama a Lebanon

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare hare ta sama Lebanon kan ƙungiyar Hezbollah.

    Rundunar ta ce ta kai harin ne kan kayayyakin soji a wani martani na hare haren da ƙungiyar Hezbollah ke kai mata.

    Kazalika rundunar ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda ta lalata wasu gine-gine.

    Harin ya zo ne sa'o’i bayan ministan harkokin wajen Iran ya yi gargaɗin cewa Isra'ila za ta fuskanci munanan hare-hare daga sauran ƙungoyin da ke yankin idan ba ta daina abin ta ke ba.

    Tun da farko Isra'ila ta ce ta kwashe gwamman mutanen da ke kusa da iyakar Lebanon.

    • Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari
    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
  17. Biden zai kai ziyara Isra'ila a ranar Laraba

    Shugaba Biden zai kai ziyara Isra'ila a gobe Laraba, a wani ɓangare na nuna goyon baya ga ƙasar a yayin da ta ke ci gaba da yaƙi da Hamas.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ne ya sanar da ziyarar shugaban bayan wata tattaunawa cikin dare da suka yi a Tel Aviv.

    Ya ce za a faɗa wa shugaban irin dabarun da Isra'ila ke amfani da su, da kuma yadda za a takaita hare haren da ake kai wa kan fararen hula.

    Mr Blinken ya kuma ce shugabannin Isra'ila sun amince a samar da wani tsari da zai bayar da damar shigar da kayan agaji cikin Gaza.

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Mulkin mallakan da ya hargitsa rayuwa a Gabas ta Tsakiya
  18. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Talata.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Ahmad Tijjani Bawage.

    Ku kasance da mu domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma faɗin duniya, musamman ma yaƙin Isra'ila da Falasɗinu.