Hari kan asibiti ya kashe ɗaruruwan 'yan Gaza, Isra'ila ta musanta hannu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage, Umar Mikail, Mukhtar Adamu Bawa and Haruna Kakangi

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi ba don labarai sun ƙare ba. Kuna iya duba sauran shafukanmu a wannan dandali don samun wani sabon labari.

    Kazalika, idan kuka duba ƙasa za ku ga labaran da muka wallafa a yau musamman game da halin da ake ciki a Zirin Gaza da Isra'ila.

    Umar Mikail da Mukhtar Bawa ne ke muku fatan alheri.

  2. Me ya sa har yanzu Isra'ila ba ta ƙaddamar da samame ta ƙasa kan Gaza ba

    Dakarun Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar soja ba ta sanar da lokacin ƙaddamar da hari, kuma ta Isra'ila ma ba za ta yi hakan ba.

    Wani kakakin rundunar ya faɗa a ranar Talata cewa: "Ba za mu bayyana shirinmu ba - za mu iya yin wani abu daban."

    Sai dai Isra'ilar ta ce ta tattara dakarunta, kuma an tsara tankunan yaƙi da makaman atilare a mazaunansu kusa da iyakarta da Gaza, da ma sauran iyakoki.

    Tabbas bayanan da rundunar ke yi na nuna cewa nan gaba kaɗan za ta ƙaddamar da harin. Amma kuma jibge dakaru tsawon lokaci ba tare da gwabza yaƙi ba zai iya shafar shirinsu da kuma karsashinsu.

    Har yanzu ana tafka ruwan sama a yankin kuma yanayi na da muhimmanci a lokacin yaƙi.

    Yunƙurin diflomasiyya, ciki har da zuwan Shugaban Amurka Joe Biden game da tsara yadda za a kai kayan agaji Gaza da kuma fitar da 'yan ƙasar waje daga zirin, ba mamaki na cikin dalilan. Akwai kuma maganar 'yan ƙasar wajen da Hamas ke riƙe da su.

    Idan har yaƙin nan ya ci gaba, ƙawayen Isra'ila za su so su tabbatar an kare fararen hula da kuma hana yaƙin zama babban rikici.

  3. Labarai da dumi-dumi, Hari kan asibiti: Ƙungiyar Islamic Jihad ta musanta iƙirarin Isra'ila

    Ƙungiyar 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa ta musanta ta Palestinian Islamic Jihad (PIJ) ta musanta iƙirarin da Isra'ila ta yi cewa ita ce ta kai hari kan Asibitin Al Ahli da ke Gaza.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya ambato ƙungiyar tana bayyana haka.

    Rahotanni na cewa mutanen da suka mutu sun zarta 500 kuma babu tabbas game da adadin waɗanda suka jikkata.

  4. Falasɗinawa na arangama da 'yan sanda a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Reuters

    A can birnin Ramallah da Isra'ila ta mamaye kuma yake ƙarƙashin kulawar jam'iyyar Fatah ta Mahmoud Abbas, masu zanga-zanga ne ke arangama da jami'an tsaro na Falasinu.

    Jami'an tsaron sun mayar da martani da harba hayaƙi mai sa hawaye.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce dandazon mutanen na kira ga Shugaba Abbas ya yi murabus saboda yadda yake mu'amalantar yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da abokiyar hamayyarsa ta Hamas.

    Shugaba Abbas ya soke ganawar da aka tsara zai yi da Shugaban Amurka Joe Biden a Amman babban birnin Jordan ranar Laraba, inda wani jami'i ya ce saboda ana shirin gudanar da taron shugabannin gwamnatin Falasinu ne na Palestinian Authority.

  5. Sojojin Isra'ila sun ce rokokin 'yan ta-da-kayar-baya ne suka tashi a asibiti

    Rundunar sojojin Isra'ila ta wallafa a shafin X wanda a baya ake kira da Tuwita, cewa sun yi imani hari a kan asibitin Al Ahli, ya faru ne daga luguden rokoki da Falasdinawa 'yan ta-da-kayar-baya suka harba.

    Ga cikakken sakon rundunar ta IDF:

    "Wani duban tsanaki kan harkokin rundunar sojoji ya nuna cewa luguden rokoki da 'yan ta'adda suka harba a Gaza, da ke wucewa ta kusa da asibitin Al Ahli a Gaza a lokacin da ya fada kan wurin. Bayanan sirri daga majiyoyi birjik da ke hannunmu sun nuna cewa kungiyar Islamic Jihad ce ke da alhakin kan wannan harin roka da ya kuskure kuma ya fada kan asibiti a Gaza."

  6. Mahmud Abbas ya soke ganawa da Biden, Daga Barbara Plett Usher

    Wannan wata annoba ce ta kowacce irin fuska, kuma tana iya zama hakan ga ziyarar da Shugaba Biden zai kai zuwa Isra'ila.

    Abu na farko, tashin abin fashewa a wani wuri na fararen hula karara kamar asibiti.

    Sannan kuma, wuri mai cike da marasa lafiya da mutanen da aka jikkata, da kuma mutanen da ke samun mafaka, a wani abu da suke jin cewa "wuri ne mai aminci".

    Falasdinawa na cewa harin Isra'ila ne ta sama. 'Yan Isra'ila na cewa suna gudanar da bincike kan inda abin da ya fashe ya fito.

    Mai yiwuwa ne Amurkawa za su yi hattara game da abin da za su ce, ko kuma akalla game da dora laifi, har sai an samu karin bayanai.

    Amma za ta karkatar da alkiblar ziyarar da Biden zai kai sosai zuwa kan hadurran da fararen hula Falasdinawa ke ciki a Gaza, da kuma kara tsanani kan tattaunawarsa da shugabannin Larabawa a Amman.

    Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soke ganawarsa da Biden, wadda aka tsara gudanarwa a Jordan.

  7. 'Halin da ake ciki a Gaza ya yi kama da fim ɗin shan jini'

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Jakadan Falasɗinu a Birtaniya, Husam Zomlot, ya ce halin da ake ciki a Zirin Gaza "kusan iri ɗaya ne da fina-finan shan jini".

    Zomlot ya ce mutane a Gaza na ɗaukar matakai masu tsauri na ko dai su bar gidajensu, da yadda suke karkasa ruwan sha da abinci a tsakaninsu, da kuma ko za su iya ci gaba da kula da marasa lafiya masu doguwar jinya.

    "Abu ne da yake faruwa a yanzu wanda ba za a iya kwatanta shi ba," kamar yadda ya faɗa wa tashar talabijin ta BBC News.

  8. Sojojin Isra'ila sun ce 'asibiti ba wurin da suke kai wa hari ba ne'

    Editan BBC kan al'amuran duniya, Jeremi Bowen ya ce ya karbi wata sanarwa ta kiran wayar tarho daga ofishin mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila da ke mayar da martani, kan abin da jami'an Falasdinawa suka ce harin da Isra'ila ta kai ne a kan asibitin Al-Ahli da ke Gaza.

    Sanarwar ta ce "asibiti, gini ne mai matukar muhimmanci kuma ba wuri ne da rundunar sojin Isra'ila ke kai wa hari ba."

    "Rundunar sojojin Isra'ila tana gudanar da bincike kan inda bam din da ya fashe ya fito sannan a ko da yaushe tana fifita sahihanci da tabbatar da bayanai abin dogaro."

    "Muna kira ga kowa da kowa ya bi a hankali da hattara, lokacin ba da rahotanni kan ikirarin da ba a tantance shi ba musamman idan ya fito daga wata kungiyar 'yan ta'adda."

  9. Shugaban WHO ya yi Allah-wadai da hari kan asibitin Gaza

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya yi tir "da kakkausar murya" harin da aka kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke birnin Gaza.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce rahtonnin farko-farko sun nuna cewa an kashe ɗaruruwa tare da jikkata wasu.

    "Muna ƙara kira da a kare fararen hula da lafiyarsu, kuma a janye umarnin fitar da mutane daga gidajensu," kamar yadda ya wallafa a dandalin X.

  10. Wani likita ya faɗa wa BBC yadda aka 'ɗaiɗaita asibiti' a Gaza

    BBC ta samu ta yi magana da wani likita da bai bayyana sunansa ba, wanda ke aiki a asibitin da aka kashe mutum 500 a Gaza.

    Ya faɗa wa BBC cewa an lalata komai a wurin sakamakon harin - a inda mutum kusan 4,000 ke samun mafaka bayan sun bar gidajensu.

    Ya ƙara da cewa kashi 80 cikin 100 na asibitin ba ya aiki, kuma an kashe ɗruruwan mutane tare da raunata wasu.

    Ya ce yanzu babu kowa a asibitin saboda mutane na ƙoƙarin ceto waɗanda suka tsira da ransu.

  11. Labarai da dumi-dumi, Shugaban Falasɗinawa ya ayyana makokin kwana uku bayan hari kan asibiti

    Shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas ya ayyana makokin kwana uku bayan harin da ya kashe ɗaruruwan mutane a kan Asibitin Al Ahli, a cewar kafar yaɗa labarai ta Falasɗinawa.

    Kamar yadda muka ba da rahoto a baya, Isra'ila ta ce babu tabbas game da dalilin da ya jawo tashin wutar, amma tana bincikawa.

  12. Labarai da dumi-dumi, An kashe kimanin mutum 500 a wani hari kan asibitin Gaza - Jami'an Falasdinawa

    Adadin mutanen da aka kashe ya kai 500 bayan wani hari ta sama da ake zargin an kai kan wani asibiti - a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Gaza.

    A lokaci guda kuma, wani mai magana da rundunar sojin Isra'ila ya ce ba su da masaniya kan sanadin faruwar lamarin, kuma sojoji suna bin diddigin bayanai a kan wannan batu.

    BBC tana aiki don tantance bayanai a kan wannan al'amari.

  13. Dangi na neman amsa bayan nuna bidiyon aika-aikar sace 'yan Isra'ila kai tsaye

    Hamas Attack

    Asalin hoton, FACEBOOK

    Bidiyo sun bayyana na hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai kan fararen hula a kudancin Isra'ila, da ke nuna wasu da aka sace a gidajensu kuma masu kai harin suka rika nuna bidiyo kai tsaye.

    Sama da mako daya kenan da kai hare-haren, dangin mutanen da lamarin ya ritsa da su, da ke neman bayani ido rufe suna amfani da irin wadannan bidiyo don tantance abin da ya faru da makusantansu.

    Wasu suna nuna takaici da hukumomin Isra'ila saboda rashin ci gaban da ake samu wajen nemo danginsu da ake garkuwa da su.

    Daya daga cikin wadannan mutane shi ne Nir Darwish, wani mazaunin Birtaniya kuma dan'uwa ga wasu mutane guda biyar da suka bace a Nahal Oz kibbutz.

    Dangin - Noam Elyakim, da abokiyar zamansa Dikla Arava, da danta Tomer mai shekara 17 da 'ya'yan Noam mata guda biyu Daphna, 'yar shekara 15, da Ella mai shekara 8 - an gan su kiri-kiri maharan na rike da su a gidansu.

    'Yan matan wadanda ke zaune tare da mahaifiyarsu, ana jin sun je ziyara ne wurin mahaifinsu don bikin cika shekara 70 da kafa kibbutz.

    Sai dai ranar Litinin a wannan mako, dangin sun samu labari daga hukumomi cewa an kashe Dikla da Tomer, har ma an ga gawawwakinsu a wajen garin kibbutz.

    Israeli victims of Hamas attack

    Asalin hoton, MAAYAN ZIN

  14. Labarai da dumi-dumi, Harin Isra'ila kan makaranta ya kashe mutum shida a Gaza - MDD

    Aƙalla mutum shida ne suka mut bayan harin da jirgin yaƙin Isra'ila ya kai kan wata makaranta a sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin al-Maghazi na Birnin Gaza.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an jikkata wasu da dama a harin kuma ana tunanin adadin zai ƙaru, a cewar wata sanarwa daga sashen kula da Falasɗinawa na MDD wato United Nations Relief and Works Agency for Palestine Refugees in the Near East (UNRWA).

    "Wannan abin ɓacin rai ne kuma hakan ya nuna ɗabi'ar rashin mutunta rayukan farar hula," a cewar sanarwar.

    "Babu wani sauran wuri da ya rage mai aminci a Gaza, hatta gine-ginen UNRWA."

    Ta ƙara da cewa aƙalla mutum 4,000 ne suka fake a ginin makarantar. "Har yanzu ba su da wani wurin da za su je."

  15. Labarai da dumi-dumi, Harin Isra'ila kan asibiti ya kashe ɗaruruwan mutane, in ji Hamas

    Mun samu rahotonnin da ba mu tabbatar ba, inda Hamas ta ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari kan asibitin Baptist Hospital da ke tsakiyar Gaza.

    An ambato wani mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Falasɗinu na cewa harin ya kashe ɗaruruwan mutane.

    Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.

  16. Rundunar 'yan sandan Kano ta ɗebi tubabbun 'yan daba aiki

    'Yan sanda a Kano
    Bayanan hoto, 'Yan daba 222 ne suka zubar da makamansu a Kano kuma suka rungumi zaman lafiya

    Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ƙaddamar da tubabbun 'yan daba 50 waɗanda ta ɗauka aikin ɗan sanda a jihar bayan kammala horo na wata biyu.

    Wata sanarwa daga kakakin rundunar, Abdullahi Kiyawa, ta ce an zaɓo mutanen ne daga ƙananan hukumomin Municipal, da Dala, da Ungoggo, da Gwale, da Fagge, inda aka ɗauki mutum 10 kowaccensu.

    Da yake jawabi ranar Litinin a birnin Kano, Kwamishinan 'Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ya ce 'yan daba 222 ne suka tuba tare da miƙa makamansu a birnin.

    Birnin Kano ya fuskanci hauhawar faɗan daba da kuma ƙwacen waya daga matasa masu ɗauke da makamai musamman a watannin tsakiyar 2023, a cewar 'yan sanda.

    "Wannan salo umarni ne na Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya IGP Kayode Adeolu da ya bai wa dukkan rundunonin 'yan sanda cewa su duƙufa wajen aiwatar da tsaro tare da al'umma," in ji kwamishinan.

    'Yan sanda a Kano
    Bayanan hoto, An yi faretin yaye tubabbun a rufaffen ɗakin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano a yau Talata
  17. Rashin jituwa a majalisar dattawan Najeriya bayan Ndume ya ƙalubalanci Akpabio

    Sanata Godswill Akpabio

    Asalin hoton, Facebook/Senator Akpabio

    An samu rashin jituwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya da Mai tsawatarwa na majalisar yayin wani zama a yau Talata, lamarin da ya kai ga ficewar Sanata Ali Ndume daga zauren.

    Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya bukaci majalisar ta shiga taron gaggawa na sirri bayan fitar mai tsawatarwa a kan wani hukunci da ya ce Ndume ya sauka daga kan ka'ida.

    Sanata Ndume ya bijiro da wani kuduri ne a kan zargin tafka kura-kurai, ba kuma tare da an yi gyara ba daga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.

    Kuskuren da Ndume ya yi jan hankali a kai na da alaka da wani kuduri da Sanata Kawu Sumaila ya gabatar don yin muhawara a kan bukatar a sake bude kan iyakar Najeriya da Nijar, ba tare da ya bayyana sunan kudurin nasa ba.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa mai tsawatarwa na majalisar dattijan wanda ya mike a zauren ya kafa hujja da oda ta 51 ta kundin dokokin gudanar da zaman majalisar dattijai, ya bukaci shugaban majalisar ya ba da dama a rika yin gyara kan duk wani kuskure da aka yi, ko kuma aka lura da shi a lokacin zaman majalisa.

    Ndume ya ce, ”Wannan Majalisar Dattijai ce ta Jamhuriyar Tarayyar Najeriya da ke aiki bisa dokoki da ka'idoji da tsare-tsare. Idan a lokacin zaman majalisa, aka lura da yin kura-kurai, wajibi ne a yi gyara a kansu kafin a ci gaba da gudanar da muhawara.”

    Sai dai cikin hanzari Sanata Akpabio ya katse shi, inda ya ce tun da an yanke hukunci a kan wadannan batutuwa da aka bijiro da su, ba za a iya sake waiwayarsu ba, don haka ya yanke hukuncin cewa Sanata Ndume ba ya kan ka'ida.

    Sanata Sunday Karimi daga nan ya mike a zauren majalisa, inda ya yi kokarin jaddada bayanin Sanata Ali Ndume ta hanyar wani kuduri, amma sai Shugaban Majalisar Dattijai cikin sauri ya yanke hukuncin cewa shi ma ya sauka daga kan ka'ida.

    Sai dai a wani yunkuri na kashe wutar dambarwa, Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin, cikin hanzari ya mike inda ya karanta oda ta 16, wadda ta bukaci gabatar da wani kwakkwaran kuduri daga duk wani sanata don yin gyara ko bita a kan matakin da aka dauka tun da farko.

    Cikin fushi, Sanata Ndume ya gabatar da wani kuduri da ke neman yin gyara a kan kuskuren da ake jin an aikata.

    Amma ba tare da ya kammala gabatar da bahasi ba, sai Sanata Godswill Akpabio ya sake yanke hukuncin cewa Ndume ya sauka daga kan ka'ida. Lamarin dai a cewar Punch ya harzuka Ali Ndume, wanda ya tattara takardunsa, ya fice daga cikin zauren.

    • Manyan ƙalubalen da Majalisa ta goma za ta fuskanta a Najeriya
  18. An kashe wani babban kwamandan Hamas a hari ta sama

    An kashe wani babban kwamandan Hamas a wani harin da Isra'ila ta kai Zirin Gaza ta sama, kamar yadda reshen kungiyar mai gwagwarmaya da makamai ya bayyana.

    Ayman Nofal, wakili a babbar majalisar harkokin aikin soji ta rundunar Izz el-Deen Al-Qassam, shi ne ke tafiyar da harkoki a yankin tsakiyar Zirin Gaza, Hamas ta rubuta a dandalin sada zumunta na Telegram.

  19. Mutum 344 ne har yanzu ke jinya a asibiti bayan hare-haren Hamas - Isra'ila

    Jimillar mutum 344 ne har yanzu ke kwance a asibiti cikin Isra'ila bayan hare-haren makon jiya, a cewar ma'aikatar lafiya ta Isra'ila.

    A cikin wasu sabbin bayanai da ta fitar a safiyar yau, ma'aikatar ta ce mutum 82 ne ke cikin yanayin rashin lafiya mai tsanani, sai kuma mutum 194 da ke cikin yanayin jinya tsaka-tsaki da kuma kananan raunuka 68.

    Ta ce duka-duka mutum 4,229 aka kwantar a asibitoci tun bayan aukuwar hare-haren.

  20. Labarai da dumi-dumi, Falasɗinawa 3,000 ne suka mutu a hare-haren Isra'ila kan Gaza

    Kusan mutum 3,000 ne suka rasa rayukansu a Zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba sakamakon hare-haren Isra'ila, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu.

    Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ƙara da cewa an jikkata wasu mutum 12,500.

    Kazalika, an kashe wasu Falasɗinawan 61 a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan (West Bank), wanda Isra'ila ta mamaye da kuma raunata 1,250.