Isra'ila na da 'yanci ta yi “maganin kungiyar Hamas” a cewar sakataren tsaron Birtaniya.
Da aka tambaye shi, ko gwamnatin Birtaniya tana goyon bayan gargadin Isra'ila na cewa mutum miliyan 1.1 su fice daga arewacin Gaza cikin sa'a 24, Grant Shapps ya fada wa shirin BBC's Today cewa, abu ne mai muhimmanci ga Isra'ila ta yi bayani kafin ta dauki mataki.
“Abu ne mai kyau ganin cewa sun samar da bayanai kafin (su fara kai hari), tabbas Hamas ba ta yi haka ba, kafin ta kutsa ta halaka mutane,” Shapps ya ce.
Ya kara da cewa babu cikakkun bayanai game da shirin Isra'ila, kuma Shugaba Biden ya bayyana karara cewa akwai bukatar Isra'ila ta tabbatar da yin aiki sau da kafa da dokokin kasashen duniya.
Ya kuma ce ya ba da umarnin tura jiragen ruwa da helikwaftoci da jiragen sama don samar da ayyukan bin diddigi da tattara bayanai kan shirin abokan gaba.
“Birtaniya na kokarin ba da gudunmawarta wajen tabbatar da ganin, abin bai kara bazuwa ba,” Shapps ya ce