Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar EFCC

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Sassan Zirin Gaza a safiyar yau

    Wakilin BBC Rushdi Abualouf, wanda ke zaune a Gaza, ya aiko mana da wannan bidiyo da ke nuna hare-haren jiragen yakin Isra'ila suka yi matukar rugurguza gine-gine a Zirin.

  2. BBC ta kare manufar ƙin kiran Hamas da ''yan ta'adda' duk da matsin lamba

    BBC ta kare shawarar da ta yanke cewa ba za ta kira 'yan ta-da-ƙayar-baya na Hamas da sunan ''yan ta'adda' ba, a cikin rahotannin da take yaɗawa game da hare-haren baya-bayan nan a Isra'ila.

    Wani mai magana da yawun BBC ya ankarar da cewa akwai daɗaɗɗen matsayi da tashar labaran ta duniya ta ɗauka cewa masu aika rahotanninta, ba za su yi amfani da sunan 'yan ta'adda ba, su a kan kansu, sai dai fa idan suna ruwaito zancen wani.

    Wani daɗaɗɗen wakilin BBC kan harkokin waje, John Simpson ya ce "kiran wani da sunan ɗan ta'adda, na nuna cewa, kana goyon bayan wani ɓangare ne a cikin lamari".

    Sakataren tsaron Birtaniya Grant Shapps ya ce wannan manufa na "daf da zubar da mutuncin", tashar kuma akwai buƙatar BBC ta gano inda ta ajiye "tunaninta na sanin ya kamata".

    Mai magana da yawun BBC na cewa: "BBC tashar labarai ce mai zaman kanta ta fuskar tsarin gabatar da aikin jarida, wadda aikinta shi ne ta bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa 'a ƙasa' ta yadda masu bibiyarmu za su iya yanke hukunci da kansu."

  3. Sabbin bayanai daga sojojin Isra'ila

    Ga sabbin bayanan da aka samu daga sojojin Isra'ila

    • Sama da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su 95 ne aka shaidawa cewa an kai ‘yan uwansu zuwa Gaza.
    • Sama da rokoki 5,000 ne aka harba zuwa Isra'ila daga Gaza tun ranar Asabar.
    • Isra'ila ta kai hari sama da 2,600 a Gaza.
    • Akalla ‘yan Isra’ila 1,200 ne suka mutu yayin da wasu sama da 3,000 suka jikkata sakamakon hare-haren da kungiyar Hamas ta kai a karshen mako.
  4. Sojojin Isra'ila sun ce an fille kawunan jarirai a harin Hamas na kibbutz

    Wani sabon labari daga rundunar sojojin Isra'ila - ta hannun mai magana da yawun rundunar Jonathan Conricus shi ne 'yan ta-da-kayar-baya na Hamas sun fille kawunan jarirai a lokacin da suka kai miyagun hare-hare a karshen mako.

    Conricus ya ce wani mai binciken sanadin mutuwa da ya kai ziyara bayan kisan kiyashin da aka yi a Kibbutz Be'eriya ga gawawwakin kananan yara kuma ya tabbatar da yadda suka mutu.

    "Na amsa cewa, abu ne da ya dauke mu tsawon lokaci kafin mu iya ainihin fahimta, kuma mu rarrabe wannan rahoto, amma dai yana da wuya a yarda cewa hatta Hamas tana iya aikata irin wannan aika-aika ta kidahumanci," ya ce.

    "Ina jin yanzu muna iya cewa, da kwarin gwiwa, wannan ne abin da Hamas ta aikata...akwai gawawwaki warwatse a ko'ina, an gididdiba su."

    • Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa
    • Me jarirai suka yi da Lucy ta kashe bakwai?
  5. An tsare matar hambararren shugaban kasar Gabon - rahoto

    An daure matar tsohon shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odimba a gidan yari, kamar yadda lauyanta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Ana zargin Sylvia Bongo ne da laifin wawure dukiyar jama'a.

    An hamɓarar da gwamnatin mijinta ranar 30 ga watan Agusta.

    Lauya Francois Zimeray ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa daurin da aka yi mata a ranar Laraba "ba bisa ka'ida ba ne."

    A watan jiya ne, aka tuhumi Sylvia Bongo da laifin halasta kuɗaɗen haram da kuma karbar kadarorin sata da kuma damfara.

    An kuma tuhumi danta Noureddin Bongo Valentin da laifin almundahana, sannan an tsare shi kafin a yi masa shari'a.

    Sojoji dai sun kwace mulkin kasar ne jim kadan bayan ayyana Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Gabon.

    • Ali Bongo da shugabannin Afirka da suka kafe a kan mulki
    • Bayani kan halin da Ali Bongo ke ciki da kuma makomar alaƙar Gabon da Faransa
  6. Asibitocin Gaza na neman zama ɗakunan ajiye gawawwaki - Red Cross

    Kungiyar ba da agaji a duniya ta Red Cross (ICRC) ta yi gargadin cewa asibitoci a Gaza na neman zama ɗakunan ajiye gawawwaki.

    Tashar wutar lantarki daya tilo a Zirin Gaza ta daina aiki a ranar Laraba saboda karancin man fetur. Hakan na nufin Gaza - ciki har da asibitoci - za su koma dogaro da janareta, wanda kuma ke buƙatar karin man fetur a kai a kai.

    Galibin wutar lantarkin da ake samu a Gaza, na fitowa ne daga Isra'ila, wadda ta katse wutar da yankin ke amfani da ita, bayan harin Hamas.

    Daraktan Gabas ta Tsakiya a kungiyar Red Kuros, Fabrizio Carboni ya ce "Bacin ran dan'adam da wannan tashin hankali ya haifar, abu ne mai ban tsoro, kuma ina rokon bangarorin biyu su rage radadin da fararen hula ke fuskanta."

    "Kamar yadda Gaza ta yi asarar wutar lantarki, ayyuka sun fi karfin asibitoci, suna sanya jarirai a cikin kwalaben ajiye bakwainin jarirai.yayin marasa lafiya tsofaffi ke bukatar na'urorin taimaka wa numfashi, haka ba sa iya daukar hotunan X-ray, "in ji shi.

    Carboni ya kuma bayyana fargaba a kan Isra'ilawan da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su - yana mai kira a gaggauta sakin su.

    • Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
    • Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
  7. UNICEF ya ce yara mata miliyan 7.6 ba sa samun damar karatu a Najeriya

    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa yara mata miliyan 7.6 a Najeriya, mafiya yawa daga yankunan arewacin kasar, ba sa samun damar karatu.

    Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Cristian Munduate ce ta bayyana hakan a gidan gwamnatin Kano yayin bikin tunawa da ranar yara mata ta duniya ta shekarar 2023 da aka yi wa taken: “Lokacinmu ne yanzu – hakkinmu, makomarmu.”

    Ta ce, “Yayin da nasarorin da ‘yan mata ke samu ke bayar da kwarin gwiwa ga sauran mata a wasu sassan duniya, yara mata miliyan 7.6 a Nijeriya, mafi yawa daga yankunan arewa ba sa samun wannan dama ta karatu."

    “Abin ban tsoro shi ne, Najeriya na da kashi 15 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a duk duniya. Amma duk da haka, kashi 9 cikin 100 na matalautan mata ne ke da damar zuwa makarantar sakandare. Wannan ba ƙididdiga ba ce kawai, kira ne na a tashi tsaye."

    "Amma ko yaya, a cikin waɗannan ƙalubalen, muna samun karin kwarin gwiwa a yau da gobe."

    Ta kara da cewa, a yayin da Kano ke matsayi na biyu a jerin ‘yan matan da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, lamarin da ya nuna akwai tsananin banbance-banbance wajen samun ilimi, akwai bukatar a kara jaddada canjin wajen samar da ilimi.

    • Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
    • Najeriya ce kasar da yara suka fi tsunburewa a Afirka — UNICEF
  8. Kungiyar Hamas ta ce ta sako wasu ƴan Isra'ila da take tsare da su

    Kungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ce ta sako wata ‘yar Isra’ila da ‘ya’yanta biyu da take tsare da su, tun bayan hare-haren da ta kai ranar Asabar a cikin Isra’ila.

    Har yanzu ba a tabbatar da sanarwar da dakarun na rundunar Qassam ta Hamas suka fitar ba, kuma wasu kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun yi watsi da sanarwar, suna cewa da ma can ba a yi garkuwa da matar ba.

    Tashar talbijin ta Aljazeera da ke Qatar ta yada wani bidiyo da ta ce yana nuna sakin matar da 'ya'yanta ne.

    A bidiyon, an ga wata mata tana tattara kayanta da na ƴaƴanta a filin Allah ta'ala, daidai kusa da wata katanga, ga kuma wasu mayaƙa biyu dauke da makamai suna mata rakiya.

    • Yadda mahaifi ke taraddadi kan rayuwar 'yarsa bayan harin Hamas
    • Kalli yadda mazauna Gaza ke rayuwa yayin da Isra'ila ke luguden wuta
  9. Blinken ya isa Isra'ila

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra'ila don nuna goyon bayan Amurka bayan harin Hamas

    A cikin gajeriyar ziyarar tasa Blinken zai gana da jami'an Isra'ila da kuma shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas.

    Ana sa ran Blinken zai nemi a sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, wadanda wasunsu Amurkawa ne.

    Zai kuma buƙaci a tsaigata wuta tare da neman hanyar tsira ga fararen hular Gaza gabanin yiwuwar kai hari daga Isra'ila.

    Shugaban Falasɗinawan dai yana zaune ne a Yammacin Kogin Jordan, kuma abokin hamayyar siyasa ne ga Hamas a zirin Gaza.

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Antony Blinken ya je China don kyautata alaƙa da Amurka
  10. Putin ya isa Kyrgyzstan domin ganawa da shugaban ƙasar

    Kafofin watsa labaran Rasha sun ce shugaba Putin ya isa Kyrgyzstan, a ziyararsa ta farko a zuwa wata kasa tun bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama shi.

    A watan Maris ne aka ba da umarnin, saboda zarginsa da kwashe yara daga Ukraine zuwa Moscow, bayan kaddamar da yaƙi.

    Putin zai gana da shugaban Kyrgyzstan, Sadyr Japarov, ya kuma halarci taron kasashen tsohor tarayyar Sobiyat.

    Kyrgyzstan babbar kawar Rasha ce, amma bata amince da kotun hukunta manyan lafukan ta duniya ba.

    • Putin da Kim: Abokai a lokacin neman makamai
    • Ukraine ba ta shirya wa zaman lafiya ba - Putin
  11. Sabbin bayanai kan abin da ya faru a rikicin Gaza

    Ga abubuwan da suka faru cikin sa'o'i kalilan da suka wuce a rikicin Isra'ila da Gaza:

    • Akalla mutum 51 ne aka kashe a Gaza bayan jerin luguden bama-bamai da jiragen yakin Isra'ila suka yi wa yankin, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Falatsinawa ta bayyana. Yawan mutanen da suka mutu sakamakon mummunan harin da Hamas ta kai tsallaken kan iyaka shi ne 1,200, yayin da a Gaza aka kashe akalla 1,000 a hare-haren ramuwar gayya ta sama.
    • Amurka tana tattaunawa da Isra'ila da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Masar kan yadda za a bari kayan agaji su shiga cikin Gaza, da samar da amintacciyar hanyar fita daga yankin ga fararen hula. Anthony Blinken, Sakataren harkokin wajen Amurka na kan hanyar sauka a Isra'ila cikin 'yan sa'o'i, inda ake sa ran zai nanata goyon bayan Amurka ga Isra'ila.
    • A lokaci guda kuma, fadar White House ta yi amai ta lashe game da wasu kalamai daga Shugaba Joe Biden wanda ya yi ikirarin cewa ya ga hotunan kananan yara da 'yan ta-da-kayar-bayan Hamas suka fille wa kawuna - White House ta ce Biden bai ga irin wadannan hotuna ba.
    • Isra'ila ta tattara dakaru a kusa da iyakar Zirin Gaza, wadanda suka hadar da sojojin wucin gadi 300,000. Babu bayanai karara idan da kuma ko tana shirin kaddamar da wani hari ta kasa ne a cikin Gaza
    • Dubun dubatar mazauna Zirin Gaza ne suka kwana babu hasken lantarki tun lokacin da tashar lantarkin Gaza kwaya daya tal ta dakatar da aiki saboda rashin man fetur a jiya. Mafi yawan lantarkin da Gaza take sha na zuwa ne daga Isra'ila, wadda ta dauke wuta ga yankin bayan harin kungiyar Hamas. Sai dai mun sha ji daga mazaunan Gaza suna fada wa BBC cewa dauke wutar lantarki ba sabon abu ne a wajensu ba. "Mun kasance cikin yanayin a kawo a dauke lantarki tsawon shekaru masu yawa a iyakar tunawata," in ji wata mace.
    • Baya ga lantarki, Isra'ila tana toshe damar kai muhimman kayan bukatun rayuwa ciki har da abinci da ruwan sha don mayar da martani ga harin Hamas a kan Isra'ila. Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ana bukatar hanyar kai kayan jin kai cikin sauri kuma maras shinge. Ana kara matsin lamba don a bude wata amintacciyar kafa ko kafofi da za su ba da damar kai kayan agaji da magunguna cikin Gaza, da kuma barin Falasdinawa su fice idan suna bukata
    • Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da 338,000 ne aka raba su da muhallansu a Gaza.
    • Fargaba na ƙaruwa yayin da Isra'ila ke jibge dakarunta a kan iyakar Gaza
    • Dalilai huɗu da suka sa Hamas ta kai wa Isra'ila hari
  12. Kenya ta ce za ta kawo karshen yarjejeniya da likitocin Cuba

    Kenya ta ce za ta kawo karshen yarjejeniyar shekaru shida da ta bai wa likitocin Cuba fiye da 100 damar yin aiki a asibitocin ƙasar.

    Ministar lafiya Susan Nakhumicha ta fada a ranar Laraba cewa matakin zai taimaka wajen magance ƙalubalen da ma’aikatan kiwon lafiyar Kenya ke fuskanta ciki har da rashin samun ayyukan yi.

    “Mun yanke shawarar ba za mu sabunta yarjejeniyarmu da likitocin Cuba ba. Su kansu kwararrun likitocin mu sun himmatu wajen tabbatar da hakan,” in ji ta.

    Yarjejeniyar shekarar 2017 ta kafa wani shiri na musanya wanda likitocin Cuba za su taimaka wajen cike giɓin da ake samu a asibitocin gundumomi yayin da 'yan Kenya kuma za su je Cuba don samun horar likitoci na musamman.

    Har ila yau, akwai fargabar cewa gwamnatin Kenya na biyan kwararrun likitocin Cuba fiye da likitocin ƙasar duk da cewa wasu likitocin da aka horar a cikin gida ba su da aikin yi.

    Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya dai a ƙasar Kenya sun sha yajin aiki domin neman ƙarin albashi, da kyautata yanayin aiki da kuma ƙarin likitoci.

    • Likitoci na yajin-aiki kan albashi a Kenya
    • Najeriya: Likitoci na tururuwar barin ƙasar ana tsaka da yajin aiki
  13. Duk wani mayakin Hamas sunansa 'matacce' - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani mayaƙi na Hamas sunansa "mataccen mutum," bayan taron farko na sabuwar gwamnatin gaggawa ta kasar.

    Netanyahu da ɗan adawa Benny Gantz - tsohon hafsan soji - sun haɗa gwamnatin haɗaka domin tunkarar yaƙi a ranar Laraba, inda suka ajiye adawarsu ta siyasa.

    Gantz ya ce lokaci ne na yaƙi kuma sabuwar gwamnatin da aka kafa a shirye take ta "shafe Hamas daga doron kasa".

    • Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa
    • Netanyahu ya kafa gwamnati mafi cike da masu ra'ayin riƙau a tarihin Isra'ila
  14. An tilastawa mutum 340,000 a Gaza barin gidajensu - Majalisar Dinkin Duniya

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce an tilastawa mutane dubu dari uku da arba'in a Gaza barin gidajensu yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a yankin a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai a ranar Asabar.

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa ta ce hare-haren bama-bamai a yanzu sun kashe sama da mutane dubu ɗaya da dari biyu, da raunata sama da dubu biyar.

    Da yake babu shiga ba fita, don haka babu damar kai kayan agaji.

    Falaɗinawa dai suna kira da a samar da wata mashiga don kai kayan agaji da suka haɗa da kayan abinci da magunguna da man fetur.

    Wani jami'in Masar ya ce kasar na kokarin tattaunawa da Isra'ila don ba da wannan dama.

    • Shugabannin Saudiyya da Iran karon farko sun tattauna a kan rikicin Gaza
    • Isra'ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne
  15. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkanmu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Aisha Babangida.

    Ku kasance da mu tsawon yinin yau, domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban har ma da Najeriya.