Shugabannin mulkin sojan Nijar sun ce dakarun sojin Faransa za su fara janyewa daga kasar a yau Talata.
Ana takun-saka tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin mulkin sojoji a watan Yuli da ya hambarar da zababben shugaban kasar kuma babban aminin kasar Faransa Mohamed Bazoum.
Rundunar sojin Nijar ta ce za ta yi wa kwambar motocin farko na sojojin Faransa rakiya zuwa wajen kasar. Ba a fayyace yadda tafiyar za ta kasance ba.
Har yanzu bakin iyakokin Nijar da makwabciyarta Benin da Najeriya a kudu na rufe.
Amma sauran iyakoki da kasashen Mali da Burkina Faso da Chadi waɗanda kuma ke karkashin mulkin soja, suna na nan a bude.
Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne ke taimakawa Nijar wajen yaƙar 'yan ta-da-kayar-baya masu alaka da al-Qaeda da kungiyar IS.
A watan Agusta ne, gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta buƙaci Faransa ta fice daga Nijar, inda ta zarge su da yunkurin mayar da Shugaba Bazoum kan mulki da karfi.
An shafe makonni ana zanga-zanga a wajen wani sansanin sojojin Faransa na Yamai babban birnin kasar.
Da farko dai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ƙi amincewa da janye sojojin, amma daga bisani ya amince da bukatar haka a watan jiya, yana mai cewa za su bar ƙasar a karshen shekara.
A baya dai, ana kallon Nijar a matsayin daya daga cikin manyan aminan Kasashen Yamma a yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci.
Tasirin Faransa yana raguwa a can bayan juyin mulkin da aka yi cikin wasu kasashe da ta yi wa mulkin mallaka.
-
Shin wane tasiri janyewar dakarun Faransa za ta yi ga Nijar?
-
Me ya sa har yanzu wasu ƙasashen Afirka ke maraba da sojojin Faransa?