Adadin mutanen da suka mutu sanadin zaftawar kasa ranar Lahadi a Yaounde babban birnin kasar Kamaru ya karu zuwa mutum 30, yayin da karin 17 suka ji raunuka.
Ministan cikin gidan Kamaru wanda ya je wurin da abin ya faru ne don ganin irin barnar da aka yi ya sanar da haka.
Gidaje da dama a Mbankolo, wata unguwar masu karamin karfi, sun ruguje sun zama baraguzai, bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Haka kuma akwai fargabar cewa karin mutane ne gine-gine suka rufta da su kuma har yanzu ba a kai ga gano su ba.
“Mun sanya ayarin jami'ai da zai ci gaba da aiki tsawon rana don gano mutane," kamar yadda ministar gidaje da raya birane, Celestine Ketcha Courtès ta fada wa BBC.
Daga cikin wadanda aka kubutar, har da jariri dan wata uku.
Hukumomi sun bukaci mazauna unguwar wadda ake dauka a matsayin yanki mai hatsari, su fice daga cikinta saboda fargabar sake aukuwar zaftarewar kasar.
Mazauna unguwar sun fada wa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da ruwan sama ya tumbatsa a wani kogin yanki.
Mutanen da suka yi asarar komai nasu, sun ce ba su da wani wuri da za su iya zuwa.
Wani gidan rediyon yankin ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 40. Ambaliyar ruwa na ci gaba da kawo cikas ga ayyukan ceto, abin da ya tilasta wa mutane yin amfani da hannuwansu wajen zakulo gawawwaki daga cikin laka.
Iftila'in ya zo ne kusan shekara daya bayan akalla mutum 14 sun mutu a wata zaftarewar lakar da ta faru a birnin.
Unguwar talakawa ta Mbankolo ce iftila'in ya fi muni a lamarin na baya-bayan nan, inda gidajen da aka gina a gangare, suka ruguje, ambaliya ta jijjige bishiyoyin ayaba.
An ga gawawwakin kananan yara "kwakkwance a kan tabo@, wani mazaunin unguwar ya shaida wa kafar yada labarai ta Cameroon Voice.
-
Zabtarewar kasa: Mutum 40 sun mutu ana neman 13 a Kamaru
-
Mutum 50 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Dimukradiyyar Kongo