Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Diezani Madueke ta gurfana a kotun Birtaniya kan tuhumar rashawa

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Haruna Kakangi

  1. Masu kare hakkin dan'adam sun koka a kan azabtar da mutane a kasar Masar

    Kungiyoyin kare hakkin dan'adam sun ce amfani da azabtarwa da mahukuntan Masar ke yi, ya zama ruwan dare.

    A cikin wani rahoto da aka mika wa kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan azabtarwa, bakin wasu kungiyoyin kare fararen hula shida ya zo daya, a kan cewa jami'an tsaron Masar na amfani da wasu hanyoyin azabtarwa da suka hada da duka da lalata da kuma amfani da lantarki don rufe bakin 'yan adawa.

    Sabon shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawan Amurka, Ben Cardin, ya yi barazanar dakatar da tallafin da Amurkar ke bai wa Masa, matukar gwamnatin birnin Alkahira ba ta canza hali ba.

    Ana zargin shugaba Abdel Fattah al-Sisi da murkushe 'yan adawa a tsawon shekara goman da ya kwashe yana mulki.

  2. Buɗewa

    Jama'a, masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da safiya.

    Ku kasance da mu a wannan shafi na kai-tsaye domin kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Mukhtari Bawa zai kasance da ku a wannan lokaci.