Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ganduje ya karbi 'ya'yan jam'iyyar NNPP ta Kwankwaso

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Ba ni na kashe Mohbad ba kuma ni ba ɗan ƙwaya ba ne - Naira Marley

    Mawaƙin Najeriya, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley ya sake jaddada iƙirarinsa na cewa ba shi da hannu a kisan tsohon abokin aikinsa, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da daddare, Naira Marley ya ce, kamar kowa, shi ma ya shiga cikin damuwa sosai sanadiyyar mutuwar tsohon yaron aikin nasa.

    Naira Marley ya ce Mohbad ya bar kamfanin 'Marlian Music' ne a watan Satumban 2022, sai dai ya ƙara da cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu ba ta kai yadda ɗaya daga cikin su zai riƙa yi wa ɗan'uwansa fatan mutuwa ba.

    "Gaskiya ne cewa mun samu saɓanin fahimta a lokacin da muke aiki tare, amma saɓanin bai kai yadda mutane ke zuzutawa ba. Bai kai yadda za mu yi wa juna fatan mutuwa ba." In ji Naira Marley.

    Ya kuma ce sun riƙa ƙoƙarin warware rashin jituwar ta hanyar shari'a gabanin mutuwar Mohbad.

    Marley ya ce dalilin da ya sa ya yi gum da bakinsa game da mutuwar ta Mohbad shi ne saboda kaɗuwar da ya yi, da kuma gudun kada ya kawo cikas ga binciken da jami'an tsaro ke yi kan mutuwar.

    Ya kuma ƙara da cewa ya bar Najeriya ne tun a ranar 31 ga watan Agusta, kuma bai dawo ba tun wancan lokacin, sai dai yanzu haka yana shirye-shiryen dawowa domin amsa gayyatar ƴan sanda.

    'Ni ba ɗan ƙwaya ko ƙungiyar asiri ba ne'

    Naira Marley ya kuma ce kamfaninsa ba cibiyar ta'ammuli da ƙwayoyi ko ƙungiyar asiri ba ne. Inda ya ce shi kansa ba mai safarar ƙwaya ko ɗan ƙungiyar asiri ba ne.

    Ya ce "Marlian Music kamfani ne na wasu aminan juna, waɗanda ke gudanar da ayyukansu ta halastacciyar hanya. Manufarmu ita ce yin jagora ga mutane masu basira da tallafa musu."

    A ranar 12 ga watan Satumba ne Mohbad, mai shekaru 27 a duniya ya rasu, inda yanzu haka jami'an hukumar tsaro ta DSS ke gudanar da bincike kan mutuwar tasa.

    Lamarin ya kai ga cewa an sake tono gawar mamacin bayan binne ta domin gudanar da bincike, inda yanzu haka ake jiran sakamako.

    Mutuwar Mohbad ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya da ƙasashe maƙwafta, musamman a shafukan sada zumunta.

    • ‘Yan sandan Najeriya sun kama ‘yar fim saboda ta tara jama’a
    • Shin Rahama Sadau ta sauya sana'a ne?
  2. Jakadan Faransa ya fice daga Jamhuriyar Nijar

    Jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya fice daga Yamai, babban birnin ƙasar ta Nijar da sanyin safiyar Laraba, kuma yanzu hakan ya tashi a jirgin sama daga birnin Ndjamena na ƙasar Chadi zuwa gida Faransa.

    A watan da ya gabata ne ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ta bai wa jakadan wa'adin kwana biyu ya fita daga ƙasar.

    Nijar ta ɗeba wa ambasadan wa'adin ne bayan ya ƙi yarda ya gana da jagororin mulkin soji na ƙasar waɗanda suka hamɓarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli.

    Har yanzu sojojin na ci gaba da tsare Bazoum da iyalansa a fadar shugaban ƙasa.

    Nijar dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, kuma har yanzu akwai sojojin Faransar 1,500 a ƙasar ta Nijar.

    Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa dakarun Faransa za su fice daga Nijar ɗin kafin ƙarshen wanan shekara.

  3. Kotu ta soke lasisin kasuwancin Donald Trump a New York

    Wata kotu a birnin New York ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban kasar Donald Trump ya zuzuta bayanan da ya bayar a kan dukiyarsa.

    Alkalin Arthur Engoron ya ce Mista Trump ya yi karin gishiri da kambama arzikinsa, inda ya rika kiran kansa a matsayin hamshaƙin biloniya domin samun rance mai sauki da kuma inshora.

    Don haka, alkalin ya soke lasisin kasuwancinsa a birnin na New York.

    Sai dai Trump ya fitar da wata sanarwa inda ya yi Allah-wadai da hukuncin alkalin, wanda ya kira maras kan gado.

    An daɗe ana tuhumar Mista Trump a kan harkokin kasuwancinsa, da na iyalansa

  4. Ku yi wa Najeriya addu'a a wannan lokaci na Maulidi - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al'umma da su yi wa kasar addu'o'i yayin da musulman duniya ke murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW).

    A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yada labaru, Ajuri Ngelale, Tinubu ya ce "Najeriya tana a wani lokaci mai muhimmanci na wanzuwarta, yayin da gwamnati ke daukan duk wasu matakai na ciyar da kasar gaba, ana bukatar tallafi daga al'umma ta hanyar nuna kishin kasa, da juriya da kuma addu'o'i."

    Haka nan shugaban ya kuma bukaci al'ummar musulmi da su yi koyi da halayen fiyayyen halittun ba a lokacin murnar maulidin ba kawai, har ma da sauran lokuta.

  5. Barkan mu da warhaka

    Da fatan za ku kasance tare da mu a wannan shafi tsawon wannan yini inda za mu kawo muku duk abubuwan da suka kamata ku sani kan abubuwan da ke faruwa a fadin duniya a wannan rana.

    Muna taya ku murnar zagayowar ranar maulidi.