Shugabar kotun ɗaukaka kara a Najeriya, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem, ta ce akwai kararraki guda 39,526 da ke gaban kotun ɗaukaka karar kasar.
Mai shari'a Dongben-Mensem ce ta sanar da haka yayin wani biki don shiga sabuwar shekara shari'a ta 2023/2024 ranar Litinin a Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito babbar mai shari'ar tana cewa kotun daukaka kara ta karbi jimillar kara 7,295 da aka daukaka da kuma kudurorin shari'a 3,665 a shekarar shari'ar da ta wuce.
”Kotun ta yanke hukunci a kan kara 3,765 sannan ta cimma matsaya a kan kudurorin shari'a 5,617; ta kori kara 1,030, sannan ta ba da umarnin a ci gaba da sauraron kara 10,381.
“Har yanzu kotun na da jimillar kara 39,526 da aka daukaka ya zuwa ranar 31 ga watan Agustan 2023.
Hakan ya nuna karuwar shari'o'in da aka daukaka daga 34,037 da ke gaban kotun tun daga shekarar shari'a ta 2021/2022,” in ji Mai shari'a Monica.
Ta ce jimillar rukunin alkalai guda 98 aka kafa don sauraron shari'o'in zabe a fadin kasar, wadanda za su saurari jimillar korafe-korafen zabe 1,209 da aka shigar.
A cikin korafe-korafen a cewar Mai shari'a Monica, an shigar da kara biyar a gaban kotun zaben shugaban kasa kuma tuni kuton ta kammala aiki, yayin da alkalai suka yi hukunci a kan kararrakin zaben 'yan majalisar dattijai guda 147 da kuma kararrakin da ake ci gaba da yankewa har 417 na zaben 'yan majalisar wakilai.
Haka zalika, akwai jimillar korafe-korafe 557 masu alaka da zabukan 'yan majalisun dokokin jihohi da kara 83 a kan zabukan gwamnoni su ma da ake yankewa, a cewarta jiha 28 ne aka gudanar da zaben gwamna, kuma an shigar da korafi kan zaben a jiha 24.