'Putin na son a warware matsalar Nijar'
Shugaban soji na kasar Mali Kanal Assimi Goïta ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin.
A yayin zantawarsu, shugabannin biyu sun jaddada buƙatar masalaha a siyasance game da rikicin siyasar Nijar, bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Mohammed Bazoum daga kan mulki a watan Yuli.
Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun yi gargaɗi kan tsoma bakin ƙasashen waje a ƙoƙarin mayar da shugaba Bazoum kan iko, kamar yadda Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) ta ba da shawarar ɗaukar matakin soja a matsayin zaɓin kawo ƙarshen juyin mulkin.
Sojojin Mali sun bayyana aniyarsu ta tallafa wa Nijar, matuƙar wasu ƙasashen waje suka kutsa kai cikin ƙasar, sannan za su ƙulla alaka mai ƙarfi da Rasha, ciki har da alaƙar ayyukan sojojin hayar Wagner da ke samun goyon bayan fadar Kremlin.
Shugaba Putin dai ya jajanta wa Kanal Goïta game da harin ta'addanci da aka kai arewa maso gabashin Mali wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100.
Fadar Kremlin ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa, shugabannin biyu sun tattauna a kan matakai masu amfani na inganta ayyukan hadin gwiwa tsakanin Rasha da Mali a fannoni daban-daban da suka hada da kasuwanci da tattalin arziki da jin ƙai da yaƙi da ta'addanci.
Bugu da ƙari, Kanal Goïta ya nuna godiya ga shugaba Putin a kan goyon bayan da Rasha ta bai wa ƙasarsa lokacin ƙuri'ar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa a kan janye takunkumin da ƙasashen duniya suka ƙaƙaba wa Mali.
Tun da farko a zaman Kwamitin Sulhun, Rasha ta ƙi amincewa da ƙudurin mayar da takunkumin da aka ƙaƙaba wa Mali tare da tsawaita wa'adin ƙwararrun masu sa-ido a kan cin zarafin da ƙungiyoyi masu dauke da makamai da jami'an tsaro ke yi a Mali.
- Shin Ecowas ta fara ba da kai ga sojojin Nijar ne?
- Masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar Nijar