Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Dubai ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Sallama!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi da muke kawo muku rahotanni kai-tsaye a nan zamu yi bankwana da ku sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu.

    Zubairu Ahmad Ƙasarawa da Haruna Ibrahim Kakangi ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Shugaban Brazil ya ce idan Putin ya halarci taron ƙoli na G-20 a baɗi matakin kama shi na hannun kotuna

    Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya ce a ranar Litinin kotun ƙasar za ta yanke hukuncin yuwar ko za a iya kama shugaban Rasha Vladimir Putin idan ya saka ƙafarsa Brazil domin halartar taron ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na G-20 da za a gudana baɗi.

    Lula ya sanar da manema labarai hakan a babban birnin Delhi na ƙasar Indiya, inda ya ke halartat taron ƙolin na G-20 da ake kan gudanarwa tsawon mako ɗaya yanzu haka. "Idan Putin ya yanke shaarar halarta, to hukuncin iya kama shi na hannun kotu ba gamnatina ba", in ji Lula.

    Kotun da ke Hukunta Manyan Laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kama shugaban na Rasha tun a watan Maris, inda ta ke tuhumar sa da laifukan yaƙi da suka haɗa tilastawa ɗaruruwan yara yin gudun hijira daga Ukraine.

    Rasha dai ta sha musanta cewa dakarun sojojinta na da hannu wajen aikata laifukan yaƙi ko kuma raba yara 'yan asallin ƙasar Ukrain da ƙasarsu.

  3. An fara cire tsammani kan samun masu rai a girgizar ƙasar Moroko

    Masu gudanar da ayyukan ceto a ƙasar Moroko na ci gaba da amfani da hannuwansu wajen gudanar da aikin ceto domin neman waɗanda sua tsira da rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da ta auku a ranar Jumu'a.

    Kimanin mutane 2,681 ne kawo yanzu suka mutu sakamakon girgizar ƙasar - wanda shi ne haɗari da ƙasar ta taɓa fusknatn cikin shekaru 60. Gwamnatin Moroko na shan matsi da ta karɓi agaji daga ƙasashen duniya sakamakon masu gudanar da ayyukan ceton ba su da inganatattun kayan da za su yi amfani da su.

    Tuni da aka soma samun kayan agajin daga ƙasashen Sapaniya da Birtaniya da Katar da kuama Hadaɗɗiyar Daular Laraba. Girgizar ƙarƙasar mai ƙarfin 6.8 da ta doki tsaunukan Atlas a yankin Marrakesh ta lalata garuruwa da ƙauyuka da dama.

    Ɗaya daga cikin su akwai - Tafeghaghte -mai yawan jama'a 200 da kusan rabinsu suka hallaka kana ba a san inda da dama daga cikinsu suke ba kawo wannan loakaci. Ana ci gaba da ƙokarin ganin an isa da manyan na'urorin daga abubuwa masu nauyi, amma tarin ɓuraguzai sun toshe hanyoyin da za a bi da su.

    Moulay Brahim, mai shekara 26 mazauni wani ƙauye ne, ya shaidawa BBC cewa a gabansa wani gidan maƙwabtansa ya rufta.

    "Mutum shida 'yan gida daya ne ke zaune a nan. Mahaifinsu na waje a lokaci wanda yanzu haka ya na da rai, amma matarsa da yaranta huɗu duk sun mutu", ya faɗa a cikin wani yanayin kaɗuwa.

    "Cikin yaran akwai mace mai shekara 15 da mai takwas da masu shekara biyar-biyar. Ƙaramin yaron ne da shekara uku" in ji shi.

    Ya ce tun a daren Jumu'a ya kasa bacci ko cin abinci.

    "Yanayin ya yi muni matuƙa. Ban san lokacin da zan iya dawowa hayyacina kan wannan damuwar ba", in ji shi.

    Ya shaidawa BBC lokacin da tawagar ke kan hanyar zuwa ƙauna Amizmiz ya ce yana sa ran tawagarsa za ta fara lura da waɗanda ke cikin mawuyacin hali, waɗanda ake fargabar lamarinsu na iya tsananta idan har kayan agajin ba su isa da wuri ba.

  4. Miyetti-Allah ta roƙi a saka makiyaya cikin shirin bayar da tallafi

    Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti-Allah reshen jihar Kwara, Bello Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa suna son ganin an sanya Fulani makiyaya cikin taimakon da ake bai wa al'umma na rage radadin cire tallafin man fetur.

    A lokacin da yake bayani ranar Lahadi, Abubakar ya ce an bar al'ummar Fulani a baya, wajen rabon kayan tallafi da aka soma bayarwa domin rage raɗaɗin talauci da 'yan ƙasa ke fuskanta sakamamkon cire tallafin mai.

    Shugaban ƙungiyar ta jihar ya koka a kan yadda kowane lokaci ba a bai wa Fulani cikakkiyar kulawa, inda ya ce galibinsu ma ba su da asusun ajiyar kuɗi a banki bale har su iya cirewa idan buƙatar hakan ta taso. Ya ce a duk lokacin da za su kai dabbobinsu a kasuwa sufuri kan kwashe kaso mai yawa na kuɗin dabbobin da aka sayar.

    Abubakar Bello ya kuma roƙi gwamnati ta taimaki makiyaya da alluran rigakafin baƙin cutukkan da kan kashe musu dabbobi.

    Ya gargaɗi ɓata gari a cikin Fulani da ke aikata munanan ayyuka da su yi watsi da ta'addanci tare da rungumar zaman lafiya.

    Kana ya shawaraci manoma da makiyaya da su nemi hanyoyin tattaunawa tsakaninsu domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a cikin al'ummunsu.

  5. Kotu ta bai wa Simon Lalong nasara a zaɓen sanata

    Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen 'yan majalisar dattawa ta Najeriya, mai mazauninta a Jos da ke jihar Filato, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Simon Lalong wanda ya tsaya takarar ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Filato ta kudu a ƙarkashin jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Alƙalin da ya jagoranci bayyana hukuncin, Mai shari'a Mahmoud Tukur, ya yanke hukunci cewa yawan ƙuri'un da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Napoleon Bali ya samu sun tafi a banza, saboda an zaɓe shi ba bisa ƙa'ida ba.

    Hukuncin wanda aka yanke a ranar Litinin da kuma ya samu goyon bayan dukkan alƙalan, ya bayyana cewa a lokacin da aka gudanar da zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 jam'iyyar PDP ba ta da cikakken shugabanci a jihar, kazalika sun yi watsi da batun da ya shafi zargin yin aringizon ƙuri'u inda suka ce babu gamsassun hujjoji da za su tabbatar da hakan.

    Haka ma jam'iyyar PDP ta rasa kujerar ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓun tarayya na Barikin Ladi da Riyom inda aka tabbatar da Dalyop Chollom na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Kotun ta yanke hukuncin cewa Peter Gyenden na jam'iyyar PDP ba shi ne zaɓaɓɓen Sanatan ba sakamakon jam'iyyarsa ba ta da cikakken shugabanci a jihar ta Filato a lokacin da aka gudanar da zaɓukan.

  6. Mutumin da ya faɗo daga wani dogon tsauni ya tsallake rijiya da baya

    Wani mai hawan tsaunuka a New Zealand ya tsallake rijiya da baya, bayan faɗowa daga wurin mai tsawon mita 600 (1,968ft), inda ya tsira da ƙananan raunuka.

    ‘Yan sanda sun ce mutumin ya faɗo ne daga dusten Taranaki da ke arewacin ƙasar kuma ya kuɓuta ne sakamakon yanayi na bazara wanda ya tausasa kankara wanda da ke nufin ya sauka cikin dusar kankarar.

    Ƴan sandan sun ce mahayin "ya ci sa'a ta musamman da ya rayu".

    Tazarar da ya fado ta yi daidai da Hasumiya ta agogon Makkah da ke kasar Saudiyya, ɗaya daga cikin gine-gine mafi tsayi a duniya kuma kusan nunki biyu na ginin Shard na Landan wanda ya kai mita 309.

    Mahayin na cikin tawagar da ke hawan dutsen Taranaki lokacin da hatsarin ya afku da tsakar rana a ranar 9 ga watan Satumba.

    Wani jami'in ceto na tawagar Taranaki Alpine Rescue, wanda shi ma yana cikin masu hawan dutsen a wannan ranar, ya taimaka wajen gano mahayin da ya fadi.

    Dutsen Taranaki na daya daga cikin tsaunuka mafi muni a New Zealand, a cewar Majalisar Tsaron Dutse ta kasar.

  7. An dakatar da Pogba kan zargin ta'ammali da ƙwaya

    An dakatar da ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Juventus, Paul Pogba daga wasa bisa zargin sa da aikata laifin da ya shafi ta'ammali da ƙwaya.

    Hukumar yaƙi da amfani da ƙwayoyi a lokacin wasannin motsa jiki ta Italiya ta ce gwajin da aka yi wa Pogba ya nuna cewa an samu sanadarin 'testosterone' mai yawa a jikinsa, bayan wasan da Juve ta doke Udinese da ƙwallo 3-0, a ranar 20 ga watan Agusta.

    Duk da cewa ba a yi amfani da Pogba a wasan ba, amma yana cikin ƴan wasan da aka zaɓa domin yi masu gwajin amfani da ƙwayoyi bayan kammala wasan.

    Ya zuwa yanzu Pogba ya yi wa Juve wasa na tsawon minti 51 a wannan kaka.

  8. Abin da ya sa ba mu taimaka wa Moroko ba - Faransa

    Ministar harkokin wajen Faransa ta nanata cewa ya rage ga Maroko ta nemi taimakon Faransa don taimaka mata wajen shawo kan mummunar girgizar kasar da ta faɗa mata.

    Catherine Colonna na amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa ba a saka Faransa cikin ƙasashen da ake kira da su taimaka ba.

    Zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 2,681 sakamakon girgizar ƙasar ta faru ranar Juma'a da dare.

    Duk da dai cewa jami'an Faransa sun sha musanta cewa akwai wata ɓaraka a alaƙrsu da Maroko, an kwashe watanni babu wanda ke riƙe da muƙamin jakadan Maroko a Faransa.

    Haka nan, an sha ɗage ziyarar da Shugaba Emmanuel Macron zai kai birnin Rabat.

  9. An saka dokar ta-ɓaci a Libya bayan ambaliya ta kashe mutum 150

    Aƙalla mutum 150 ne suka mutu bayan guguwa mai ƙarfin gaske ta haddasa ambaliyar ruwa a gabashin Libya, a cewar wani jami'i.

    Guguwar da aka yi wa laƙabi da Daniel ta faɗa wa ƙasar da ke arewacin Afirka ne a ranakun ƙarshen mako, abin da ya sa hukumomi suka ayyana dokar ta-ɓaci.

    A makon da ya gabata Guguwar Daniel ta kashe mutum kusan 15 a nahiyar Turai.

    Dakarun sojan Libya bakwai sun ɓace yayin aikin ceto.

    An umarci shaguna da makarantu su rufe a gabashin Libya, yayin da aka saka dokar hana fita.

    Garuruwan da guguwar ta fi shafa su ne Benghazi, da Sousse, da Derna, da kuma Al-Marj.

  10. An tabbatar da mutuwar mutum huɗu a fashewar Ghana

    An tabbatar da mutuwar mutum huɗu da kuma jikkatar wasu da dama bayan wata fashewa da afku a wani wajen haƙar ƙasa na China a Ghana.

    Kazalika, wasu gonaki da ke kusa sun lalace, kwanukan rufi sun ɗaiɗaice kuma wasu gidaje sun tsattsage.

    Fashewar ta faru ne a wani wurin haƙar ƙasa mallakar kamfanin China ranar Asabar da dare, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

    Har yanzu jami'an hukumar kashe gobara da sauran jami'an tsaro na wurin, inda suke ci gaba da aikin ceto.

    A gefe guda kuma, an samu ƙarin mutanen da ba a gani ba, yayin da wasu biyu suke cikin mummunan hali.

    Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta Ghana ba ta tabbatar da musabbabin afkuwar fashewar ba.

  11. Ana bincike kan 'likitan' da ake zargi da cire wa marasa lafiya ƙoda a Jos

  12. Labarai da dumi-dumi, Dubai ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta cire haramcin biza a kan 'yan Najeriya, kamar yadda fadar shugaban Najeriya ta bayyana.

    Wata sanarwa daga fadar shugaban ta ce United Arab Emirates (UAE) ta ɗauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a yau Litinin a birnin Abu Dhabi.

    "Kazalika, wannan yarjejeniyar na nufin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Etihad da Emirates za su ci gaba da shiga da fita a Najeriya nan take," in ji sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar.

    Ta ƙara da cewa yarjejeniyar ba ta ƙunshi biyan wani kuɗi ba a nan kusa tsakanin ƙasashen, yana mai nuni da miliyoyin dalolin da gwamnatin Najeriya ta riƙe wa kamfanonin jiragen na kuɗin tikiti.

    Kusan shekara ɗaya ke nan da UAE ta dakatar da bai wa matafiya daga Najeriya biza, a rikicin diflomasiyyar da ya samo asali tun daga lokacin annobar korona.

    • Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da ƴan Najeriya daga shiga ƙasarta
  13. Gwamnan Sokoto ya ƙaddamar da tasi ta alfarma ga mata zalla

  14. Adadin masu shan wiwi ya ninka cikin shekara biyar a Kenya - Rahoto

    Wani sabon bincike da hukumar da ke hana ta'amali da barasa da kwayoyi a Kenya ta Nacada ya nuna cewa adadin masu ta'ammali da wiwi a ƙasar ya ƙaru, wani abu da ake fargaba tsakanin matasa.

    Yawan mutanen da ke shan wiwi a Kenya ya ninka sau biyar kamar yadda rahoton Nacada ya bayyana.

    Sabbin alƙaluma sun nuna yadda ake samun ƙaruwar masu ta'ammali da kwayoyi a ƙasar.

    Sun nuna ƙarancin shekarun da mutane ke fara shan waɗan nan kwayoyi a matakai daban-dabn, kuma yanzu sun nuna yadda ƙananan yara ke fara shan wiwi a ƙananan shekaru.

    Alkaluman sun una yadda yara ke fara ta'ammali da kayan shaye-shaye irinsu hodar iblis suna da shekara takwas zuwa sha hudu, yayin da suke fara shan koken a shekara 20.

    Rahoton ya nuna aka ɗauki matsalar da muhimmanci tsakanin hukumomi.

  15. Jirgin ruwan yaƙin Birtaniya na ci gaba da taya sojojin Najeriya tabbatar da tsaron teku

    Wani jirgin ruwan yaƙin Birtaniya, HMS Trent, ya sauka a Lagos don taimakawa wajen yaƙi da haramtattun ayyuka ciki har da fashin teku da fasa-ƙwauri a tsakanin ƙasashen yankin.

    Wata sanarwa da ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya fitar, ta ce wannan karo na biyu da jirgin yaƙin Trent ke kawo ziyara Najeriya.

    “Ziyarar za ta taimaka wajen bunƙasa samar da horo da tallafa wa tsaron teku a yankin mashigin tekun Guinea,” kamar yadda sanarwar ta ce.

    Jirgin HMS Trent ya baro Gibraltar ɗauke da wani rukunin ƙwararrun sojojin ƙundumbalar Birtaniya da wani jirgi maras matuƙi da ke aikin tattara bayanai mai suna Puma. Aikin jirgin HMS Trent shi ne ya tallafa wa Ƙasashen Afirka ta Yamma abokan ƙawancen Birtaniya wajen inganta ƙwazo kan yaƙi da laifuka a teku da kuma tabbatar da kawo ƙarin kwanciyar hankali a faɗin yankin.

    Da harkokin kasuwancin fam biliyan shida na Birtaniya da ke wucewa ta yankin, wani ɓangare na aikin Trent shi ne tallafa wa ayyukan kwanciyar hankali a Mashigin Tekun Guinea ta hanyar ba da horo don taimaka wa rundunonin sojin ruwan ƙasashe abokan ƙawance, su kai yaƙi ga masu aikata laifi da kyautata ƙawance da musayar ilmi a lokacin da suke sintiri don ƙara tabbatar da tsaro.

    Babban kwamandan jirgin ruwan HMS Trent, Kwamanda Tim Langford, ya ce, “wata karramawa ce ga jirgin yaƙin HMS TRENT ya sake komo wa Najeriya, wannan wata muhimmiyar ziyara ce ga aikin da aka turo jirgin ruwan zuwa Afirka ta Yamma tsawon wata uku”.

    Mataimakin Babban Jakadan Birtaniya a Najeriya, Jonny Baxter ya ce, “Turo wannan jirgin ruwan yaƙi zuwa Afirka ta Yamma wata manuniya ce kan yadda Birtaniya ke daɗa bayar da himma a matakin harkokin duniya wajen shawo kan ƙalubalen tsaro.

  16. Yarima Mohammed bin Salman ya tattauna da Modi na India

    Yarima Mohammed bin Salman na Saudyya na wata ziyara ta musamman a India bayan kammala taron G20 a Delhi.

    A yayin ziyarar ya yi wata tattaunawa tsakaninsa da Firaiminista Nerandra Modi a gidan Hyderabad da ke Delhi.

    Bayan tattaunawar Yariman ya ce "Tun farkon alaƙar Saudiyya da India ba a taɓa samun rashin fuskantar juna ba, yau kuma muna duba yadda goben waɗannan alaƙoƙi za su koma...Ina so na yi wa India godiya kan yadda ta sauki baƙuncin taron G20, ina kuma taya ta murnan cimma wasu nasarori masu yawa, ciki har da alaƙar kasuwanci da Ƙasashen gabas Ta Tsakiya, Indiya da Turai da sauransu."

    Yarima Salman zai yi ziyarar kwana uku ne a ƙasar bayan kammala taron G20 da aka yi a ranar Lahadi.

    Wannan ne karo na biyu da Yariman ya ziyarci India bayan ziyarar da ya kai ƙasar a watan Janairun 2019.

    India ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar kasuwanci ta gida layin dogo daga ƙasar zuwa Gabas ta Tsakiya zuwa Gabashin Turai. Ana yi wa wannan yarjejeniya kallon kalubalantar China na gina hanyoyi da take yi da muka faɗaɗa ikon ta a ƙasashen duniya.

  17. 'Sudan na tsunduma cikin zaman kara-zube'

    Mutanen da rikici tsakanin ɓangarori masu gaba da juna ya ritsa da su a birnin Khartoum na Sudan, na bayyana ƙasar a matsayin wadda ta auka cikin yanayi irin na kara-zube da rashin tabbas.

    A wani lamari mafi muni da ya faru tun bayan fara rikici tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan RSF a watan Afrilu, kusan mutum hamsin ne aka kashe a ranar Lahadi, lokacin da jiragen saman soji suka auka wa wata kasuwa in ji shaidu.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan biyar ne aka tilasta wa barin gidajensu a fadin ƙasar, sakamakon rikicin da ake fama da shi.

    Wani mazaunin birnin mai fama da hare-haren manyan bindigogi a kusa da gidajensu, mutane kamar Ahmed dole ne su yanke shawara cikin gaggawa: su tsaya a inda suke, ko kuma su nemi mafaka a wani wuri.

    Ahmed ya shaida wa BBC cewa mutanen gidansa kamar mahaifiyarsa da matarsa da yaransa a halin yanzu suna zaune a wurare daban-daban.

    Ahmed ya bayyana yadda yaƙin ke jefa Sudan cikin duhu, ya kuma bayyana ɓarnar da aka yi a birnin Khartoum a matsayin wadda ba za ta iya misaltuwa ba.

    Wani likita daga ƙungiyar ba da agaji ta MSF (Médecins Sans Frontières) ya shaida wa BBC cewa hatta gogaggun likitoci da ma'aikatan jinya da ke kula da wadanda hare-haren ranar Lahadi ya ritsa da su, sun shiga ɗimauta.

  18. Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar Moroko ya kai 2500

    Ma'aikatar harkokin cikin gidan Moroko ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta faru ranar Juma'a ya ƙaru zuwa 2,497 daga adadin da aka samu a baya na 2,122.

    Bugu da kari, adadin wadanda suka jikkata kuma ya haura zuwa 2,476 daga 2,400.

  19. Bazoum ne kadai zai iya janye sojojinmu daga Nijar - Faransa

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya sake tabbatar da cewa gwamnatin mulkin sojan da ta tsige shugaban Nijar Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki ba ta da hurumin ba da umurnin janyewar sojojin Faransa daga yankin Sahel na Nijar.

    Macron na mayar da martani ne ga sanarwar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta yi a ranar 9 ga watan Satumba inda suka zargi Faransa da yin amfani da dabaru na yaudara tare da haddasa tsaiko wajen janye sojojinta 1,500 kamar yadda wani shafin yada labarai mai zaman kansa ActuNiger ya ruwaito.

    “Muna cikin Nijar ne domin yakar ta’addanci, bisa bukatar ƙasar da hukumominta da aka zaba, wadanda suka hada da shugaba Bazoum, da gwamnatinsa da majalisar dokokin kasar,” in ji Macron yayin taron G-20 a Indiya.

    Ya kuma jaddada cewa, matakin da Faransa ta dauka ya taka muhimmiyar rawa wajen rage hare-haren ta'addanci a Nijar, duk kuwa da hasarar rayukan sojojin Faransa.

    Macron ya kuma bayyana cewa, Faransa na haɗa kai da shugabannin kasashen yammacin Afirka domin ganin an sako Bazoum da kuma maido da tsarin mulkin Nijar.

    Sabanin haka, shugaban mulkin sojan kasar Birgediya Janar Abdourahmane Tchiane ya zargi Faransa da goyon bayan shirin kungiyar Ecowas na shiga tsakani a Nijar tare da mayar Bazoum kan muƙaminsa.

    Ban da haka kuma, wata kungiyar farar hula mai goyon bayan soji mai suna M62 ta shirya wani gagarumin raye-raye a Yamai domin nuna goyon bayansu ga shugabannin sojojin da kuma kiran janyewar sojojin Faransa.

    Bikin ya samu halartar jami’an soji da dama wadanda suka godewa magoya bayansu bisa gagarumin taron da suke yi na yakar Faransa.

    • Mece ce makomar tsaron Nijar idan dakarun Faransa suka fice?
    • Kullum sai na yi magana da Bazoum - Shugaban Faransa
  20. Labarai da dumi-dumi, Harin ƴan al-shabab ya kashe ƴan majalisa a Eelgaras

    Labaran da ke fitowa daga yankin Galgaduud na cewa wata nakiya da ta tashe a garin Eelgaras, ta kuma kashe 'yan majalisar dokokin Galmudug biyu da kuma na karamar hukumar Dhusamareb babban birnin kasar, kamar yadda majiyoyin a yankin suka tabbatar wa BBC.

    Fashewar ta faru ne jim kadan bayan da dakarun gwamnati suka yi nasarar karbe iko da birnin Eelgaras, daga hannun kungiyar Al-Shabaab.

    Fashewar ta janyo mutuwar wani mutum da ke tare da 'yan majalisar biyu.

    Idan dai ba a manta ba dakarun gwamnati da 'yan sa kai na ƙalibilu daban-daban sun yi nasarar shiga garin na Eelgaras ba tare da fuskantar wata turjiya ba.

    Eelgaras dai gari ne da ke kan hanyar a tsakanin Dhusamareb da Elbur, kuma ya kwafe shekaru da dama a karkashin ikon kungiyar Al-Shabaab.

    Kwace garin Eelgaras da dakarun gwamnati da na kananan hukumomi suka yi, ya zama wani gagarumin mataki na kwato ikon gundumar Elbur, wanda ke nuna yadda ake ci gaba da kokarin daidaita yankin da kuma yaki da masu tsatsauran ra'ayi.

    • Harin bam ya kashe mutum tara ƴan gida ɗaya
    • Gwagwarmayar da Somalia take don fatattakar mayakan al-Shabab