Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Aljeriya ta gabatar da tsarin sasanta rikicin siyasar Nijar

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Al-Shabab ta kwace yankuna daga hannun sojojin Somalia

    Mayakan kungiyar al-Shabab sun sake kwato akalla wurare biyu da sojojin Somaliya suka kwace a wani sabon farmaki da suka kai.

    Akwai rahotannin da ke cewa bangarorin biyu sun samu gagarumar asara a lokacin da ake gwabza kazamin fadan neman iko da Cowsweyne.

    Majiyoyi a wani asibitin sojoji sun ce an kai akalla sojoji 50 da suka jikkata domin samun kulawa.

    Shugaba Hassan Sheikh Mohamud dai ya yi alkawarin kawo ƙarshen al-Shabab cikin watanni.

    A ranar Juma'ar da ta gabata sojoji da mayakan sa-kai sun yi shagulgulan murnar karbe wani sansanin mayakan al-Shabab da ke El Bur.

    • Masu mayafi da ke yaƙar mayaƙan al-Qaeda da al-Shabab a Somaliya
    • Al-Shabab ta ce ta kame wani otal a Somalia
  2. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da warhaka.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya ta Talata domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da makwabtan kasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Mu je zuwa....