Babban hafsan rundunar sojojin Sudan kuma shugaban ƙasar ya mayar da martani ga wata sanarwa da abokin hamayyarsa a rikicin ƙasar ya fitar, da cewa a shirye yake su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokaci.
Sai dai Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce "ba mu, ba yarjejeniya da 'yan cin amanar ƙasa".
Tun da farko, shugaban dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya ce duk wata yarjejeniya da za a ƙulla, sai ta kasance wadda za ta mayar da Sudan kan cikakken tsarin mulkin farar hula.
Ya kuma yi kira a kawo ƙarshen hare-haren da dakarun ƙasar ke kai wa a kan fararen hula.
Sai dai babban hafsan sojojin Sudan Janar al-Burhan ya ce:
"Ba mu, muka fara wannan rikici ba, kuma ba mu neme shi ba. Su [RSF] ne suka fara yaƙi. Don haka, sai an ga bayansu kuma sai sun yi bayani kan laifukan da suka tafka..."
"Duk wanda ya ce an cimma wata yarjejeniya [da RSF] ko wani yana taimakawa, mafarki ne kawai. Ba mu, ba yarjejeniya da masu cin amanar ƙasa ko wasu mutane da suka ci amanar al'ummar Sudan kuma ba za mu yi aiki da duk wani ɓangare da ya ci amanar jama'ar Sudan ba."
Masu rajin kare 'yancin dimokraɗiyya a Sudan sun yi watsi da kalaman Hemedti, inda suka ce akwai tsagwaron munafunci a ciki, ganin ya ba da gagarumar gudunmawa wajen shirya hare-hare a kan fararen hula da kuma tabbatar da ganin sojoji sun ci gaba da mulki a Sudan.
A ranar 15 ga watan Afrilun bana ne faɗa ya ɓarke tsakanin dakarun RSF da rundunar sojin Sudan bayan shugabannin ƙasar biyu sun samu saɓani game da makomar ƙasar da kuma shirin miƙa mulki hannun farar hula.
Dubban mutane ne suka rasu kuma mutane fiye da miliyan huɗu sun tsere wa gidajensu.
-
'Yadda na haihu a hanya domin tsira da raina'