An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a jihar Adamawa

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan dake faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Litinin - idan Allah ya kai mu za mu dawo muku da sabbin labarai.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Atletico ta ci Man City a wasan karshe na sada zumunta a Asia

    Wasanni

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Atletico Madrid da ci 2-1 a wasan sada zumunta da ta buga na karshe a Asia, don tunkarar kakar bana.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Atletico ta fara cin kwallo ta hannun Memphis Depay da kuma Yannick Carrasco.

    Daga baya ne City ta zare ɗaya ta hannun Ruben Dias, saura minti huɗu a tashi daga karawar.

    Tun farko an yi lattin take leda, sakamakon zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya a karawar ta birnin Seoul.

    Kyle Walker, wanda ake alakanta shi da komawa Bayern Munich kafin fara kakar bana, ya buga tamaula ta bugi turke a wasan.

    Haka kuma ya rage kaɗan 'yan wasan City da suka haɗa da Erling Haaland da Phil Foden kaɗan su zura kwallo a raga tun kan hutu.

    City mai rike da Premier League da FA Cup da Champions League za ta fuskanci Arsenal a Wembley a Community Shield ranar 6 ga watan Agusta.

    Wasanni

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Fafaroma Francis ya yi kira ga Rasha da ta koma kan yarjejeniyar fiton hatsi

    Pope Francis

    Asalin hoton, Getty Images

    Fafaroma Francis ya yi kira ga Rasha da ta koma kan yarjejeniyar fiton hatsin ta bahar Aswad domin Ukraine ta samu damar fidda hatsi duk da yakin da ake gwabzawa.

    Shugaban na Katolika ya yi wannan roko ne yayin da yake jawabi a dandalin St Peters.

    Fafaroma Francis ya ce za su ci gaba da yi wa Ukraine addu'a saboda yaƙin da take da Rasha.

    Farashin Alkama dai ya yi tashin gwauron zabi bayan Rasha ta sanr da janyewa daga yarjejeniyar.

  4. Muna samun ƙarin nasarori a yaƙi da Rasha - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana ƙarin nasarori da Ukraine ke samu a yakinta da Rasha.

    Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan Rasha ta sanar da harɓo wasu jirage marasa matuka na Ukraine lokacin da suke shawagi a Moscow.

    Cikin jawabin da ya yi a bidiyo Mista Zelensky ya umarci sojin ƙasar su kasance cikin shiri domin Rasha za ta kai farmaki cibiyoyin makamashin Ukraine nan ba da jimawa ba.

  5. Shugaba Tinubu ya naɗa mai bincike na musamman kan Babban Bankin Najeriya

    CBN

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wani mai bincike na musamman mai suna Jim Osayande da zai yi bincike a babban bankin Najeriya.

    Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Tinubu ya aika wa Obazee, shugaban hukumar masu bayar da rahotannin harkar kuɗaɗe ta Najeriya.

    Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da alaƙa da bankin ta hanyar amfani da ƙwararru da hukumomin tsaro da masu yaƙi da rashawa da suka dace don aiwatar da aikin.

    Tinubu ya kuma aikewa Obazee kwafin umarninsa na dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Emefiele ke fuskantar shari'a kan zargin taimaka wa ta'addanci, sai dai ya musanta zargin.

  6. Hotunan yadda Ecowas ta gudanar da taro a Abuja

    Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS sun bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa'adin kwana bakwai su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki.

    Shugabannin da suka halarci taron sun haɗar da

    1. Shugaban mulkin sojin Chadi Gen Mahamat Idris Derby

    2.Umaro Mokhtar Sissoco na Guinea Bissau

    3. Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma na Togo

    4. Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire

    5. Macky Sall na Senegal

    6. Patrice Talon na Jamhuriyar Benin

    7. Nana Akofo-Ado na Ghana

    8. Adama Barrow na Gambia

    Sai ministocin harkokin wajen Cape Verde da na Liberiya da kuma wakilai daga kungiyar haɗin kan Afirka da AU da wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Tinubu

    Asalin hoton, Presidency

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar Bola Tinubu ne ya jagoranci gudanar da taron.
    Ecowas

    Asalin hoton, Presidency

    Ecowas

    Asalin hoton, Presidency

    Ecowas

    Asalin hoton, Presidency

  7. Jami'in kashe gobara ya mutu yayin kashe wuta a Canada

    Gobara

    Asalin hoton, Reuters

    Wani ma’aikacin kashe gobara ya mutu yayin da yake kashe gobara a lardin British Columbia da ke yammacin ƙasar Canada, a cewar hukumomin yanki.

    An tilastawa mazauna yankin kudancin jihar da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Amurka barin gidajensu sakamakon bazuwar gobara.

    A halin yanzu, kashi ɗaya bisa uku na gobarar ta Kanada na faruwa ne a lardin British Columbia.

    Zuwa yanzu gobarar ta yi ɓarna a yankuna da yawa a Kanada fiye da Koriya ta Kudu ko Cuba.

    A farkon watan nan ma, wasu ma’aikatan kashe gobara biyu suka rasa rayukansu a gobarar mafi girma a tarihin ƙasar.

  8. An sayi ɗan dambe naira 200,000

    Ɗan dambe

    Kungiyar damben Kudawa ta kasa ta sayi Bahagon mai Bulala naira 200,000 ranar Lahadi a gidan wasa da ke DeiDei a Abuja ranar Lahadi.

    Shi dai Bahagon Mai Bulala mutumin Hadejia ne a jihar Jigawa, Nageriya, amma yake wakiltar Guramada.

    Tun da sanyin safiyar Lahadi dan wasan ya je ya gaisa da Alhaji Aminu mai Unguwa, Garkuwan Kudawa ya ce masa zai koma Kudu da dambe.

    Kudawa sun tambaye shi koda wanda ya matsa masa sai ya bar Guramada zuwa Kudu, sai ya ce shi da kansa ya amince da wannan hukunci.

    Haka kuma dan damben ya fada cewar iyayensa da abokansa sun taka rawar gani, yadda suka ba shi shawara da ya ga ita ce mafita.

  9. Abin fashewa ya hallaka mutum 35 a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, نجات 1122

    Wani abin fashewa a lardin Khyber Pakhtunkhwa na Pakistan ya yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata wasu da dama.

    An kashe Maulana Ziaullah ɗaya daga cikin manyan jagororin wata kungiyar addinin Islama a lamari.

    Wani jami'in lardin ya sanar da cewa adadin waɗanda suka jikkata sun kai kusan mutane 200.

    Fashewar ta afku ne a wajen taron magoya bayan Jami'ar Ulema Islam, kuma a cewar hukumomin yankin, ana sa ran ƙaruwar waɗanda abin ya shafa.

    Wannan kungiya karkashin jagorancin Maulana Fazal Rahman, ta bukaci firaminista da ministan jihar da su binciki wannan fashewar.

    Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin wannan fashewar.

  10. An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a jihar Adamawa

    s

    Asalin hoton, AHMADU UMARU FINTIRI/TWITTER

    Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar takaita zirga-zirga ta tsawon sa'a 24 a faɗin jihar.

    Cikin wani saƙon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, ya ce an sanya dokar ne sakamakon ƙaruwar hare-haren da ɓata-gari ke kai wa mutane da kasuwanni a faɗin jihar.

    Rahotonni daga jihar sun ce wasu ɓata-gari ne suka riƙa far wa mutane da makamai a birnin Yola tare da sace musu dukiyoyi a shagunansu.

    Gwamna Fintiri ya ce an hana zirga-zirga a jihar, sai iya mutanen da ke ayyuka na musamman, waɗanda ke ɗauke da katin shaidar aiki.

    Gwamnan wanda ya yi kira ga al'ummar jihar da su yi biyayya ga dokar, ya ce tsaron lafiyar mutanen jihar shi ne babban abin da ya sanya a gaba.

    Wani mazaunin Yola mai suna Aminu Yakubu ya shaida wa BBC cewa wasu matasa maza da mata ne suka fito a garin Jimeta, tare da aɓkawa rumbunan ajiye abinci, inda suka yi ta ɗiban kayan abinci daban-daban irin shinkafa da taliya da sauransu.

    Ya ce jami'an tsaro sun yi amfani da karfi kan mutanen ne bayan da suka nuna turjiya.

    Ya kuma ce jami'an tsaro sun kama mutane da dama kan lamarin, tare da tafiya da su domin ci gaba da bincike.

    "Garin Jimeta ne kawai abin ya shafa, Yola da sauran wurare babu matsala," in ji Malam Aminu.

    Sai dai ya ce zuwa yanzu hankali ya kwanta kuma dokar takaita zirga-zirgar ta fara aiki, indaa aka rufe kasuwanni da sauran wurare.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. An fara taron ECOWAS kan juyin mulkin Nijar a Abuja

    b

    Shugabannin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS na gudanar da taro a Abuja babban birnin Najeriya domin tattauna batun juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.

    Shugabannin kasashe takwas da ministocin kasashen waje biyu ne suka hallara Abuja gabanin fara taron.

    Shugaban Najeriya kuma shugaban kungiyar Bola Tinubu ne ke ƙarbar baƙuncin taron.

    Shugabannin da suka halarci taron sun haɗar da

    1. Shugaban mulkin sojin Chadi Gen Mahamat Idris Derby

    2.Umaro Mokhtar Sissoco na Guinea Bissau

    3. Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma na Togo

    4. Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire

    5. Macky Sall na Senegal

    6. Patrice Talon na Jamhuriyar Benin

    7. Nana Akofo-Ado na Ghana

    8. Adama Barrow na Gambia

    Sai kuma ministocin harkokin wajen Cape Verde da na Liberiya

    Sai kuma wakilai daga kungiyar hadin kan Afirka da AU da wakilan Majalisar Dinkin Duniya

  12. Yajin aiki zai ci gaba har sai gwamnati ta biya mana buƙatu - Likitocin Najeriya

    gg

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A makon da ya gabata ne Kungiyar NARD ta sanar da shiga yajin aiki

    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta jaddada matsayinta na ci gaba da gudanar da yaji aiki har sai gwamnatin ƙasar ta biya mata buƙatunta.

    Hakan na zuwa ne a yayin da ƙungiyar ke shiga kana na huɗu tun bayan fara yajin aikin sai-baba-ta-gani a ƙasar.

    Shugaban kungiyar Dakta Emeka Oji ya bayyana hakan a lokacin ani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar a birnin Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da yajin aikin har sai an samu ani gagarumin ci gaba daga ɓangaren gamnatin tarayya, domin duba buƙatun ƙungiyar.

    Dakta Oji ya kuma ce kamtin gudanarar kungiyar tasu na yin kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su gaggauta biya wa kungiyar bukatunta domin kauce wa ci gaba da yajin aikin, lamarin da ya ce ka iya kawo cikas ga fannin lafiyar ƙasar.

    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) na da mambobi 15,000 daga cikin likitoci fiye da 40,000 da ake da su a ƙasar.

    To sai kungiyar ce ƙasai ke cikin yajin aikin, yayin da babbar kungiyar likitocin ƙasar ta (NMA) ba ta cikin yajin aikin.

    To sai Dakta Oji ya ce za su ci gaba da tuntuɓar ƙungiyar likitocin ƙasar ta NMA domin ganin ta bi sahunsu wajen shiga yajin aikin.

    • Abin da ya sa likitocin Najeriya suke neman aiki a kasashen waje
    • Yadda tsadar rayuwa ta tilastawa likitocin Najeriya ficewa zuwa ƙasashen waje
  13. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Umayma Sani Abdulmumin tare da Zulaihat Abubakar Kibiya ne suka gabatar da shirin na wannan makon

  14. Gwamnatin mulkin sojin Nijar na neman ɗauki daga Rasha

    s

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani

    Dakarun sojin Nijar da suka yi wa gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum juyin mulki na kira ga ƙasar Rasha da ta kawo musu dauki, tare da neman ƙasar Faransa da sauran ƙasashen yamma da ke ƙasar da su fice da Nijar ɗin.

    Cikin wata sanarwa ta kakakin majalisar ceto ƙasar ta sojoji Kanal Manjo Amadu Abdurahamane, ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya yi kira ga ƙasar Rasha da ta taimaka wa Nijar da sojoji da kayan aiki.

    A yau ne ƙungiyar Ecowas ke gudanar da taro don tattauna batun juyin mulkin da sojojin suka yi a Nijar.

    To sai dai cikin sanarwar da majalisar ceton ta Nijar ta fitar, ta yi zargin cewa taron na Ecowas yunƙuri ne far wa Nijar da yaƙi.

    A don haka ne ma Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya ce a shirye suke su kare ƙasarsu daga hare-haren da ya yi zargin Ecowas za ta ƙaddamar wa ƙasar.

    Sannan kuma ya yi kira ga 'yan ƙasar da su fito su gudanar da zanga-zanga domin mara musu baya.

    ss

    Asalin hoton, RNT

    Bayanan hoto, Kakakin majaliar ceton Nijar Kanal Manjo Amadu Abdurahamane

    Ƙasar Rasha dai na da dakaru a Mali mai makwabtaka ta Nijar, lamarin da ya sa Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka janye sojojinsu da ke aikin wanzar da zaman lafiya daga ƙasar.

    A ranar Laraba ne dai sojojin Nijar suka sanar da kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, lamarin da ya sa ƙasashen duniya da ƙungiyoyi ke ci gaba da yin Allah wadai da abin da sojojin suka yi, tare da kira da su maido da mulkin fara hula da kuma sakin shugaban ƙasar wanda suke tare da shi.

    Ko a ranar Asabar ma ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU ta bai wa sojojin ƙasar wa'adin kwanaki 15 da su koma barikokinsu tare da maido da mulkin fara hula a ƙasar.

  15. Amsoshin Takardunku

    Amsoshin Takardunku tare da Badariyya Tijjani Kalarawi

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  16. An yi garkuwa da wata Ba'amurkiya tare da ɗanta a Haiti

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Wata ƙungiyar agaji ta mabiya addinin Kirista ta ce an sace wata malamar jinya Ba'amurkiya da ɗanta a ƙasar Haiti.

    Kungiyar ta ce an sace su ne a ranar Alhamis bayan Amurka ta shawarci yan ƙasarta su gaggauta ficewa daga Haiti sakamakon taɓarɓarewar tsaro a ƙasar.

    Shugaban ƙungiyar El Roi Haiti, ya ce malamar jinyar matar daraktansu ne wanda ɗan asalin Haiti ne.

    Ma'aikatar cikin gida a Amurka ta ce ta san halin da ake ciki, za kuma ta yi aiki tare da hukumomin Haiti domin kuɓutar da matar.

    Kungiyoyin 'yan ta'adda ne dai ke riƙe da rabin babban birnin ƙasar Porto Prince, sannan sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare a ƙasar.

  17. ECOWAS na shirin gudanar da taro kan juyin mulkin Nijar

    STATE HOUSE

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, Bola Tinubu ya zama shugaban ECOWAS a taron da ƙungiyar ta gudanar a Guinea-Bissau cikin watan Yuli

    Nan gaba kaɗan ne a yau ƙungiyar Shugabannin ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS za su yi wani taro a Abuja babban birnin Najeriya, domin tattauna batun juyin mulkin soji a jamhuriyar Nijar.

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar ta Ecowas ne zai jagoranci taron, wanda ake sa ran shugabannin ƙasashen yankin za su halarta.

    Tuni dai shugaban na Ecowas cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya yi Allah wadai da juyin mulkin, tare da alƙawarta cewa ƙungiyar Ecowas tare da sauran ƙasashen duniya za su yi duk abin da ya dace wajen ganin sun kare dimokradiyya.

    Ya ƙara da cewa ƙungiyar za kuma ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin mulkin farar hula ya ci gaba da wanzuwa a yankin yammacin Afirka.

    Cikin sanarwar taron na Ecowas da ta fito daga fadar shugaban na Najeriya, ta ce mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da Babban Sakatare Janar na MAjalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres a tattaunawar da suka yi daban-daban da shugaba Tinubu, sun bayyana goyon bayan Amurka da kuma MDD kan matsayin ƙungiyar Ecowas da shugaban na Najeriya.

    Za dai ayi taron ne alhalin sojojin da sukai juyin mulkin na ci gaba da tsare shugaba Muhammad Bazoum da suka kifar da gwamnatinsa.

    Tuni dai ƙasar Faransa da ƙungiyar EU suka sanar da dakatar da ayyukan tallafi da suke bai wa Nijar sakamakon juyin mulkin da sojojin suka yi.

    Ita ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU a nata ɓangare, ta ce ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki 15 su koma barikokinsu, su kuma maido da mulkin farar hula a ƙasar da ke yankin yammacin Afirka.

    • Sojoji sun yi juyin mulki a Nijar
    • Lokuta biyar da aka yi juyin mulki a Nijar
  18. Rikici ya ɓarke a sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinu a Labanun

    p

    Asalin hoton, AP

    Rikici ya barke a sansanin 'yan gudun hijirar Falasdinu da ke kasar Labanoon inda mutum guda ya mutu da jikkatar wasu shida ciki har da yara ƙanana.

    Majiyar Falasdinu a sansanin Ain al-Helweh da ke kusa da Sidon, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa mamban wata kungiya jihadi ne ya rasu.

    Rikiçin ya ɓarke tsakanin mambobin ƙungiyar Fattah da mayaƙan jihadi na IS.

    Sama da 'yan gudun hijira dubu 54 ne ke fakewa a sansanin, su ma Falasdinawa da ke guje wa yaƙin Syria suna zama a wajen.

    Ƙarƙashin wata yarjejeniya, sojin Lebanon ba sa shiga sansanonin 'yan gudun hijira 12, waɗanda rashin bin doka da oda ya yi katutu a cikinsu.

    Fiye da 'yan gudun hijirar Falasdinu dubu 450 Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa rajista a Lebanun

  19. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.