Makamai masu linzami sun lalata gine-gine a Dnipro
Wasu makamai masu linzami da aka harba sun faɗa kan wasu gine-gine biyu da ke tsakiyar gabashin birnin Dnipro na Ukraine.
Wata tawagar BBC da ke birnin ta ce hare-haren sun lalata wani gini a birnin, sannan wani gini na jami'an tsaro wanda ba a amfani da shi ya rushe.
An ga yadda gilasai suka farfashe suka warwatsu kan titunan da ke kusa da gine-ginen da makaman suka faɗa.
mutane da dama ne suka samu raunuka, to amma babu rahoton rasa rai kawo yanzu.