Nan da shekara ɗaya, za a samu kyakkyawan sauyi a Najeriya - Shettima

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan dake faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Bankwana

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Lahadi - idan Allah ya kai mu za mu dawo da sabbin labarai.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Lokaci ya yi da za mu daina musayar ɗalibai da China - Jamus

    Ministar ilimi a Jamus ta ce lokaci ya yi da za a sake nazarin hanyoyin musayar ɗalibai da ƙasar China saboda karuwar ayyukan leken asirin kimiyya.

    Bettina Stark-Watzinger ta bayyana cewa China ta kasance abokiyar hamayyar tsarin mulki a fannin kimiyya da bincike.

    Don haka ta yi maraba da shawarar Jami'ar Friedrich-Alexander ta yi, na yanke shawarar daina karɓar ɗaliban ƙasar China waɗanda China ke ɗaukar nauyin karatunsu.

  3. Faransa ta dakatar da dukkan gudummawar da ta ke ba Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, Reuters

    Faransa ta dakatar da dukkan gudummawar da ta ke ba Jamhuriyar Nijar, a wani mataki na mayar da martani game da juyin mulkin da sojoji su ka yi a wannan makon.

    Ta kuma yanke agajin kasafin kuɗaɗe da ta ke ba Nijar ɗin a fannin tattalin arziki.

    Ma`aikatar Harkokin Wajen Faransa ta buƙaci a dawo da tsarin mulki karkashin zaɓaɓɓen shugaba Mohamed Bazoum.

    Tun da farko Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da janyewar haɗin kai a fannin tsaro da taimakon kuɗaɗe tsakaninta da Nijar.

    Wannan na zuwa ne bayan da Kungiyar Ƙasashen Afirka ta ba sojojin wa`adin kwana 15 su koma bariki.

    A gobe Lahadi Shugabannin Afirka ta Yamma za su gana don tattauna batun na Nijar.

  4. Ƴan sanda sun kama mutum huɗu da ake zargi da safarar yara a Benue

    Ƴan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a jihar Benue sun ce sun kama wasu mutum huɗu da ake zargi da safarar yara a Makurdi, babban birnin jihar.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce an samu nasarar kama mutanen ne bayan samun bayanai cewa suna safarar yara a wani sansanin ƴan gudun hijira a wasu sassa Makurdi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Anene na cewa sun kuma samu nasarar kama mutuanen huɗu bayan kai samame wuraren, sai dai jagoransu ya tsere.

    Ta ce waɗanda ake zargin sun bayyana cewa sun samar da wasu mata masu ciki, waɗanda idan suka haihu sai a karɓi jariran daga hannunsu, inda ake biyansu 150,000 kan kowane jariri.

    Ta kara da cewa sun samu nasarar gano wani yaro a gidan jagoran nasu wanda tun da farko iyayensa suka yi shigiyar cewa ya ɓata.

    Kakakin ƴan sandan ta shawarci iyaye cewa su sanya ido kan yaransu a kowane lokaci musamman ma yanzu da makarantu ke hutu.

  5. Chelsea ta kusa kammala sayen Ugochukwu daga Rennes

  6. Mayakan Wagner za su iya shigar burtu su shiga Tarayyar Turai, in ji Firaministan Poland

    Wagner

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Poland, Mateusz Morawiecki, ya yi gargaɗin cewa mayakan Wagner da ke Belarus na iya shigar kamar ƴan cirani su shiga Tarayyar Turau.

    Ya ce Wagner na iya neman shiiga ta ɓarauniyar hanya daga Belarus, wanda Poland ta bayyana a matsayin yaƙin gaɓar juna.

    Firaministan ya kara da cewa, dakarun Wagner kusan 100 ne suka koma kusa da birnin Grodno, da ke kusa da kan iyakokin Poland da Lithuania.

    A watan Yuni ne wasu sojojin Wagner suka koma Belarus.

    Warsaw ta ce tana kallon kasancewar Wagner a Belarus a matsayin wata barazana, wadda kuma ke neman haye yankin gabacinta.

  7. Ban so Henderson ya bar Liverpool ba in ji Kloop

  8. Nan da shekara ɗaya, za a samu kyakkyawan sauyi a Najeriya - Shettima

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Kashim Shettima/Twitter

    Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Najeriya za ta samu kyakkyawan sauyi nan da wata tara zuwa shekara ɗaya karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin ne a ranar Juma'a a birnin St Petersburg yayin wani zama da al'ummar ƴan Najeriya mazauna Rasha.

    Kashim ya tabbatarwa ƴan Najeriya musamman ma waɗanda ke zaune a ƙasar Rasha, cewa gwamnatin Tinubu za ta yi aiki tukuru don kawo ci gaba.

    A lokacin da yake tattaunawa da ƴan Najeriya a Rasha, Kashim ya ce "ina tabbatar muku cewa nan da wata tara zuwa shekara ɗaya, za a samu sauyi mai kyau a Najeriya, na faɗi haka ne saboda na yi imani da irin hazakar da Shugaba Bola Tinubu ke da shi."

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Kashim Shettima/Twitter

    Ya ce gwamnati mai ci na yin duk ƙoƙarinta wajen kyautata yanayin tattalin arzikin ƙasar da kuma farafad da kamfanoni da za su kawo mata ci gaba.

    Shettima ya kuma suna da burin horas da ƴan Najeriya miliyan ɗaya a ɓangaren ilimin zamani na intanet.

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Kashim Shettima/Twitter

  9. Abin fashewa ya hallaka mutum tara da jikkata 100 a Thailand

    Thailand

    Asalin hoton, THAI ARMED FORCES

    Akalla mutane tara ne suka mutu yayin da wasu fiye da 115 suka jikkata bayan fashewar wani abu a wani ɗakin ajiyar kayan wuta da ke wata kasuwa a kudancin ƙasar Thailand.

    Fashewar ta afku ne a ranar Asabar a garin Sungai Kolok da ke kan iyaka da Malaysia da misalin karfe 3 na rana.

    Ana kyautata zaton cewa aikin gini ne ya haddasa shi. Yanzu haka dai an shawo kan gobarar a kasuwar, kamar yadda gwamnan yankin ya shaida wa AFP.

    Sakamakon fashewar, tagar motoci da shaguna da gidaje duka sun kone.

  10. AU ta buƙaci sojojin Nijar su koma barikokinsu cikin kwana 15

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta AU ta buƙaci sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da su koma barikokinsu tare da maido da mulkin farar hula a ƙasar.

    Hakan na zuwa ne yayin da Kungiyar ECOWAS ke shirin gudanar da taro ranar Litinin kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, wanda kasashen duniya da dama suka yi Allah wadai da shi.

    Nijar dai ta shiga jerin ƙasashen yankin Sahel da sojoji suka ƙarbe ikon gudanar da mulki

    Wannan babban martani ne da wata ƙungiyar ƙasa-da-ƙasa ta yi. Cikin wata sanarwa da kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar haɗin kan ƙasashen Afirka ta AU ya fitar, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojjin Nijar sua gudanar.

    Kungiyar ta AU ta kuma ce ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki 15 da su koma barikokinsu.

    Sanarwar ta yi daidai da ta tarayyar turai wadda ta dakatar ta ce ta dakadar da tallafin kudi da na aikin soji da take bai wa ƙasar.

    Shi ma a nasa ɓangare sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurka za ta dakatar da tallafin miliyoyin daloli da take bai wa Nijar.

    Kasar Nijar wadda ke yankin Sahel ta kasance babbar ƙawa ga ƙasashen yamma a ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel da ke yammin Afirka.

    shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na shirin karɓar baƙuncin taron ƙungiyar shugabannin ƙasashen yammacin Afirka domin tattauna batun juyin mulkin na Nijar.

    A ranar Laraba da daddare ne sojojin Nijar suka ayyana kifar da gwamnatin farar hula da Mohammed Bazoum, bayan da suka wuni suna tsare da shi a gidansa.

    A ranar Juma'a ne kuma shugaban dakarun da ke taron fadar shugaban ƙasar Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban mulkin sojin ƙasar.

  11. Sadio Mane zai koma Saudi Arabia

  12. Najeriya za ta bai wa Google goyon baya don samar da ayyukan yi miliyan ɗaya

    TINUBU

    Asalin hoton, TINUBU/TWITTER

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa take wajen mara wa babban kamfanin fasaha na Google baya don samar da ayyukan yi miliyan guda a ƙasar.

    Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Mista Richard Gingras ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake ya fitar, Shugaban na Najeriya ya ce Najeriya na da matasa masu basira da fasaha, waɗanda koyaushe a shirye suke wajen koyon sabbin abubuwa musamman a wannan zamani na bunƙasar fasahar zamani.

    Yana mai cewa kamfanin google na da dukkan abubuwan da matasan Najeriya ke buƙata don bunƙasa fasaharsu.

    "Ina farin ciki cewa Google a shirye yake ya yi aiki da mu. kun amsa kiranmu wajen samar wa matasanmu sabbin ayyukan fasahar zamani. Kuna mara wa yunƙurinmu baya na bunƙasa sabbin hanyoyin tattalin arziki na zamani. A shiye muke mu yi aiki da ku kan yunkurinku na amar da ayyukan yi miliyan guda ga matasanmu'', in ji shugaban na Najeriya.

    Ya ƙara da cewa "Za mu ba ku duk goyon bayan da kuke buƙata domin cika wannan buri naku''.

    Najeriya na da miliyoyin matasa marasa aikin yi a ƙasar wadda ta fi kowacce yawan al'umma a nahiyar Afirka

  13. EU ta dakatar da taimakon soji da na agaji da take bai wa Nijar

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta dakatar da taimakon soji da take bai wa Nijar bayan kifar da gwamnatin ƙasar da sojoji suka yi.

    Matakin na zuwa jim-kaɗan bayan da Amurka ta sanar da matakin bai wa hamɓararren shugaban ƙasar goyon baya.

    Ana yi wa Mohamed Bazoum kallon babban abokin ƙasashen yamma, a ƙoƙarin da yake yi kakkaɓe ayyukan masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

    A ranar Juma'a ne shugaban dakarun da ke tsaron fadar shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasar.

    A yayin wani jawabi da ya gabatar Janar Tchiani ya ce taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa ne suka sanya shi ƙwace mulkin ƙasar.

    To sai dai ƙasashen yamman na nuna fargaba game da ƙasashen da sabon shugaban ƙasar zai ƙulla ƙawance da su.

    Duka makwabtan Nijar, Burkina Faso da Mali sun karkatar da ƙawancensu ga ƙasar Rasha tun bayan da aka yi juyin mulki a ƙasashen.

    Shugaban hukumar kula da al'amuran ƙasashen waje na ƙungiyar EU Josep Borrell ya bi sahun Amurka da Faransa wajen ƙin amincewa da sabbin juyin mulkin, yayin da ya ce taimakon soji da na agaji da ƙungiyar ke bai wa Nijar ya tsaya ba tare da ɓata lokaci ba.

    Haka kuma ita ma ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU ta yi kira ga sojojin Nijar da su koma sansanoninsu cikin kwanaki 15.

  14. Gwamnatin Jigawa ta ce ta ɗauki matakan kare ambaliya ruwa

    Umar Namadi

    Asalin hoton, NAMADI/FACEBOOK

    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta sayo mashina biyu waɗanda za ta yi amfani da su wajen yashe kogunan jihar domin kauce wa ambaliya ruwa a faɗin jihar.

    Gwaman jihar Mallam Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da BBC.

    Malam Namadi ya shaida wa BBC cewa ''Yawancin abin da ke janyo mana ambaliya shi ne kogunan da muke da su na Tiga da Chalawa sun cike, an daɗe ba a yashe su ba, saboda haka dole ta sa ake ambaliya''.

    Ya ƙara da cewa ''kogunan biyu an gina su ne bisa yaƙinin cewa za su ɗauki litar ruwa kimanin biliyan guda, to amma yanzu kusan lita miliyan 700 baya samun inda zai shiga a cikin kogunan dole sai ya fito ya samar wa kansa hanya, dalilin kenan da ya sa ke amun ambaliya a jihar Jigawa''

    Bayan mashina biyun da gwamnatin jihar ta saya, gwamnan ya ce hukumar kula da kogin Hadejia/Jama'are ta samar wa jihar wasu ƙarin injina biyu domin taimaka wa wajen yashe kogunan jihar don magance aukuwar ambaliyar.

    Haka kuma Mallam Umar Namadi ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gina jinga a wuraren da ake samun ambaliyar ta yadda za a rage wa ruwan gudu.

    ''A yanzu haka mun gina kusan kilomita 85 na jingar, kuma ana ci gaba da aikin'', in ji gwamnan.

    Jihar jigawa dai na daga cikin jihohin Najeriya da ambaliya ruwa ta yi wa ɓarna mai yawa a shekarar da ta gabata, lamarin ya haddasa karyewar gadoji da lalacewar tituna, tare da asarar amfanin gona na miliyoyin kuɗi.

  15. Abincin gargajiya da gasar tseren ninƙaya cikin hotunan Afirka

  16. Lafiya Zinariya: Matakan ajiye abinci don kauce wa gurɓacewa

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron shirin
  17. 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da cire wa wani mutum hannu

    s

    Asalin hoton, Police NG/Twitter

    Rundunar 'yansa jihar Bauchi ta ce ta kama wani mutum da take zargi da cire wa wani matashi hannu tare da sare masa kai.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ya ce mutumin mai suna Muhammad Abdullahi na daga cikin jerin mutanen da rundanar 'yan sandan jihar ke neman ruwa-a-jallo kimanin shekara biyu da suka gabata kan zargin aikata daba tare da munanan ayyuka.

    SP Wakili ya ce mutumin ya aikata laifin tare da wasu mutum biyu da rundunar ke ci gaba da nema.

    Sanarwar ta ce an kama Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Luwawu ne, a lokacin da tawagar 'yan sanda suka kai samame gidansa da ke birnin Bauchi.

    “Tun shekarar 2021 rundunar 'yan sandan Bauchi ke nemansa ruwa-a-jallo kan zargin haɗin baki wajen aikata miyagun laifuka da suka haɗar da daba, da ji wa mutanen raunuka da cutar da su, da sauran munanan laifuka'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa a shekarar 2021 ne Muhammad Abdullahi tare da haɗin bakin wasu mutum biyu ɗauke da adduna da sauran miyagun makamai suka sari wani mutum mai suna Mubarak Abdullahi da wuƙa a kansa tare da fille masa tafin hannunsa''.

    SP Wakili ya kuma ce mutumin da ake zargi ya amsa laifin a lokacin da aka tuhume shi da aikata lafin.

    Ya ƙara da cewa rundunar na ƙoƙari domin kamo sauran mutanen da ake zargi da aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kotu.

    • 'Yan sanda na neman mutanen da suka ƙwaƙule wa almajiri ido a Bauchi
    • Yadda wani mutum ya yi wa agolarsa mai shekara uku fyaɗe a Bauchi
  18. Abu biyar game da sabon shugaban mulkin sojin Nijar

    Janar Abdourahmane Tchiani ya shelanta kansa a matsayin sabon shugaban ƙasa a Nijar bayan wani juyin mulki bagatatan.

    Mutumin wanda kuma ake kira da Omar Tchiani, shi ne ya shirya ƙwace mulkin da aka fara ranar Laraba, lokacin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa da yake jagoranta suka kama shugaban Nijar.

    Hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na farko da ya gani wani zaɓaɓɓen shugaba tun bayan samun 'yancin kai a 1960.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  19. Abin da ya sa na sake naɗa kwamishinonin Badaru - Gwamnan Jigawa

    Umar Namadi
    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi

    Gwaman jihar jigawa Malam Umar Namadi ya ce ya sake naɗa wasu daga cikin kwamishinonin da suka yi aiki a lokacin tsohon gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar ne, saboda sun cancanta.

    Yayin wata tattaunawa da BBC, Umar Namadi ya ce kamar yadda tsohon gwamna ya yi aiki da su, shi ma ya yi aiki da su a a lokacin yana matsayin mataimakin gwamna kuma ya san irin rawar da suka taka a tsohuwar gwamnatin.

    ''Duka wadannan kwamishinoni da ake ganin na sake naɗawa da suka yi aiki ƙarƙashin tsohon gwamna, ni ma sun yi aiki ƙarƙashina a lokacin da nake riƙe da muƙamin mataimakin gwamna, saboda haka na san kowa, na san abin da zai yi, na kuma san abin da ba zai iya yi ba''.

    Tun bayan bayyana sunayen sabbin kwamishinonin jihar ne, wasu suka riƙa sukar gwamnatin da cewa tsoffin jami'an gwamnatin da ta gabata ne suka mamaye sunayen kwamishinonin, maimakon bayar da dama ga wasu sabbin fuskoki.

    To sai dai Gwamna Namadi ya ce yana ganin babu laifi kan wannan mataki, ''abin da kawai muke buƙata shi ne waye zai iya riƙe amana, waye zai iya yi wa mutanen jihar jigawa abin da ya dace'', in ji Gwamna Namadi

    • Zan bai wa fannin tattalin arziki muhimmanci - Gwamnan Jigawa
    • Umar Namadi ya lashe zaben gwamna a Jigawa
  20. INEC ta nuna damuwa kan rigingimu a jihohin da za a yi zaɓe a Nuwamba

    d

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta bayyana damuwarta kan rigingimun da ake samu a jihohin Bayelsa da Kogi da jihar Imo gabanin zaɓen gwamnonin jihohin da ke tafe cikin watan Nuwamba.

    Shugaban hukumar zaɓen farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin taron kwamitin tuntuɓa kan sha'anin tsaro na hukumar da aka gudanar a babban ɗakin taro na hukumar da ke Abuja.

    Farfesa Mahmood ya ce ''a yayin da muke nazari kan baban zaɓen ƙasar da ya gabata, yana da kyau mu mayar da hankali kan zaɓen gwamnoni da ke tafe a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi''.

    Tuni dai aka ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohin uku daga ranar 14 ga watan Yuli, za kuma a ci gaba har zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba mai zuwa.

    Hukumar zaɓen ta ce tuni aka fara samun alamomin tashe-tashen hankula tsakanin magoya bayan jam'iyyun adawa da 'yan takara daban-daban a waɗanann jihohi.

    INEC ɗin ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan masu rura utar rikice-rikicen, tare da ɗaura ɗamara domin kawar da abubuwan da suka saɓa wa Dimkoraɗiyya a lokacin zaɓen kamar batun sayen ƙuri'a da kai wa ma'aikatan zaɓen hari tare da kawo cikas ga harkokin zaɓen.

    A ranar 11 ga watan Nuwamba ne dai za a gudanar da zaɓukan gwamnoni a jihohin uku.

    • Jihohin Najeriya bakwai da ba a zaɓen gwamnansu tare da sauran
    • Mata 25 da suka yi takarar gwamna a Najeriya