Da alheri
Masu bibiyar mu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Laraba.
Ku tara gobe da safe domin samun sababbin rahotanni da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke fatan mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida and Rabiatu Kabir Runka
Masu bibiyar mu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Laraba.
Ku tara gobe da safe domin samun sababbin rahotanni da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke fatan mu kwana lafiya.

Asalin hoton, DUTCH COASTGUARD
Wuta ta tashi a cikin wani jirgin dakon kaya mai dauke da motoci akalla 3000 kusa da gaɓar tekun tsibirin Ameland, inda ɗaya daga cikin matuƙa jirgin da wasu abokan aikinsa 22 suka raunata.
Wasu daga cikin matuƙa jirgin sun faɗa cikin tekun don guduwa daga wutar.
Mai magana da yawun dakarun tsaron tekun Netherland ya ce wutar ta tashi ne a cikin motoci masu amfanin da lantarki guda 25 da jirgin ya ɗauko.
An ƙaddamar da aikin ceto a arewacin tekun kuma jami'an da ke aikin sun ce wutar tana iya shafe kwanaki tana ci.
Da farko dai matuƙa jirgin sun nemi kashe wutar da kansu, amma sai ta ci ƙarfin su, ta kuma tilasta masu ficewa daga jirgin.
Kaftin ɗin jirgin Willard Molenaar ya ce bakwai daga cikin jami'ansa sun fada cikin tekun.
Jirgin ruwan ya taso ne daga gaɓar tekun Bremerhaven dake arewacin Jamus a ranar Talata, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa gaɓar Port Said ta ƙasar Masar

Asalin hoton, Salihu Moh Lukman/Facebook
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa mai wakiltar shiyyar arewa maso yamma, Malam Salihu Lukman ya ajiye muƘaminsa.
A yau Laraba ne ya miƙa takardar ajiye aikinsa ga muƙaddashin shugaban jam'iyyar na Ƙasa, Sanata Abubakar Kyari.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan tsohon shugaban jam'iyyar, Sanata Abdullahi Adamu da kuma sakatarenta na Ƙasa Sanata Iyiola Omisore suka yi murabus.
A cikin sanarwar, Malam Salihu Lukman ya ce ya ajiye muƙamin nasa ne saboda zargin shisshigi wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar, wanda ya saɓa turbar da aka kafa jam'iyyar a kai.
Ya ce ya zaɓi yin murabus ne saboda baya son ci gaba da zama a wajen da ake yi wa fafutukar neman kawo gyaran da yake yi a matsayin yunkurin turjiya.

Asalin hoton, Getty Images
An samu koma-baya a yunƙurin cimma yarjejeniyar yin hukunci mai rangwame a shari'ar ɗan Shugaba Joe Biden, kan zargin da ake yi masa na rashin biyan haraji da kuma mallakar bindiga babu izini.
Yarjejeniyar da aka ɗauki makonni ana tattaunawa a kan ta, ta so bai wa ɗan shugaba Biden damar tsallake yiwuwar aika shi gidan yari.
Sai dai, a yau Laraba alƙaliyar kotun da ake sauraron ƙarar ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar, ba tare da ta yi nazari ba.
Karon farko kenan da ma'aikatar shari'ar Amurka ta gurfanar da ɗan shugaban ƙasa mai ci.
Wannan dai na zuwa ne bayan shafe tsawon shekara biyar ana bincike kan dukiyar Hunter Biden, wanda ya halarci zaman kotun a Wilmington.
Bisa tanadin yarjejeniyar da aka ƙulla a watan jiya, an shirya tuhumar ɗan shugaban Amurkan da laifin ƙin biyan haraji a 2017 da kuma a 2018.
Ya kuma amsa cewa ya taɓa mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba lokacin yana ta'ammali da ƙwaya.

Magoya bayan jagoran adawar Kenya, Raila Odinga sun yi taron addu'o'i ga mutane fiye da 30 da aka kashe lokacin da fada ya kaure tsakanin ƴan sanda da masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
Mista Odinga ya ziyarci mutanen da ke jinya a asibiti a cikinsu har da waɗanda ƴan sanda suka lakaɗa wa duka. Ya kuma ajiye furanni a wurin da aka yi makokin.
An zargi ƴan sanda da yin amfani da ƙarfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsadar rayuwa a Kenya.
Sai dai, masu sukar Mista Odinga sun ce yana amfani da batun ne don cimma burinsa na siyasa, bayan ya sha kaye a hannun Shugaba William Ruto a zaɓen ƙasar na bara.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bai wa gwamnatin Bola Tinubu wa'adin kwana bakwai ta janye duk tsare-tsaren da ta kira ''masu jefa jama'a cikin wahala'' ciki har da ƙarin farashin man fetur.
A cikin wata sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar, NLC ta yi barazanar fara yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023, idan gwamnatin tarayya ta gaza ɗaukar matakin da ya kamata.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero da sakatarenta Emmanuel Ugboaja ta ambato NLC na cewa gwamnatin tarayyar ta nuna halin ko-in-kula kan halin da 'yan ƙasar ke ciki, kuma ta ce gwamnatin ta kaddamar da yaƙi ne a kan ma'aikata da talakawa.
Ƙungiyar ƙwadagon ta ce tun daga lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, ''hankalin 'yan Najeriya bai kwanta ba''.
Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce cire tallafin man fetur ɗin ya zama wajibi a halin da ƙasar take ciki, matuƙar tana son samun kuɗaɗen gudanar da muhimman ayyuka.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar shugaban Najeriya ta ce babu batun biyan kudin karatu (tution fee) a ckin kuɗaɗen da jami’o’in gwamnatin tarayya a kasar suka ƙara.
Dele Alake, mai bai wa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
A baya-bayan nan ne mahukuntan Jami’ar Legas suka ƙara kuɗin makaranta inda dalibai za su biya N190,250 daga N19,000 ga masu karanta fannin likitanci, sai kuma ɗaliban da ke nazarin kwasa-kwasan da ke buƙatar shiga ɗakunan gwaje-gwaje za su biya N140,250.
Wannan ya haifar da martani yayin da mutane da dama suka soki matakin, wanda ya zo a lokacin da ake fama da raɗaɗin cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.
Sanarwar ta ce "A farkon makon nan ne wasu kafafen yada labarai suka bayyana cewa gwamnati ta ƙara kudin karatu a jami’o’in tarayya a ƙasar nan."
"Waɗannan rahotannin ba daidai ba ne. Muna sane da cewa wasu jami’o’i a ‘yan makonnin da suka gabata sun sanar da karin kudin da dalibai ke biya na makaranta."
"Sai dai kuma mun tabbatar da cewa wadannan kudade da jami’o'i suka ƙara wa dalibai na wurin kwana ne da rijistar da ake yi duk bayan zangon karatu da kuɗin rijistar ɗakin gwaje-gwaje da sauran kuɗaɗe amma ban da kudin karatu (tution fee) a ciki."
"Mahukuntan wadannan jami'o'in sun fayyace hakan wajen bayyana dalilan da suka sa aka yi ƙarin kuɗaɗen don gujewa shakku."
Sanarwar ta ƙara da cewa shugaba Tinubu ya ci gaba da jajircewa kan alkawarin da ya dauka na ganin kowane dan Najeriya ya samu damar samun ingantaccen ilimi mai zurfi, ba tare da la’akari da halin iyayensa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Firayim Ministan Indiya Narendra Modi za ta fuskanci kada kuri'a rashi ƙwarin gwiwa a majalisar dokokin kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin gwamnati da ƴan adawa dangane da tashe-tashen hankula a jihar Manipur.
Wani dan majalisa daga jam'iyyar adawa ta Congress ya gabatar da kudurin kaɗa kuri'ar a ranar Laraba.
Gwamnatin Modi ba za ta yi rashin nasara a ƙuri'ar ba saboda jam'iyyarsa da kawayenta ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar.
Sai dai shugabannin 'yan adawa sun ce matakin zai tilasta wa Mista Modi yin magana kan Manipur.
Suna neman ya yi jawabi ga majalisar dokokin ƙasar kan rikicin kabilanci a jihar wanda ya barke a cikin watan Mayu tsakanin kungiyar Meitei da ke da rinjaye da kuma tsirarun kabilar Kuki.
Akalla mutane 130 ne aka kashe tare da raba wasu dubbai da muhallansu.

Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK
Shugaba Bola Tinubu ya ce ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ba za ta amince da abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar ba.
Da safiyar yau Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa dakarun tsaro sun toshe fadar shugaban ƙasa da ofisoshin jami'an gwamnati a kasar.
A martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa, Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS ya ce ba za a lamunci yunƙurin juyin mulkin sojoji ba.
Sanarwar ta ce "Bayanan da aka samu daga jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa dadi da ke faruwa a ɓangaren shugabannin siyasar ƙasar."

Asalin hoton, JOHN MACDOUGALL
Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya nada Freda Prempeh a matsayin ministar tsaftar muhalli da albarkatun ruwa.
Ta karbi mukamin ne daga hannun Cecilia Abena Dapaah, wadda ta yi murabus daga aiki a karshen mako sakamakon badakalar kuɗaɗen da aka sace.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaru na ofishin Shugaban ƙasa, Eugene Arhin ya sanya wa hannu a ranar Talata.

Asalin hoton, GETTY IMAGES/PRESIDENCY
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce zai kawar da tsofaffin takardun kuɗin naira “a hankali” tare da maye gurbinsu da sababbin.
Mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin (MPC) a Abuja.
"Idan aka buga kudi kuma aka fitar da su ana sa ran za a yi amfani da su har zuwa lokacin da za su tsufa kuma har lokacin da babban banki zai janye su ya meye gurbinsu da sababbi, abin da muke yi ke nan", a cewarsa lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.
“Dole ne mu fitar da tsofaffin takardun kuɗi. Kuma yayin da suke shigowa, ana sarrafa su kuma ana dawo mana da su sannan mu kuma mu sake fitar da su domin maye gurbin tsofaffin da sababbi."
A watan Oktoban da ya gabata, Gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda aka dakatar, ya ɓullo da shirin sake fasalin manyan takardun kudi uku na N200 da N500 da N1000.

Asalin hoton, AFP
Firaminstan Mali Choguel Kokalla Maiga ya yi watsi da takunkumin da Amurka ta kakaba wa ministan tsaro, da babban hafsan sojin sama da mataimakinsa na ƙasar a matsayin "kawar da hankali" tare da yin alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga jami'an gwamnatin mulkin soja.
“Takunkumin da aka sanya wa jiga-jigan jami’anmu ba shi da wata manufa face karkatar da hankalin al’ummar Mali. Babu wani abu da zai dauke hankalinmu daga aikin sake gina kasar Mali." Mista Maiga ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ƙasar Amurka ta kakaba takunkumi kan mutanen uku saboda "tallafa" wa faɗaɗa ayyukan Wagner na Rasha a Mali.
Ana zargin dakarun Wagner da aikata manyan laifuka tare da sojojin Mali a yaƙin da suke yi da 'yan jihadi, inda Amurka ta ce yawan fararen hular da suka rasa rayukansu ya ninka fiye da sau uku tun bayan da aka tura su a karshen shekarar 2021.
Firaministan ne kadai babban jami'i a gwamnatin mulkin soja da ya yi tsokaci kan takunkumin.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dokokin Ghana ta soke hukuncin kisa, bayan da amince da yin gyara ga dokar hukumar manyan laifuka ta 2022. Ya biyo bayan tsawon lokaci na hanƙoro daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na ganin an yi watsi da dokar.
Lauya mai hanƙoron kare hakkin dan'adam kuma dan majalisa Francis-Xavier Kojo Sosu ne ya miƙa wa majalisar kudirin dokar domin sauya ta tare da goyon bayan wata kungiya da ke Birtaniya mai rajin ganin an yi watsi da hukuncin kisa (Death Penalty Project).
Ya ce “A kan hukuncin kisa, fursunoni suna farkawa da tunanin cewa wannan ita ce ranarsu ta ƙarshe a duniya. Sun kasance kamar matattu masu rai, sun daina yi kamar mutane saboda haka soke hukuncin kisa zai nuna cewa a matsayinmu na al’umma mun kuɗuri aniyar cewa ba za mu kasance masu cin mutunci ko haifar da rashin zaman lafiya ba."
A halin yanzu akwai maza 170 da mata 6 da aka yanke wa hukuncin kisa, waɗanda a yanzu za a maye gurbin hukuncin da daurin rai da rai.
Ko da yake kotuna a Ghana sun zartar da hukuncin kisan ne kan waɗanda aka samu da laifin kisan kai da yunkurin aikata kisa da kisan kare dangi da kuma fasa-ƙwaurin zinare; ba a cika aiwatar da hukuncin ba. Ghana ta zartar da hukuncin kisa na ƙarshe ne a shekarar 1993.
Kungiyoyin kare hakki sun yi ta fafutukar ganin an soke dokar. Ɓangarori da dama na yaba wa ƙasar kan matakin soke hukuncin na kisa.
Babbar jami'ar diflomasiyyar Birtaniya a Ghana Harriet Thompson, ta ce "Ghana ta shiga cikin dangin ƙasashen Commonwealth da suka dauki wannan mataki mai cike da tarihi."
Birtaniya na adawa da hukuncin kisa a kowane hali kuma ta ce suna tare da Ghana a wannan batu."

Asalin hoton, Getty Images
Masu bincike a Birtaniya sun ce motsa jiki ciki har da kwanciya a kan hannu da kafa kuma a ɗan daga kaɗan wato planking da kuma zama a jikin bango wato squatting na daga cikin hanyoyi mafi kyau da ke saukar da hawan jini nan da nan.
Masu binciken sun ce yawanci a yanzu mutane sun fi mayar da hankali wajen yin tafiya da tuka keke da kuma gudu a matsayin motsa jiki, a don haka suka ce akwai bukatar mutane su rinka irin wannan motsa jikin.
An yi gwajin irin wannan motsa jikin a kan mutane dubu 16, kuma anan ne aka gano cewa irin wannan motsa jikin na saukar da hawan jini sosai.
Cutar hawan jini dai mummunar cuta ce da ke janyo bugawar zuciya ko kuma shanyewar barin jiki.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Kenya William Ruto ya ce a shirye yake ya gana da ɗan jagoran 'yan adawa Raila Odinga a cikin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a baya-bayan nan.
Mutane da dama sun mutu a zanga-zangar.
Mista Odinga shine ke jagorantar zanga-zangar domin ingiza wa gwamnati wajen rage haraji da kuma sassauta wasu ƙarin farashin kayayyaki.
“Abokina Raila Odinga, na tafi Tanzaniya don tattaunawa da daidaita faɗaɗa ayyukan yi a nahiyarmu. Zan dawo ranar Laraba da yamma, kuma kamar yadda kuka sani, a shirye nake don ganawa da ku a kowane lokaci da kuka so," in ji William Ruto a shafinsa na Twitter.
Hakan ya biyo bayan wani taron manema labarai da Mr Odinga ya yi da cewa Mista Ruto ya yi watsi da tayin da shugaban ƙasar Tanzaniya ya yi masa na yin sulhu tsakanin gwamnati da 'yan adawa.
Mista Odinga ya yi Allah-wadai da yadda 'yan sanda suka yi wa masu zanga-zangar maras imani, ya kuma yi kira da a fito a ranar Laraba don girmama mutanen da aka kashe a zanga-zangar.

Asalin hoton, Getty Images
Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin sai baba ta gani a kan abin da suka kira gazawar gwamnatin na magance matsalolinsu.
Yajin aikin likitoci a Najeriya na shafar ayyukan da ake yi a asibitoci musamman na gwamnati.
Daga cikin bukatun likitocin akwai biyansu dukkan albashinsu da kuma alawus alawus din da ya kamata a basu.
Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akalla likitoci 50 na barin ƙasar a kowanne mako inda suke fita kasashen waje don su yi aiki a can.
Rashin biyan likitoci albashi mai kyau da rashin cikakkun kayan aiki a asibitoci da ma tsadar rayuwa na daga cikin abubuwan da ke sa likitoci fita daga kasar don neman aiki a waje.
Masu bibiyar shafin BBC hausa na kai tsaye barkan mu da safiyar Laraba.
Aisha Babangida da Rabiatu Kabir Runka ke fatan kasancewa da ku a yau domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Ku biyo mu.