DSS ta gurfanar da Emefile a kotu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Sanatoci sun hana gamayyar masu neman kawo canji kafa gwamnati a Thailand

    g

    Asalin hoton, AFP

    Sanatoci masu ra’ayin mazan jiya sun hana gamayyar masu neman kawo canji kafa gwamnati a Thailand.

    Gamayyar masu neman canjin ta samu rinjaye a majalisar wakilan ƙasar, amma mutumin da ta nemi ya zamo firaminista, ya gaza samun goyon bayan majalisar dattawan da gwamnatin ƙasar ta kafa.

    Masu adawa da yunkurin sun yi alkawarin gyara dokar ƙasar

    A karshe sanatocin da gwamnatin ƙasaar ta naɗa sun yi abinda ake zaton za su yi.

    13 ne kacal daga cikin sanatoci 249 suka goyi bayan Mr Pita na jam’iyyar Move Forward.

  2. MDD za ta cimma kudurinta na daƙile yaɗuwar cutar HIV a 2030

    Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa za ta cimma kudirinta na kawo ƙarshen yaɗuwar cutar HIV zuwa shekarar 2030.

    Sai dai ta yi gargaɗin cewa rashin kuɗin aiki da kuma nuna tsangwama ga masu cutar yana kawo cikas ga aikin.

    Kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta nuna cewa mutum miliyan 39 ne ke ɗauke da cutar HIV a duniya.

    Kuma akalla mutum miliyan 30 daga cikinsu ne ke karɓar maganin da ke rage kaifin cutar.

    Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce akwai buƙatar samun ƙarin kuɗin yaƙi da cutar, da kuma mayar da hankali daga bangaren gwamnatoci, idan har ana son kawar da ita.

  3. DSS ta gurfanar da Emefile a gaban kotu

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele a gaban kotun.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Peter Afunaya ya fitar, ya ce hukumar ta gurfanar da Mista Emefiele a gaban kotun ne domin bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta bayar da ta umarci hukumar ta DDS da kai shi kotu domin tuhumarsa ko kuma ta sake shi.

    Sanarwar ta ambato Mista Afunaya na cewa tun shekarar 2022 ne, hukumar DSS ta nemi umarnin kotu domin tsare Emefiele don gudanar da bincike kan wasu manyan laifuka da ka zarge shi da aikatawa.

    Ranar Laraba ne dai wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sake shi.

    Mista Emefiele ne dai ya shigar da ƙarar don tabbatar da 'yancinsa na ɗan'adam, inda yake ƙalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS take yi.

    A ranar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele, kwana guda bayan shugaban ƙasar ya dakatar da shi.

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya naɗa Emefiele a matsayin shugaban CBN a shekarar 2014.

    Ya ci gaba da zama shugaban babban bankin na Najeriya har ƙarshen wa’adin mulki na biyu na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

    Sai dai wasu matakai da ya ɗauka gabanin babban zaɓen Najeriya na 2023 ya janyo ce-ce ku-ce mai yawa a ƙasar.

    Batun sauya fasalin kuɗi da bankin ya ƙaddamar ya haifar da ƙarancin kuɗi a hannun al’umma, wani abu da ya janyo wahalhalu da dama.

    Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yaƙi da rashawa da matsalar tsaro da kuma ɗabbaƙa tsarin rage amfani da tsabar kuɗi tsakanin al’umma.

    Amma wasu daga cikin makusantan Tinubu sun yi zargin cewa sauya fasalin kuɗin wani yunƙuri ne na yin zagon-ƙasa ga nasararsa a zaɓen.

  4. Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci kan samar da abinci

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan batun samar da abinci a ƙasar.

    Mai magana da yawun shugaban ƙasar Dele Alake, ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

    Shugaban ƙasar ya bayar da umarnin mayar da duka al'amuran da suka shafi samar da abinci da ruwan sha, a matsayin manyan abubuwan dogaron rayuwa zuwa ƙarƙashin kulawar majalisar tsaro ta ƙasa.

    Alake ya ce umarnin na cikin tsare-tsaren gwamnatin Tinubu na tabbatar da tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar.

    Ya ce Shugaban ya damu kan yadda farashin kayan abinci ke ƙaruwa da yadda hakan ke shafar talakawan ƙasar.

    Shugaban ya kuma bayar da umarnin gaggauta bai wa manoman ƙasar taki da irin shuka domin rage musu raɗadin cire tallafin man fetur.

    Ya ƙara da cewa “Dole hukumomin ayyukan gona da ta ruwan sha su yi aiki tare domin tabbatar da ingantuwar noman rani a ƙasar don tabbatar da samar wadataccen abinci a ƙasar a kowanne yanayin shekara''.

  5. An haramta wa maza yin kitso a Zanzibar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a tsibirin Zanzibar mai ƙwarya-ƙwaryar yanci kai da ke ƙasar Tanzaniya sun aiwatar da wata doka da ta hana maza yin kitso.

    Sun ce yin kitso ga maza daɓi'a ce da ta saɓa wa doka da al'adun gargajiya kuma barazana ce ga tarbiyyar mutane.

    Sakataren raya al'adun yankin na Zanzibar Omar Adam ya ce kitson da wasu maza suke yi , wata al'ada ce da aka ɗauko daga wajen yankin.

    Omar Adam ya yi watsi da damuwar da wasu suka nuna a kan cewa matakin zai shafi yan luwadi da maɗigo da ke zaune a tsibirin inda aka haramta auren jinsi ɗaya..

    Sai dai duk da cewa dokar da ta hana maza yin kitso ba sabon abu ba ne, saboda tun shekarar 2015 ne aka zartar da ita amma a yanzu ne mahukuntan Zanzibar suka aiwatar da ita.

    Dokar dai ta yi tanadin cewa duk wani namiji da ya shiga yankin da kitso ko yana zaune a cikin yankin, za a ci tarar fiye da dala 400, ko kuma ɗaurin wata shida a gidan yari ko hukuncin duka biyun.

    Sai dai duk da cewa Zanzabir na cikin wuraren da masu yawon buɗe ido suke son zuwa amma mahukunta yanki sun ce dokar za ta yi aiki kan baki.

    A cikin watanni biyu da suka gabata ne gwamnatin Zanzibar ta haramta wasu sunayen littattafai 16 da kuma amfani da launukan bakan gizo a makarantu saboda a cewarsu suna goyon bayan masu kare hakkin 'yan luwadi da maɗigo

  6. Dakatar da Max Air a Najeriya ba zai shafi jigilar mahajjata ba - NAHCON

    Mahajjata

    Asalin hoton, DN

    Hukumar Alhazan Najeriya ta ce dakatarwar da Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA ta yi wa jirgin Max Air ba zai shafi jigilar mahajjata da ake yi daga Saudiyya ba.

    Cikin wata sanawar da hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta fitar, ta ce tana so ta kwantar wa Alhazan da iyalansu hankali.

    Domin kuwa dakatarwar da hukumar kula da sufurin jirgin sama ta ƙasar ta yi wa kamfanin ya shafi jigilar cikin gida ne, ba abin da ya shafi jigila tsakanin kasashe ba ne.

    Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA dai ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al'amura da suka faru da jiragen Max Air ƙirar B737, ciki har da lalacewar wilin tayar saukar jirgin ta gaba, da ta janyo wani mummunan al'amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.

    Hukumar Alhazan ta ce tana mai tabbatar wa al'ummar ƙasar cewa dakatarwar ba za ta shafi jigilar alhazan ƙasar da ke gudana ba.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa kamfanin zai tabbatar da kwaso duka alhazan da aka ware masa domin yin jigilarsu.

    ''Muna son gode wa duka 'yan ƙasar da Alhazan dangane da hakuri da juriya da suke nunawa, kuma muna masu tabbatar da cewa za a kammala kwaso mahajjatan ƙasar a kan lokaci kamar yadda aka tsara'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Tuni dai hukumar Alhazan ƙasar ta soma jigilar mahajjatan ƙasar daga Saudiyya zuwa Najeriya

  7. Majalisar Dattijai ta amince da naɗin manyan hafsoshin sojin Najeriya

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da naɗin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa manyan hafsoshin sojin ƙasar.

    Amincewar ta biyo bayan tantance hafsoshin da aka yi a zauren majalisar ranar Alhamis.

    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce a lokacin tantancewar, wadda aka yi a asirce, hafsoshin sojin sun amsa tambayoyi kan lamurran da suka shafi tsaro da kuma halin da ƙasar ke ciki.

    A ranar Litinin, Shugaban Tinubu ya aika wa majalisar da wata takarda yana buƙatar amincewa kan naɗin da ya yi wa manyan hafsoshin.

    Manyan hafsoshin da aka amince da naɗin nasu su ne:

    • Manjo-Janar C.G Musa (Hafsan hafsoshin dakarun Najeriya)
    • Manj-Janar T. A Lagbaja (Babban hafsan mayaƙan ƙasa)
    • Rear Admiral E. A Ogalla (Babban hafsan mayaƙan ruwa)
    • AVM H. B Abubakar (Babban hafsan mayaƙan sama)
    • IGP Kayode Agbetokun (Mai riƙon muƙamin Sufeta-Janar na ƴan sanda)
    • Manjo-Janar EPA Unidianye (Shugaban Hukumar Tattara bayanan sirri na tsaro)
  8. Ce-ce-ku-ce a kan hukuncin 'cakumar mace daƙiƙa 10 ba iskanci ba ne'

  9. Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kuɗin rage raɗaɗin tallafin mai

    ...

    Asalin hoton, other

    Bayanan hoto, ...

    Majalisar wakilan Najeriya ta amince da naira biliyan 500 a matsayin kuƙin rage raɗaɗin cire tallafin mai fetur.

    Majalisar ta amince da kudin ne bayan nazari da buƙatar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar na yin gyara a dokar karin kasafin kudin shekarar 2022.

    Kakakin majalisar Rt. Hon. Abbas Tajudeen, PhD, ne ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar a ranar Laraba, inda ya shugaban kasar ya bukaci a gyara ga dokar da za a ware naira biliyan 500 ga shirin tallafa wa ƴan Najeriya bayan raɗaɗin cire tallafin man da suka shiga.

    Wasikar Shugaba Tinubun na cewa “Na rubuta wa Majalisar Wakilai wannan wasika domin neman amincewarta wajen yin gyara a dokar karin kasafin kuɗin 2022''.

    “Buƙatar ta zama dole saboda a samu kuɗin da ake buƙata don samar da abubuwan da zai rage wahalar cire tallafin man fetur ga ‘yan Nijeriya.

    “Duk da ina fatan majalisar wakilai za ta yi la’akari da wannan bukata cikin gaggawa, don Allah a yarda''.

    A zaman majalisar na ranar Alhamis, wanda kakakin majalisar Tajuden Abbas ya jagoranta, ‘yan majalisar da dama da suka yi magana kan bukatar, sun bayyana goyon bayansu ga cire tallafin mai da kuma shirye-shiryen majalisar na mara wa gwamnatin Tinubu baya kan yadda za a shawo kan illolin da cire tallafin ya jawo wa ƴan Najeriya.

  10. Za a bai wa iyalai miliyan 12 naira 8,000 na tsawon wata shida

    ...

    Asalin hoton, TINUBU/TWITTER

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatin kasar na bai wa gidajen talakawan Najeriya miliyan 12 Naira 8,000 na tsawon watanni shida.

    Hakan na kunshe cikin wata wasika da shugaban kasar ya rubuta wa majalisar wakilai dangane da bukatar gwamnatin Buhari ta karbo bashin dala miliyan 800 domin shirin rage raɗaɗin talauci

    Shugaban kasar na neman amincewar majalisar ne domin samun bashin.

    Don tabbatar da kudin sun isa ga talakawan, Shugaban ya ce za a tura kudin zuwa asusun aiyarsu ta bank.

  11. An gano gawarwaki 87 a yankin Darfur - MDD

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce an gano akalla gawarwaki 87 a Masali na yankin Darfur na kasar Sudan da ake zargin dakarun RSF ne suka kashe sannan suka binne su a kabarin bai daya.

    MDD ta ce ta ce mutanen Masalit na daga cikin wadanda aka binne a wani kabari mara zurfi da ke wajen El-Geneina.

    Tun cikin watan Afrilu ne ake gwabza kazamin fada tsakanin dakarun RSF da sojojin Sudan.

    Dakarun RSF da ƙawayensu masu tayar-da-kayar-bayan yankin Darfur, sun musanta cewa suna da hannu a fadan baya-bayan nan a yammacin Darfur.

    Dubban mutane ne suka mutu, sannan aka tilasta wa miliyoyi barin gidajensu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan da kuma RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakin al-Burhan Mohamed Hamdan Daglo.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla gawarwakin mutum 37 ne aka binne a yankin yammacin Darfur a ranar 20 ga watan Yuni, yayin da wasu 50 kuma aka binne su a wuri guda washegari.

    Daga cikin wadanda aka binne har da mata da kananan yara.

  12. Hotuna: Zafin rana mai tsanani ya auka wa sassan Turai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ƙasashe a kudancin Turai na cikin bala'in zafi rana da ake sa ran zai haifar da wani yanayi mai wahala cikin kwanaki masu zuwa.

    Ana sa ran ma'aunin zafin jiki zai ƙaru da salsiyas 40 a sassan Spain da Faransa da Girka da Croatia da kuma Turkiyya.

    An samu rahotannin cewa mutane da dama da suka hada da 'yan yawon bude ido sun suma saboda tsananin zafi a Italiya. Akalla mutum daya ya mutu.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata ta rufe saman kanta da tawul don samun sauki daga ranar mai bala'in zafi a Rome
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata ƴar yawon bude ido daga Burtaniya ta sami taimako a kusa da Colosseum bayan ta suma saboda tsananin zafi a Rome
    ...

    Asalin hoton, SHUTTERSTOCK

    Bayanan hoto, Wannan matar kuma tana zuba ruwan sanyi a kanta a birnin Turin, arewacin Italiya
    ...

    Asalin hoton, SHUTTERSTOCK

    Bayanan hoto, Masu yawon bude ido sun lullube kansu da tawul a birnin Malaga na kudancin Spain saboda tsananin zafin rana
    ...

    Asalin hoton, SHUTTERSTOCK

    Bayanan hoto, Wasu mata biyu sun sanya hula don kare kansu daga rana mai zafi a Malaga

    Hukumar kula da yanayi ta Italiya ta kira tsananin zafin a matsayin abu mai hatsari da ban tsoro

  13. NCAA ta dakatar da jiragen Max Air ƙirar Boeing 737 daga aiki

    ...

    Asalin hoton, BOEING

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar kula da sufurin jirgin sama ta Najeriya NCAA ta ce ta dakatar da ayyukan jirgin sama na Max Air ƙirar Boeing 737 nan take.

    Da take bayyana dakatarwar a cikin wata sanarwa, Daraktan kula da Ayyuka da Horaswa da kuma ba da Lasisi, Kyaftin Ibrahim Dambazau da kuma Babban Daraktan Hukumar Kyaftin Musa Nuhu suka fitar, hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al'amura da suka faru da jiragen Max Air ƙirar B737.

    A cikin wasikar, hukumar ta NCAA ta lissafa abubuwan da suka faru waɗanda har suka sanya ta ɗaukar wannan mataki.

    A ciki har da lalacewar wilin tayar saukar jirgi ta gaba, da ta janyo wani mummunan al'amari ga jirgin Boeing 737-400 tsakanin tashinsa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukarsa a filin jirgin Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 7 ga Mayu, 2023.

    Hukumar NCAA ta sake soke tashin jirgin Max ƙirar Boeing 737-400 mai lamba 5N-MBD a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) saboda fitar iskar gas mai tsananin zafin a jirgin ranar 11 ga Yuli, 2023.

    NCAA ta kuma cewa ta kafa wata ayarin jami'an bincike da za su bi diddigi game da harkokin kamfanin na Max Air.

    Hukumar ta ce dole sai sun gamsu da sakamakon binciken, kafin ta bai jirgin Boeing 737-400 damar ci gaba da ayyukansa.

  14. Ku saki Emefiele a cikin mako ɗaya - Kotu

    Emefiele

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya ta tuhumi Godwin Emefiele dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sake shi.

    Kotun ta ba da wannan umarni ne a lokacin sauraron ƙara da Emefiele ya shigar don tabbatar da 'yancinsa na ɗan'adam, inda yake ƙalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS take yi.

    A ranar Asabar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele.

    Da farko ta ce Emefiele ba ya hannunta, kafin daga bisani ta tabbatar da cewa ya shiga hannu.

    Tun a daren Juma'a ne, wasu rahotanni suka ce jami'an tsaro sun yi awon gaba da shi, jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga kan muƙaminsa.

    "DSS na tabbatar da cewa Emefiele, dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike," a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam'iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yunƙurin hana su cin zaɓen da aka kammala cikin watan Fabrairu saboda tsarin rage kuɗi a hannun jama'a da ya ƙaddamar da kuma canza fasalin naira.

    Kafin haka, DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta'addanci, har ma aka kai shi kotu kan zarge-zargen.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
  15. Amnesty International ta nada Isa Sanusi sabon shugaban ofishinta a Najeriya

    isa

    Asalin hoton, Isa Sanusi

    Bayanan hoto, Isa tsohon ma'aikacin BBC ne a ofishin Abuja da kuma na London

    Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta duniya Amnesty International ta sanar da naɗa Isa Sanusi, mai fafutukar kare haƙƙin dan'adam kuma tsohon dan jarida a matsayin sabon daraktanta na Najeriya.

    Wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya fitar, ta ce Isa Sanusi zai jagoranci fadada ayyukan bincike da gangamin kungiyar a Najeriya.

    Zai kuma mayar da hankali a kan al'amuran da suka shafi rikice-rikice da ilmi da kare hakkin dan'adam da daidaiton jinsi da sauyin yanayi da shigar da matasa cikin harkokin ingantawa da kare hakkin dan'adam.

    “Nadin Isa Sanusi a matsayin daraktan kasa zai karfafa tasirin kungiyar Amnesty International a Najeriya.

    Yana da gogewar aiki ta tsawon shekara bakwai, abin da ke nufin zai ba da gudummawa wajen ci gaba da ganin tasirin ayyukan Amnesty a Najeriya,” in ji Auwal Musa Rafsanjani.

    Kafin sabon nadin nasa, Isa Sanusi shi ne manajan yaɗa labarai da sadarwa na Amnesty International a Najeriya, mukamin da yake rike da shi tun 2016. Ya kuma taɓa aikin jarida da BBC tsawon shekara 10, sannan ya taɓa zama mataimakin editan jaridar Daily Trust.

    Mallam Isa ya kuma jagoranci ayyukan kare hakkin dan'adam iri daban-daban da horar da masu fafutukar kare hakkin dan'adam a Najeriya.

    Ya yi digirin farko a fannin Ingilishi a Jami’ar Bayero Kano sannan yana da digiri na biyu a fannin aikin jarida daga Jami’ar Landan.

    • Amnesty ta caccaki Najeriya kan kasa kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga
  16. An shigar da nakasassu 500 cikin shirin inshorar lafiya a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Najeriya ta ce ta shigar da nakasassu 500 cikin shirin inshorar lafiya na kasa (NHIS), domin inganta hanyoyin samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

    Babban sakataren ma’aikatar jin kai da ci gaban jama’a, Dakta Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wani taron ba da katin cin gajiyar shirin inshorar lafiya ga waɗanda suka amfana a Abuja.

    A cewarsa, matakin zai tabbatar da samar da ayyukan kula da lafiya cikin sauki ga masu buƙata ta musamman a fadin kasar.

    Gwarzo ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya jagoranci jami'an ma'aikatar lafiya zuwa fadar sarkin Karo Majiji kuma shugaban masu buƙata ta musamman a Abuja.

    Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa hukumar kulla da masu buƙata ta musamman ta ƙasa (NCPWD) ce ta dauki nauyin yin rijistar.

    An dauki matakin ne domin rage wahalhalun da mutane masu nakasa ke fuskanta wajen samun ayyukan kula da lafiya.

    Ya ce gwamnati ta fara aiwatar da shirin ne a babban birnin tarayya kuma ana sa ran za a faɗaɗa shi zuwa jihohi 36 na Najeirya.

    • Najeriya ta amince da yi wa 'yan ƙasar riga-kafin maleriya
  17. MDD ta bukaci Ghana kada ta kori ƴan gudun hijirar Burkina Faso

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Ghana ta dakatar da shirin korar 'yan gudun hijirar da suka shiga kasarta daga Burkina Faso.

    Hukumar ta ce ta damu matuƙa da rahotanni da ke cewa ɗaruruwan 'yan Burkina Faso akasari mata da yara ana tilasta mayar da su gida daga Ghana bayan tserewa rikici a kasarsu.

    MDD ta ce a shirye take ta taimaka wa Ghana da duk abin da za ta bukata domin walwalar 'yan gudun hijiran.

    Mutane sama da miliyan biyu ne rikicin kungiyoyin masu iƙirarin jihadi ya tilasta wa tserewa daga Burkina Faso, inda wasu ke samun mafaka a kasashen yankin Sahel.

    • MDD ta roki Tanzania ta daina korar 'yan gudun hijira
  18. Shugabanni Afrika na fafutukar kawo karshen yaƙin sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Wasu kasashe hudu na gabashin Afirka karkashin jagorancin Kenya wanda Masar ne ke shirin daukar nauyin taron da zai mayar da hankali kan yada za a kawo karshen yakin Sudan.

    Ƙasashen sun matsa kaimi wajen tura dakaru zuwa yankin da za su kare fararen hula tare da tabbatar da ganin an kai agajin gaggawa ga miliyoyin mutanen da suka makale a yankin yaƙi.

    Kusan wata uku kenan da ake gwabza yaƙi a Sudan, lamarin da ya haifar da tsananin bukatar agaji a yankunan Kasar.

    Wakiliyar BBC, ta ce Bangarorin dakaru za su tura wakilansu taron, duk da dai kokarin da aka yi a baya wajen sulhunta rikicin kasar daga yankunan da ketare ya ci tura.

    A ranar Laraba, shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar, da Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed su hadu a birnin Alkahira inda suka tattauna rikicin na Sudan.

    • An ceto jariran da rikicin Sudan ya ritsa da su a gidan marayu
    • Yadda ƴan bindiga ke ƙona ƙauyuka ƙurmus a Darfur
  19. An gano shaidu kan kifewar jirgin bakin-haure a Girka

    ...

    Asalin hoton, GREEK COAST GUARD

    Bayanan hoto, ...

    Wani bincike na BBC ya gano shaidu da ke haifar da shakku a kan masu kula da gabar tekun Girka, game da bayanansu na abin da ya janyo nutsewar jirgin bakin-haure a tekun Mediterranean cikin watan jiya.

    Tun farko, mutum 82 aka tabbatar sun nutse a tekun amma yanzu akwai fargaba kusan mutane 500 ne suka mutu.

    Wakilin BBC ya ce, Mutum biyu da suka tsira daga jirgin da ya nutse a Athens sun shaida wa BBC cewa jami'an da ke kula da gabar tekun Girka ne suka janyo kifewar jirgin a wani mummunan yanayi a kokarin janyo jirgin zuwa gaɓa.

    Sannan sun ce an bukaci su yi shiru da bakunansu kuma an umarce su dora laifin abin da ya faru kan wasu 'yan Masar tara da ake zargi da safarar mutane.

    Mahukuntan Girka dai sun ki amincewa a dora musu wannan laifi.

    • 'Maimakon su cece mu sai suka kifar da jirginmu'
  20. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da war haka.

    Aisha babangida ce ke fatan kasancewa da ku a yau ranar Alhamis don kawo muku labarai iri-iri daga Najeria da sauran sassan duniya.

    Ku kasance da mu