Shugaban Najeriya ya ba da umarnin rage nau'o'in haraji

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Zafin rana na neman hana mahajjata sallar Juma'a a Ka’aba

    ...

    Asalin hoton, AP

    Hukumomin kasar Sa’udiyya sun bayar da sanarwa, cewa yanayin zafi zai iya kai maki 50 a ma'aunin yanayi a gobe Jumma’a. Saboda haka, suka shawarci mahajjata da sauran jama’a da su yi sallar Juma’a a masallatan da ke unguwannin birnin Makka, wato ba sai sun je Harami ko kuma Ka’aba ba.

    Hukumomin sun ɗauki matakin ne domin kauce wa hadarin da ke tattare da tsananin zafin da za a yi fama da shi a goben.

    A nata bangaren, hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON ta jaddada wa mahajjatan Najeriya da su dauki matakan guje wa tsananin zafin ranar da za a fuskanta ta hanyar bin shawarar hukumomin na Saudiyya na yin sallar juma’a a masallatan da ke kusa da inda suke zama.

    Daraktan ayyukan gudanarwa da al’amuran ma’aikata na hukumar, Dokta Ibrahim Sodangi ya shaida wa BBC cewa bijire ma wannan shawarar na iya sanya mahajjata a wani mawuyacin hali ta hanyar haifar da kalubale ga lafiyar jikinsu.

    Daraktan ya bayyana cewa an shafe shekaru da dama ba a sami yanayi mai irin wannan tsananin zafin ba don haka ya ƙara yi kira ga mahajatan Najeriya su yi ƙokarin guje wa shiga rana ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba.

  2. Matsalar lalata da ƙananan yara na tsananta a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police

    Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta samu fiye da mutum 100 da ake zargin yin lalata da ƙananan yara a cikin watanni uku da suka gabata.

    Jihohi da dama a Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar cin zarafin yara tare da yi masu fyaɗe, wanda mutane da yawa suka bayyana a matsayin annoba.

    Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa manema labarai cewa, hukumomi sun damu da yadda ake samun ƙaruwar masu lalata da ƙanann yara a jihar.

    "A halin yanzu ana kan binciken kusan ƙararraki 83, wanda ke nuna ƙudurin rundunar na hukunta duk wani abu da ya shafi irirn wadannan laifukan a jihar," in ji shi.

    Mista Hundeyin ya bayyana cewa a tsakanin watan Afrilu zuwa 14 ga watan Yuni an samu rahoton aikata laifukan fyaɗe da kuma laifuka 56 na rikicin cikin gida.

    Ya kuma bayyana cewa an gurfanar da mutane 99 a gaban kotu.

    A Najeriya laifukan da suka shafi lalata da kananan yara na neman su kai matakan tashin hankali.

    Ɗaruruwan abubuwan da suka faru ba a bayar da rahotonsu saboda cin hanci da rashawa da ke yaɗuwa, da ƙyamar da ake nunawa waɗanda abin ya shafa da kuma tafiyar hawainiyar shari'a.

    Masu fafutuka na ci gaba da kokawa kan yadda ake cigaba da cin zarafin yara da kuma yi masu fyade, da kuma ƙarancin hukuncin da ake yi wa masu aikata irin waɗannan laifukan a ƙasar.

    Sun daɗe suna matsawa kan daukar tsauraran matakai don magance matsalar.

  3. Kylian Mbappe ya kai ziyara ƙasar Kamaru

    ...
    Bayanan hoto, Jama'a da dama sun kewaye da wasan bayan saukansa a jirgi

    Kylian Mbappe, kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafar Faransa kuma dan wasan gaba na Paris Saint-Germain, ya isa ƙasar Kamaru.

    Yana tare da mahaifinsa, Wilfred Mbappe, wanda aka haifa a Douala, babban birnin Kamaru.

    Wannan ita ce ziyarar farko da Mbappe ya kai ƙasar.

    A ziyarar tasa ta kwanaki uku, yana shirin buga wasan sada zumunta da kungiyar kwalon ƙafa da ke rukuni na biyu a ƙasar kuma mallakar tsohon dan wasan tennis Yannick Noah.

  4. Kotu ta bayar da belin Abba Kyari

    Abba Kyari
    Bayanan hoto, Abba Kyari

    Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya bayar da belin tsohon shugaban bangaren 'yan sanda masu kai ɗaukin gaugawa, Abba Kyari bayan ya shafe watanni 18 a tsare.

    Kotun ta ce an bayar da belin ne kasancewar, dakataccen jami'in ɗansandan bai tsere daga gidan yarin Kuje ba a lokacin da aka kai hari gidan yarin a ranar 5 ga Yuli, 2022.

    Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa, yadda Kyari da tawagarsa suka ki tserewa a lokacin da aka kai wa gidan yarin hari, inda kusan kashi 90 cikin 100 na fursunonin suka tsere, ya tabbatar da cewa Kyari a shirye yake ya fuskanci duk wani zargi da ake yi masa.

    Alkalin ya ci gaba da cewa duk zargin da ake yi masa za a iya bayar da belinsa a kan su, kuma ba a tunanin cewa zai gudu.

    An kama Abba Kyari tare da wasu ‘yan tawagarsa a watan Fabrairun 2022 bayan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta yi zargin cewa Kyari na da hannu cikin wasu miyagun kwayoyin da aka kama.

    Rundunar ta IRT ta kama Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, a cikin watan Janairun 2022 bisa zargin su da safarar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 21.25, inda daga bisani suka mika waɗanda ake zargin ga hukumar NDLEA tare da hodar da aka kama su da ita.

    An saki Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne daga gidan yari bayan sun gama fuskantar hukuncin da aka yanke musu.

    Daya daga cikin lauyoyin da ke kare dakataccen ɗan sandan a kotun, Hamza Kyari, ya ce Abba Kyari ba zai iya komawa gida ba domin yana da wata tuhumar da zai amsa a gaban wani alkali a babban kotun tarayya da ke Abuja, inda har yanzu ake sauraron buƙatar belin da ya shigar.

  5. Wane ne Messin Turkiyya da Real Madrid ke nema

  6. INEC ta maka Hudu Ari a Kotu

    Yunusa Hudu Ari
    Bayanan hoto, ...

    Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya (INEC) ta shigar da tuhume-tuhume shida a gaban kotu, kan dakataccen kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sannun shugaban sashen wayar da kan al'umma na hukumar, Festus Okoye, ta ce an shigar da ƙarar ce a babbar kotun jiha da ke Yola, a jihar Adamawa.

    Sanarwar ta kuma tabbatar da samun takardar kammala bincike kan laifukan da suka shafi zabe daga hannun 'yan sanda, bayan kammala bincike kan laifukan zabe da aka yi a babban zaben na 2023, ciki har da wanda ya shafi Ari.

    Sanarwar ta ce, “Kamar yadda sashe na 145(1) na dokar zabe ta 2022 ya tanadar, laifin da aka aikata a ƙarƙashin dokar za a iya gurfanar da shi a gaban kotun majistare ko kuma babbar kotun jihar da aka aikata laifin, ko kuma babban birnin tarayya, Abuja.

    Bayanin ya ƙara da cewa Kotu ta sanya ranar Laraba 12 ga Yulin 2023 don fara shari’ar.

    Yunusa-Ari dai ya shiga matsala ne bayan kammala zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar 15 ga Afrilun 2023, lokacin da ya bayyana Aisha Dahiru ‘Binani’ ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben da aka gudanar a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.

  7. Shugaban Najeriya ya ba da umarnin rage nau'o'in haraji

    ...

    Asalin hoton, BOLA TINUBU/TWITTER

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sa hannu a kan umarnin shugaba guda huɗu, da nufin rage wasu nau'o'in haraje-haraje ga al'ummar ƙasar.

    Ɗaya daga cikin umarnin shugaban ƙasar shi ne dakatar da harajin kashi biyar a kan ayyukan wayoyin sadarwa da kuma dakatar da harajin da aka tsawwala a kan kayan da ake sarrafawa a cikin gida.

    Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman da al'amuran sadarwa, Dele Alake ya faɗa ranar Alhamis cewa shugaban ƙasar ya kuma sa hannu a kan Dokar Kudi ta 2023, wadda a yanzu ta jingine fara aiki da sauye-sauyen da ke cikin dokar daga ranar 23 ga Mayun 2023 zuwa 1 ga Satumban 2023.

    A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, an yi hakan ne domin tabbatar da bin ka’idar ba da sanarwa ko notsi na aƙalla kwana 90 ga sauye-sauyen haraji kamar yadda yake ƙunshe a Manufar Tattara Haraji ta Kasa ta 2017.

    Shugaba Tinubu ya kuma rattaba hannu a kan dokar karɓar harajin shigo da kaya da aka yi wa garambawul ta 2023, inda ya canza ranar fara aiki da dokar harajin daga 27 ga watan Maris zuwa 1 ga Agustan 2023 kamar yadda yake cikin Manufar Karɓar Haraji ta Ƙasa.

    Tinubu ya kuma bayar da umarnin dakatar da wani sabon haraji mai suna Green Tax da aka ɓullo da shi kan robobin da ake amfani da su sau ɗaya, sannan a jefar, ciki har da mazuban roba da goran roba, ya kuma dakatar da wani nau'in haraji da ake karɓa a kan wasu nau'o'in motoci da ake shiga da su ƙasar.

  8. Yevgeni Prigozhin yana Rasha

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Wagner, Yevgeny Prigozhin - wanda ya jagoranci tawaye na gajeren lokaci ga Rasha cikin watan jiya - yana ƙasar Rasha ne ba Belarus ba, in ji shugaban Belarus.

    Sanin taƙamaiman inda Prigozhin yake, abu ne da ya kasance mai ɗaure kai tun bayan ganin da aka yi masa a kudancin Rasha lokacin boren da ya jagoranci sojojinsa.

    A ƙarkashin yarjejeniyar kawo ƙarshen turka-turkar, an yi watsi da tuhumar da ake yi wa Prigozhin kuma za a bar shi ya koma Belarus tare da magoya bayansa.

    Shugaban Belarus Alexander Lukashenko ne ya taimaka wajen ƙulla yarjejeniyar.

    Kwanan baya ne, Mista Lukashenko da ke mulkin Belarus tun 1994, ya ce Prigozhin ya isa Belarus.

    Amma, a ranar Alhamis Mr Lukashenko ya shaida wa manema labarai cewa: "Prigozhin yana St Petersburg, ba ya cikin ƙasarsa."

    BBC ta bi sawun jirgin Prigozhin mai zaman kansa da ya tashi zuwa Belarus a ƙarshen watan Yuni, kuma ya koma Rasha da yamma.

    Tun daga lokacin, jirgin ya yi ta zirga-zirga tsakanin St Petersburg da Moscow - ko da yake ba a bayyana ko Mista Prigozhin na ciki ba.

    BBC ba ta iya tabbatar da ikirarin Mr Lukashenko game da inda shugaban na Wagner yake ba.

    A ranar Alhamis ɗin nan, Mr Lukashenko ya kara da cewa "kamar yadda na sani" sauran mayaƙan Wagner na nan a sansanoninsu - waɗanda za su iya hadawa da na gabashin Ukraine ko kuma sansanin horo a yankin Krasnodar na Rasha.

    Shugaban Belarus ya ce tayin Wagner na tura wasu mayaƙa zuwa Belarus - wanda ya firgita makwabtanta ƙasashen Nato - har yanzu yana nan.

    • Dole mu gurfanar da mayaƙan Wagner a gaban kuliya - Putin
    • Shin me juyin mulkin Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
  9. Gwamnatin Kwara ta janye tsarin aikin gwamnati na kwana uku a mako

    ...

    Asalin hoton, KWARA STATE GOVERNMENT

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Kwara ta sanar da soke umarninta na mayar da aikin gwamnati tsawon kwana uku cikin mako ga ma'aikatan jihar.

    A ranar 5 ga Yuni ne, shugabar ma’aikata ta jihar, Mrs Susan Oluwole ta fitar da wata sanarwa wadda a cikin take bayyana matakin rage kwanakin aiki daga biyar zuwa uku a mako.

    Ta ce gwamnatin Kwara a yanzu ta janye matakin ne don bai wa gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago damar tsara hanyoyin da za a bi wajen shawo kan illolin cire tallafin man fetur da Najeriya ta yi ga rayuwar ma’aikata.

    A sanarwar da ta aika wa shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs), Mrs Oluwole ta ce jihar Kwara ta yi watsi da matakin da gwamnati ta ɗauka tun da farko.

    Sanarwar ta kuma ce: “An umurce ni, na sanar da dukkan shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati (MDAs) cewa an janye umarnin rage kwanakin aiki; Don haka, dukkan ma'aikata su ci gaba da zuwa aiki tsawon kwana biyar a mako, daga ranar 10 ga watan Yulin 2023".

    Ta kara da cewa "Ma'aikatan da ba su faɗa cikin tsarin rage kwanakin aikin ba, za a ba su alawus na musamma don nuna godiya."

    Ma’aikatan da aka kebe tun farko sun hadar da malamai, ma’aikatan lafiya da sauran nau’o’in ma’aikatan da ke samar da muhimman ayyuka a jihar.

  10. Ana gudanar da babban taro kan ƙirƙirarriyar basira a Geneva

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Majalisar Ɗinkin Duniya za ta buɗe wani babban taro da za a baje-kolin mutum-mutumi iri daban-daban masu amfani da fasahar ƙirkirarriyar basira ranar Alhamis a Geneva.

    Ƙungiyar Harkokin Sadarwa ta Duniya ITU ce ta ɗauki nauyin taron, wanda zai mayar da hankali kan yadda za a yi amfani da ƙirƙirarriyar basira wato AI wajen tallafa wa aikin Majalisar Dinkin Duniya da inganta rayuwa da kuma sauƙaƙa wa al'umma.

    Za a nuna mutum-mutumi da yawa da suke da ƙwarewar kwaikwayon fikirar ɗan'adam ta fuskar taimakawa don gudanar da wasu ayyuka a ma'aikatu.

    Sai dai saɓanin fargabar cewa mutum-mutumi mai aiki da ƙirkirarriyar basira na iya haifar da illolin da za su haddasa rashin aikin yi ga ɗan'adam, taron zai samar da wasu dokoki da za su ƙayyade ayyukan fasahar.

    Gagga-gaggan kamfanonin sadarwa na duniya irinsu Google da Amazon da Microsoft, da sauran ƙwararru a fannin fasahar sadarwa da wakilan gwamnatoci ne za su albarkaci taron.

    • Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam
    • Mutum-mutumin da zai kare mata daga jin mummunan rauni in an yi hatsari
  11. Majalisar dokokin Ghana ta amince da dokar haramta auren Jinsi

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Ghana ta goyi bayan wasu gyare-gyare a kudurin dokar haramta luwadi da maɗigo wanda zai iya sa a yankewa masu yi hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

    Kudurin neman yi wa dokar kwaskwarima ya haramta bayar da tallafin kudi domin harkokin ‘yan luwadi da madigo.

    Dama dai an haramta wa maza neman junansu a Ghana, to amma sabon kudirin dokar ya hada da haramta wa mace neman yar uwarta.

    ‘Yan majalisar daga jam’iyyu daban daban sun tafka muhawara kan rahoton wani kwamiti da aka ba shi aikin yi wa kudurin kwaskwarima.

    Kungiyoyin ‘yan majalisar wakilai suma sun goyi bayan gyare-gyaren, za kuma a sake nazarin gyare-gyaren kafin su zama doka.

    Wata yar majalisa daya tilo da ta nuna dan sassauci a fili ga masu luwadi da madigo to fuskanci sowa har sai da ta mika wuya.

    A watan Agustan 2021 ne aka fara gabatar da kudurin dokar hana auren jinsi a zauren majalisar Ghana, sai dai an rika fuskantar mummunar suka gida da waje.

    An shigar da kararraki da dama a gaban kotunan kasar da nufin kalubalantar kudurin.

    Wadanda suke adawa da shi sun ce idan ya zama doka zai tauye wa 'yan luwadi da madigo yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su.

    Sai dai masu goyon bayan kudirin sun ce zai taimaka wajen kiyaye kyakkyawan tsarin iyali na al’ummar Ghana.

    Majalisar za ta sake bibiyar kudirin kafin amincewa da shi don zama doka.

  12. Likitoci sun bai wa gwamnatin Najeriya wa'adin mako biyu ta cika alkawari

    ...

    Asalin hoton, ISTOCK

    Bayanan hoto, ...

    Likitocin Najeriya da ke aiki a asibitocin gwamnati sun bai wa gwamnatin kasar wa'adin mako biyu ta cika musu alkawuran da ta daukar musu a jarjejeniya da suka cimma a baya.

    Gwamnatin da ta shude ce dai ta alkawarta warware duka matsalolin da kungiyar bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da likitocin suka yi a watan Mayu, to amma kungiyar ta ce babu abin da aka yi game da cika musu alkawari tun bayan da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki.

    A cikin wata sanarwa da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fitar, ta ce ta yi imanin cewa wa'adin mako biyu ya isa hukumomi su magance mata matsalolinta.

    Matakin na zuwa ne, wata guda bayan da likitocin suka ce za su bai wa sabuwar gwamnati lokaci domin duba lamarin.

    Wasu daga cikin bukatunsu sun hada da ƙarin kashi 200 na albashinsu, da biyan su wasu kukakde da suka ce suna bin gwamnati, da kudin horarwa, da batun cike gurbin ma'aikata da suka bar aiki, domin magance ''matsalar karancin likitoci a asibitocin kasar''.

    Ƙungiyar ta yi gargadin cewa matukar aka kasa biya mata bukatunta zuwa ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki, "Fannin kiwon lafiyar kasar zai sake shiga wani hali" a fadin ƙasar.

    Rashin isassun kuɗaɗe, da rashin isassun kayan aiki da karancin albashin ma’aikatan kiwon lafiya ya sa kwararrun likitoci da dama na neman ayyuka a ƙasashen waje.

    • Abin da ya sa likitocin Najeriya suke neman aiki a kasashen waje
    • Yadda tsadar rayuwa ta tilastawa likitocin Najeriya ficewa zuwa ƙasashen waje
  13. Kenya ta jinkirta bude kan iyakarta da Somaliya saboda hare-hare

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Kenya ta ce za ta jinkirta bude kan iyakarta da Somaliya bayan wasu hare-hare da aka kai cikin kasar da ake alakantawa da kungiyar masu iƙirarin jihadi ta al-Shabab.

    Ministan cikin gida Kithure Kindiki ya ce matakin sake bude kan iyakokin da ake shirin yi cikin watan Yuli ba zai samu ba.

    Ya ce an dauki matakin ne sakamakon "barazanar hare-hare da rshin tsaro da makwabtan kasashen yankin ke fuskanta".

    Hakan na zuwa ne yayin da aka kashe fararen hula biyar da ‘yan sanda takwas a wasu mabambantan hare-hare da aka kai kusa da kan iyakar a watan da ya gabata.

    Tun a shekarar 2011 ne aka rufe iyakar, saboda hare-haren da kungiyar al-Shabab ke kai wa, wadda ke tayar da ƙayar baya ga gwamnatin tarayya a Mogadishu.

    Ministan ya kuma sanar da cewa, nan da wasu makwanni kaɗan, ƙasar Kenya za ta fara hada 'yan gudun hijirar da suka zauna a sansanonin, a wani bangare na sabuwar hanyar kula da su.

    Ya ce sabon tsarin zai bai wa hukumomi damar kawar da "wakilan ta'addanci da masu aikata laifuka da ke amfani da wuraren 'yan gudun hijira don cutar da al'ummomin da ke karɓar bakuncin".

  14. Zanga-zanga ta barke a Tel Aviv bayan murabus din shugaban ƴan sanda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Isra'ila sun fanTsama kan tituna tare da toshe babbar hanyar shiga birnin Tel Aviv, bayan murabus din da kwamishinan 'yan sandan birnin ya yi.

    Amichai Eshed ya ce ya zaɓi ya yi murabus, maimakon ya ba da kai ga matsin lambar wasu 'yan siyasa da ke son ya nuna karfi a kan masu zanga-zangar da suka kwashe makwanni suna nuna adawa ga garambawul a bangaren shari'a.

    Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce indai har gwamnati za ta yanke shawarar korar kwamishinan 'yan sandan Tel Aviv, don kawai ya ki amincewa ya nuna karfi a kan su, to kuwa ba shakka an kama hanyar wani abun daban ba dimukradyya ba.

    Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna 'yan sanda na feshe masu zanga-zangar da ruwa, yayin da kuma ake dukan wasu.

    Mutum daya ne ya ji rauni bayan wani direban mota ya afkawa masu zanga-zangar a kan babbar hanyar.

  15. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da war haka

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Alhamis domin kawo muku irin labaran da ke faruwa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.