Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Najeriya ta bayyana wuraren da za a iya samun ambaliya a bana

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Ibrahim Yusuf Mohammed and Haruna Kakangi

  1. Gawawwaki fiye da 50 ne ba a gano danginsu ba, bayan hatsarin jirgin Indiya

    Gawawwaki fiye da 50 ne har yanzu ba a gano danginsu ba, wata ɗaya bayan mummunan hatsarin jirgin ƙasan da ya halaka mutane akalla 293 a Indiya.

    Hatsarin ya faru ne ranar 2 ga watan Yuni a jihar Odisha da ke gabashin ƙasar, lokacin da wani jirgin ƙasa dauke da fasinja ya yi karo da wani jirgin dakon kaya da ke tsaye.

    Mutane sama da 1,000 ne suka jikkata, a abin da ya kasance ɗaya daga cikin hadurran jirgin ƙasa mafi muni da aka taɓa gani a Indiya cikin wannan ƙarni.

    Tuni dai aka gyara wurin da hatsarin ya auku, har ma an ci gaba da harkoki, amma iyalai da dama sun ce sun kasa gano gawawwakin 'yan'uwansu.

  2. Najeriya ta ce za ta rage magungunan da ake shigarwa ƙasar da kashi 20%

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage shigaR da magunguna cikin ƙasar daga kashi 60 zuwa kashi 40 kawai cikin 100 domin bunkasa harkar sarrafa magunguna a cikin gida.

    Mai bai wa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkar lafiya, Salma Anas-Ibrahim ce ta bayyana hakan a wani taron ƙarawa juna sani da aka shirya domin karfafa dabarun hadin gwiwa tsakanin Hukumar Lafiya ta Duniya a Abuja.

    A cewarta, wannan wani ɓangare ne na burin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya gaba da nufin cike giɓin da ake samu a fannin kula da lafiya na ƙasar.

    Sauran fannonin da sabuwar gwamnatin za ta fi bai wa fifiko sun haɗar da haɓaka damar samun ayyukan kula da lafiya ga kowa da kowa da shigar da al'umma cikin shirin inshorar lafiya na ƙasa da aƙalla kashi 40% don tabbatar da ganin duk 'yan Najeriya ciki har da rukunin al'umma masu ƙaramin ƙarfi.

    • Yadda sabon tsarin canji na CBN zai shafi darajar naira
    • Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
  3. Hotuna: sakamakon tashin hankalin da aka yi a Jenin

    Mazaunan Jenin a arewacin Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaya, sun wayi gari da ganin ɓarnar da aka yi a kan titunan unguwar wadda ta ƙunshi ƙonannun motoci bayan arangamar cikin dare.

    Ga yanayin da aka tashi da shi da safiyar yau:

  4. Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir zai nemi tazarce

    Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce za a gudanar da zaɓukan ƙasar da aka daɗe ana jira a shekara mai zuwa karo na farko tun bayan da ƙasar ta samu 'yancin kanta.

    Mista Kiir ya kuma ce zai yi takarar neman tazarce, inda yake kan mulki tun daga 2011.

    Sai dai rikici ya ci gaba da ɗaiɗaita ƙasar har bayan samun 'yancin kan - yaƙin basasa ya ɓarke a 2013 lokacin da shugaban ƙasar ya ɓata da jagoran adawa Mista Machar.

    An saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma kafa gwamnatin haɗin kai a watan Agustan 2018 don kawo ƙarshen yaƙin na shekara biyar.

    Sai dai yarjejeniyar ta ƙare tun a 2022, inda aka cimma yarjejeniyar tsawaita ta don lalubo bakin zaren ƙalubalane da suka hana aiwatar da ita yadda ya kamata.

  5. An kama masu zanga-zanga 4,000 a Faransa zuwa yanzu

    Ma'aikatar shari'a ta Faransa ta tabbatar da cewa kusan mutum 4,000 aka kama kan zanga-zanga da fashe-fashen shaguna da aka shafe kwanaki ana yi.

    Tarzomar ta faru ne bayan kisan da ɗan sanda ya yi wa wani matashi a makon da ya gabata.

    Kusan ƴan sanda 800 aka jikkata a boren. Akwai kuma kusan gine-gine 1,000 da aka kai wa hari ko aka lalata, akasari da tartsatsin wuta.

    Zanga-zangar ta lafa tun daga ranar Lahadi, amma a ranar Talata 'yan sanda a birnin Paris sun tabbatar da kama mota makare da kilogram 300 na kayan wuta.

    Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da daftarin doka da zai taimaka da kuɗaɗe wajen gyaran tittuna da gine-gine da motoci da sauran kayayyakin da aka barnatar a zanga-zangar.

  6. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da war haka

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Laraba domin kawo muku irin labaran da ke faruwa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.