Matsalar tsaro ta fara raguwa Najeriya - Ribadu

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Habasha ta mayar da martani ga rahoton BBC kan takardun haihuwan 'yan gudun hijira

    ..

    Asalin hoton, bbc

    Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Habasha (RRS) ta mayar da martani ga rahoton BBC a makon da ya gabata cewa ba a bayar da takardar shaidar haihuwa ga jariran da iyaye ‘yan gudun hijirar Eritiriya suka haifa ba.

    Iyayen sun ce hakan na kawo cikas ga haduwar iyali.

    RRS ta kira ikirarin cewa "zargin ba shi da tushe"

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce "ana yin rajista tun watan Nuwamba 2022 kuma an yi wa yara 'yan Eritrea 2,149 rajista.

    Sai dai sanarwar ba ta yi magana kan ko an bayar da takardar shaidar haihuwa da iyalai ke bukata ba ko a'a.

    Wani mutum da ke zaune a Jamus ya shaida wa BBC cewa ya dade yana jiran ya kawo matarsa ​​da 'ya'yansa su zauna da shi amma ofishin jakadancin Jamus na buƙatar takardun haihuwa kafin ya ba da bizar ga jariran.

    "Na ga amsa daga RRS. Matsalarmu ba rajista ba ce – abin da muke bukata shi ne takardar shaidar haihuwa wadda ofishin jakadancin Jamus ke nema,” in ji wani uba.

    Wani kuma ya ce: “Matanmu sun kwashe watanni suna zuwa ofisoshin RRS suna neman takardar shaidar haihuwa amma duk da haka har yanzu muna jira duk da alkawuran da aka sha yi mana.”

  2. An kashe Falasɗinawa bakwai yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da samame a birnin Jenin

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Fiye da sa'o'i goma sha biyu bayan da sojojin Isra'ila suka fara wani abin da suka bayyana a matsayin farmakin yaki da ta'addanci, ana ci gaba da jin karar fashewar wasu abubuwa da kuma musayar wuta a birnin Jenin.

    Jenin ya fuskanci hare-hare da dama daga sojojin Isra'ila a cikin 'yan watannin nan, amma wannan shi ne mafi muni kuma ya kasance mafi tsayi a cikin shekaru masu yawa.

    Daruruwan sojojin Isra'ila da ke samun rakiyar jiragen sama marasa matuki da kuma motocin katafila masu rusa gine-gine na cigaba da gudanar da samame a birnin.

    Falasdinawa sun yi ta jifan sojojin Isra'ila daga bayan shingen kan tituna da ke ci da wuta. Akalla Falasdinawa 7 ne suka mutu sannan wasu tamanin suka jikkata.

    Wani mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila Birgediya-Janar Daniel Hagari ya ce aikin na iya fadada zuwa yankunan arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

  3. Ana taƙaddama kan ɗalibar da ake zargin ta ƙara wa kanta makin JAMB

  4. Akwai buƙatar gina ban-ɗaki miliyan huɗu duk shekara a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce Najeriya za ta bukaci ban-ɗaki miliyan 3.9 a duk shekara domin cimma burin kawo karshen ba-haya a fili nan da shekarar 2025.

    Dakta Jane Bevan, shugabar sashen kula da ruwa da tsaftar mahalli ta UNICEF, ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron kwanaki biyu na masu sana’ar sana'ar ban-daki karo na farko a Abuja.

    Bevan ta ce yawan ban-dakuna da ake samarwa a kowace shekara a yanzu ya tsaya ne kan guda 180,000 - 200,000, tana mai bayyana hakan a matsayin wanda bai isa ba.

    Ta ce taron ya zo a lokacin da ya kamata domin masu gidajen su na da muhimmanci wajen kawo karshen matsalar yin ba-haya a fili a Najeriya.

    A cewarta, kamfanoni masu zaman kansu na da rawar da za su taka wajen karfafa ɓangaren tsaftar muhalli a kasar.

    Bevan ta ce mutane miliyan 48 ne ke yin ba-haya a fili, yayin da miliyan 95 ba su da hanyoyin da suka dace na tsaftar muhalli.

  5. Matsalar tsaro ta fara raguwa Najeriya - Ribadu

    ...

    Asalin hoton, D. Olusegun/Twitter

    Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi iƙirarin cewa rashin tsaro ya ragu cikin mako biyu bayan naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron kasar.

    Ribadu wanda ya yi wannan furuci bayan wata ziyara da hafsoshin tsaron suka kai wa Shugaba Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja, ya ce hakan ya tabbata ne saboda ƙwararrun hannu da aka zaɓa a matsayin masu jagorantar sha'anin tsaron Najeriya.

    Ya kara da cewa sun ziyarci shugaban ƙasar ne don su nuna godiya da damar da aka ba su, ta bayar da irin tasu gudunmawar wajen ci gaban ƙasa, za kuma su yi aiki tukuru waje tabbatar da ingantaccen tsaro a fadin kasar.

    Ya ce shugaba Tinubu ya bayar da tabbacin cewa zai ba su cikakken goyon baya domin gudanar da ayyukansu.

    Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai babban hafsan tsaro, Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja da babban hafsan sojin ruwan Najeriya, Rear Admiral Emmanuel Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Hassan Abubakar, da kuma mukaddashin babban sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun.

    ,,,

    Asalin hoton, D. Olusegun/Twitter

  6. Gambia ta buƙaci kamfanin Indiya ya biya ta diyya kan 'gurbataccen' maganin tari

    ...

    Wasu iyaye a kasar Gambia sun fara shari'a kan gwamnati, da wani kamfanin harhada magunguna na kasar Indiya, da kuma wani mai shigo da magunguna kan wasu gurbatattun maganin tari da suka haddassa wasu mae-mace da dama.

    Iyayen guda goma sha tara na neman diyyar kusan dalar Amurka miliyan 4.7 saboda mutuwar yaran da ake zargi sun yin amfani da magungunan da aka shigo da su daga Indiya.

    Wannan dai shi ne karon farko na shari'a tun bayan da akalla yara 70 suka mutu a Gambia bayan shan gurbataccen maganin tari a bara.

    Tawagar lauyoyi daga ƙungiyar lauyoyin Gambia da ƙungiyar lauyoyin mata ta Gambia ne ke wakiltar iyayen.

    Takardun kotun sun kuma ba da sunan ma'aikatar lafiya da hukumar kula da magunguna. Suna son ma’aikatar da hukumar kula da harkokin su amince da cewa sun gaza wajen gudanar da ayyukansu na kayyade shigowa da kuma sayar da magunguna a kasar.

    Suna kuma neman a ba da sanarwar cewa 'ya'yansu sun mutu daga maganin tarin da aka shigo da su daga Indiya kuma a kwace lasisin wanda ya shigo da kayan.

    Idan aka yi nasara a Babbar Kotun, kowane cikin iyayen za su sami fiye da dala dubu tamanin da uku a matsayin diyya da kuma karin dala dubu dari da sittin da bakwai saboda radadin da suka sha.

  7. Likitoci sun yi gargaɗi game da ƙaruwar cutar ƙyanda a Sudan

    Sudan fight

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A watan Afrilu ne aka fara rikici tsakanin sojoji da dakarun RSF masu ta-da-ƙayar-baya

    An samu ƙarin ɓarkewar cutar ƙyanda a Khartoum, babban birnin Sudan, saboda faɗan da ake ci gaba da gwabzawa, ya hana aikin allurar riga-kafi, wani likitan yara ya faɗa wa BBC.

    Da yake jawabi ta cikin wani shiri kan rayuwa a Sudan mai taken Sudan Lifeline, Dr Mohamed al-Taher, wanda ke zaune a Khartoum, ya ce ana fama da ƙarancin alluran riga-kafi, abin da ka iya janyo ɓarkewar cutuka a tsakanin ƙananan yara.

    "Alhakin ma'aikatar lafiya ne ta samar da riga-kafi, amma ba za ta iya sauke wannan nauyin ba musamman ta fannin alluran riga-kafi," in ji shi..

    "Akwai ƙarancin alluran riga-kafin ƙyanda kuma tuni aka samu yaran da suka kamu da cutar, sannan ana tsammanin lamarin zai yi tsanani... Cutar na iya tsananta saboda jikinsu ba zai iya bijirewa ƙwayoyin cutar ba."

    Yayin da ake ci gaba da luguden bama-bamai a unguwannin birnin masu cunkoson jama'a, akwai matuƙar hatsari a yi ƙoƙarin kai wa ga asibitocin da ke can.

    Ƙungiyar likitocin ba da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta yi gargaɗin cewa yayin da mutane ke tserewa gidajensu, akwai ƙaruwar cutukan ƙyanda da rashin abinci mai gina jiki a sansanonin da ke cikin jihar White Nile, kudu da babban birnin Sudan.

    Ƙungiyar likitocin ta ce al'ummomi sun ba da rahoton samun ƙaruwar mace-macen ƙananan yara mafi yawa saboda cutar da ake zargi ƙyanda ce.

  8. Sojojin Isra'ila sun kama mutum 15 zuwa 20 a Jenin

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ...

    Sojojin Isra'ila ba su da "nufin" mamaye sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, ko ma su zauna a yankin tsawon lokaci", a cewar wani babban hafsan sojin Isra'ila.

    Jami'in ya ce a halin yanzu sojojin Isra'ila suna cikin sansanin Jenin kuma suna "kai samame ne bisa la'akari da sahihan bayanan da suka samu" ta hanyar amfani da "dabarun faɗa na musamman" don yaƙi a yankuna masu cunkoso da nufin rage yiwuwar ritsawa da fararen hula.

    Jami'in ya ƙara da cewa zuwa yanzu sojojin Isra'ila sun kama mutum 15 zuwa 20 tare da kai hari a kan "'yan ta'adda da makamai da bama-bamai da ababen more rayuwa" a wasu hare-hare ta sama masu yawa.

  9. Jiragen ruwan yaƙin China sun kawo ziyara gaɓar tekun Najeriya

    Chinese destroyer

    Asalin hoton, AFP

    Wani ayarin jiragen sojojin ruwan China bisa jagoranci wani jirgin yaƙin wargaza hare-hare mai suna Nanning ya sauka a Najeriya, a wata ziyara da ba a saba ganin irinta ba daga dakarun sojin China a gaɓar tekun Atalantika cikin nahiyar Afirka.

    Jakadan China a Najeriya ya yaba wa ziyarar ayarin jiragen sojin ruwan ta kwana biyar a matsayin wani muhimmin lamari cikin alaƙar ƙasashen biyu, kuma rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyarta na aiki tare da China don magance barazanar tsaron teku da tabbatar da kwanciyar hankali a Mashigin Tekun Guinea, in ji wata sanarwa daga ofishin jakadancin China.

    China dai ta daɗe tana ƙoƙarin bunƙasa faɗa-a-jinta a Afirka.

    Jirgin wargaza hare-haren da kuma wani jirgin yaƙi mai rakiya da ake kira 'Sanya' tare da wani jirgin dakon kaya, Weishanhu sun isa daf da gaɓar tekun Lagos a cewar wata sanarwa daga sojin ruwan Najeriya.

    Yankin Afirka ta Yamma mai arziƙin man fetur, muhimmin yanki ne da ke fitar da ɗanyen mai a duniya.

    Yankin, musamman ma dai Angola da Najeriya na cikin manyan ƙasashe masu samar da man fetur ga China. Sannan wani babban kamfanin haƙar man fetur na China CNOOC Ltd kuma yana aikin fito da man fetur daga can ƙarƙashin tekun gaɓar Najeriya.

    A watan Janairu ne, Najeriya ta buɗe wata tashar teku mai zurfi ta dala biliyan ɗaya da China ta gina a Legas. Sabuwar tashar jiragen ruwan ta Lekki, na ɗaya daga cikin tashoshin ruwa mafi girma a yankin, kuma kamfanonin China Harbour Engineering Co. mallakar gwamnatin China da Tolaram Group na ƙasar Singapore na da jarin kashi 75% a tashar.

    Akwai raɗe-raɗin cewa ƙasashen yankin Tekun Guinea na iya bai wa sojojin China wuri don kafa sansaninsu.

    A bara, jami'an tsaron Amurka sun bayyana damuwar cewa irin wannan sansani mai yiwuwa a ƙasar Equatorial Guinea na iya barazana ga tsaron Amurka.

    A shekara ta 2017, China ta buɗe sansanin sojojin ruwan ta na farko a wajen ƙasar cikin Djibouti ɗaya daga cikin cibiyoyi mafiu muhimmanci na hada-hadar teku, abin da ya tsananta damuwar cewa hukumomin Beijing na iya kafa ƙarin sansanonin a yankin, daidai lokacin da sojojinta ke daɗa bunƙasa don gudanar da aikace-aikace a wurare masu nisan dubban kilomitoci daga gida.

    • Ko China za ta iya kere Amurka a fagen ƙirƙirarriyar basira ta AI?
    • Ko kun san wane ne shugaban kamfanin TikTok?
  10. Alhazan bogi sun yi wa mahajjatanmu kutse a bana - Jami'an Najeriya

    Hajji

    Asalin hoton, ARAB NEWS

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar alhazai ta Najeriya, NAHCON ta bayyana damuwa a kan kutsen da alhazan bogi suka yi a Mina da Arafa wanda ya janyo rashin isassun tantuna a tsakanin mahajjatan Najeriya.

    Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Mutawif, kamfanin kula da alhazan ƙasashen Afirka da waɗanda ba Larabawa ba, a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

    Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ambato Zikrullah Hassan na cewa “Da farko, zan so na mayar da martani a kan yadda alhazan bogi suka mamaye yankunan aikin Hajjin bana kuma wannan abin kunya ne.

    “Ban san iyakar adadinsu ba, amma mun ga mutanen da ba su da wani aiki a Mina, bayan ‘yan kwanaki sai kuma suka mayar da Mina tamkar kasuwa ko kuma wurin biki.

    “Duk da haka, ba mu da ikon bincikar su. Ba mu ne ke da ikon tsaro ba saboda haka babu yadda za mu iya tunkarar lamarin, gaskiya hakan abin kunya ne.

    Hassan ya ce tantunan da aka yi amfani da su a aikin Hajjin bara wajen tsugunnar da mahajjata 43,000, su ne tantunan da Najeriya ta yi amfani da su ga mahajjata 95,000 yayin aikin hajjin bana.

    “Saboda rashin isassun tantuna, yawancin mahajjata da suka yi burin gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, sun ƙare da samun kansu cikin rana tsawon kwanaki.

    “Mutane da yawa ba su san cewa mafi girman abin da za mu iya yi a matsayinmu na hukumar aikin Hajji shi ne kawai yin korafi ba. Ba mu da wani iko a kan lamarin.

  11. Ɗan Gaddafi, Hannibal yana cikin mawuyacin hali - Rahoto

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Rahotanni sun ce an garzaya da ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Muammar Gaddafi, zuwa asibiti cikin "mummunan yanayi" bayan an ɗauke shi daga gidan yarin Lebanon, inda yake yajin cin abinci.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato tashar talbijin ta Al-Hadath da ke birnin Dubai na cewa sinadarin sukari da ke cikin jinin Hannibal Gaddafi ne ya yi ƙasa.

    Yana dai tsare a gidan yarin Lebanon ne, tsawon sama da shekara takwas.

    Ya fara yajin cin abinci ne a watan jiya domin nuna adawa da tsawaita zamansa da aka yi a gidan yari ba tare da shari’a ba.

    An tsare shi ne a Lebanon tun bayan kama shi a Syria inda ya gudu bayan kashe mahaifinsa da ‘yan tawaye suka yi a shekarar 2011.

    • Tarihin dan Gaddafi da ke takarar shugabancin Libya
    • Me ya sauya bayan shekara 10 da kashe Mu'ammar Gaddafi?
  12. A cikin Hotuna: Faɗan bindiga da hare-hare ta sama a Jenin

    Ana ci gaba da kai farmaki a Jenin, inda aka yi imanin cewa dubban sojojin Isra'ila ne aka tura don ƙaddamar da samamen a brinin da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Ga wasu daga cikin hotunan da ake gani na wannan rikici kawo safiyar yau:

    Jenin

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Da sanyin safiyar Litinin ne sojojin Isra'ila suka fara kai farmakin, wanda da alama yana ɗaya daga cikin mafi girma a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a cikin shekaru da dama.
    Jenin

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Birnin Jenin ya sha fuskantar hare-haren sojin Isra'ila a bara, inda ake alaƙanta Falasdinawa a yankin da kai farmaki masu yawa a kan 'yan Isra'ila.
    Jenin

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Kimanin mutum 14,000 ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar, wanda ya mamaye wani ƙaramin yanki na birnin.
    Jenin

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila sun yi amfani da jirgi maras matuƙi wajen kai hari a wani gida da ke tsakiyar babban sansanin 'yan gudun hijira na Jenin
    Jenin

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Tuni aka ci gaba da amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare ta sama kuma a halin yanzu ana kyautata zaton dubban sojin Isra'ila ne ke aiwatar da wannan samame
  13. An kashe Falasɗinawa takwas, an jikkata hamsin - Jami'ai

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta bayyana cewa, tun bayan ƙaddamar da babban farmakin Isra'ila, sojojin Isra'ila sun kashe mutane takwas.

    An kuma samu mutane 50 da suka jikkata - 10 daga cikinsu sun ji munanan raunuka, kamar yadda rahotanni na baya-bayannan ke cewa.

    • Dakarun Isra'ila sun kai hari cikin Masallacin Kudus
    • Mai mota ya kashe mutum ɗaya da raunata bakwai a rikicin Isra'ila da Falasɗinu
  14. Halin da ake ciki bayan kashe-kashen ƙabilanci a Taraba

  15. Sarkin Zulu ya kwanta jinya bayan cin abincin da ake zargi yana da guba

    Zulu
    Bayanan hoto, ...

    Sarkin Zulu na Afirka ta Kudu, Misuzulu kaZwelithini, ya kwanta jinya a asibiti bayan an yi zargin cewa ya ci abinci mai guba, in ji wani firaministansa.

    Cif Mangosuthu Buthelezi ya ƙara da cewa Sarkin ya nemi tafiya jinya zuwa ƙasar Eswatini saboda hankalinsa ba ya kwanciya wajen neman magani a Afirka ta Kudu.

    Hakan ya zo ne bayan mutuwar daya daga cikin manyan mashawartansa, wanda kuma ake zargin guba ce ta yi ajalinsa, in ji Cif Buthelezi.

    Sai dai mai magana da yawun sarkin ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.

    A halin yanzu sarkin ba ya kwance a asibiti, kuma bai kamata a "haifar da wata fargaba ba", in ji Yariman Africa Zulu.

    An nada Sarki Misuzulu sarauta a gaban dubban mutanensa a watan Oktoban da ya gabata.

    Sai dai ana ci gaba da tafka adawa tsakanin iyalan sarautar bayan hawan mutumin mai shekara 48 kan mulki, kuma a baya-bayan nan rikici ya barke tsakanin sarkin da Cif Buthelezi.

  16. Farmakin Isra'ila: 'Motocinmu cike suke da mutanen da aka raunata'

    Falasɗinu

    Asalin hoton, Reuters

    Wani direban motar ɗaukar marasa lafiya a Falasɗinu ya bayyana yadda tashin hankali ke ƙaruwa a yankin Jenin na Falasɗinu, wanda ya raunata mutane da dama.

    Khaled Alahmad ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa lamarin ya yi "kama da yaƙi", yayin da hare-haren sojan Isra'ila ke sauka kan sansanonin 'yan gudun hijira.

    "Duk lokacin da muka shiga da mota kamar biyar ko bakwai...sai mun fito da su cike da mutanen da aka raunata," a cewarsa.

  17. Alhazan Najeriya 13 sun rasu yayin Aikin Hajjin bana a Kasa mai Tsarki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Alhazan Najeriya da suka mutu a aikin hajjin bana sun kai 13, kuma wasu 41,632 suka kamu da rashin lafiya a kasar Saudiyya.

    Shugaban jami'an likitocin Najeriya mai kula da alhazan ƙasar, Dr Usman Galadima ne ya bayyana hakan a daren Lahadi a birnin Makkah yayin taron bibiyar yadda al'amura ke tafiya bayan Arafat.

    A jawabinsa, Dr Galadima ya bayyana cewa, jimillar mahajjata bakwai ne suka rasu kafin Misha’ir – tafiya daga Mina zuwa Arafat, da komawa Mina – yayin da wasu shida kuma suka rasu a lokacin Misha’ir.

    Ya ba da shawarar a riƙa yi wa maniyyata cikakken gwajin lafiya kafin tafiya aikin Hajji tare da ba da takardar shaidar cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

    Ya ce kamata ya yi a hana tsofaffin alhazai da majinyata marasa lafiya daga zuwa Jamarat (wurin da alhazai ke jifan shaidan).

    Ya kuma buƙaci a riƙa aiwatar da hada-hadar mahajjata kamar yadda hukumomin Saudiyya suka ba da shawara.

    Ya buƙaci jihohin da ke da motocin ɗaukar marasa lafiya su gabatar da su don aiki tare da jami'an likitocin kula da mahajjata na ƙasa don samun ƙarin haɗin kai a kan lamuran da ke buƙatar gaggawa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan hukumar alhazai ta ƙasa mai kula da harkokin sufurin jiragen sama, Goni Sanda na cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa gida, daga ranar Talata 4 ga watan Yuli sannan kuma a kammala ranar 3 ga watan Agusta.

    • Yadda aka damfari masu son zuwa aikin hajji a Najeriya
    • Eid el Kabir 2020: 'Shekara 29 ban yi Sallar Layya a gida ba sai bana'
  18. Jagoran ƴan adawa ya yi kira ga magoya bayansa su fito zanga-zanga a Senegal

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Jagoran 'yan adawa a Senegal, Ousmane Sonko ya buƙaci 'yan kasa su fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zangar adawa da manufar shugaba Macky Sall ta neman takara a karo na uku.

    A yau Litinin ake sa ran shugaba Sall zai gabatar da jawabi domin sanar da anniyarsa ta takara a zaben 2024 ko akasin haka- matakin da akasari kwararu a fannin shari'a ke cewa zai karya ƙundin tsarin mulkin Senegal.

    Mista Sanko ya ce ya shafe tsawon shekaru yana fuskantar barazana a rayuwarsa, saboda kwadayin mulki na mutum guda.

    A watan da ya gabata, Dubban mutane suka fantsama kan tituna su na zanga-zanga a biranen Senegal bayan yanke hukunci shekaru biyu kan Mista Sonko akan ɓata matasa.

    Magoya-bayan Mista Sonko da wasu masu sharhi na ganin wannan hukuncin ƙoƙari ne kawai na datse shi daga takarar shugaban kasa a zaben baɗi.

  19. An kashe Falasɗinawa a wani gagarumin samamen sojojin Isra'ila

    Falasdinawa

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Hukomomin lafiya na Falasdinu sun ce akalla Falasdinawa uku aka kashe tare da jikkata wasu sama da 20 a hare-hare ta sama da dakarun Isra'ila suka ƙaddamar kan sansanin 'yan gudun hijira a yankin jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da ke ƙarƙashin mamaye.

    Wakiliyar BBC ta ambato jami'an tsaron Falasdinawa na cewa Isra'ila ta ƙaddamar da wani gagarumin samame a yankin, inda aka hango jerin gwanon motocin soja na shiga sansanin, ta kowacce kusurwa.

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce jami'ansu na aiki tukuru cikin 'yan sa'o'in da suka wuce, a ƙoƙarin kawar da abin da ya kira "'yan ta'adda" a Jenin.

    Jagoran mayaƙan Hamas, Ismail Haniyeh, ya bayyana harin da aka kai wa sansanin da cewa rashin imani ne kuma babu tausayi.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da war haka

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Litinin domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.