Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton EU kan zaɓen 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Ƙasashen Musulmi na taro a Saudiyya don ɗaukar mataki kan ƙona Al'qur'ani a Sweden

    Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya OIC na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al'qur'ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

    Tattaunawar wadda Saudiyya ta shirya za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin da ƙungiyar ta kira ''abin Allah wadai'' da aka aikata.

    Tuni dai ƙungiyar ta yi aAllah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

    Akasarin ƙasashen musulmi sun gayyaci jakadunsu da ke Sweden domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

  2. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da hutun ƙarshen mako

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a wannan safiya domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.