Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton EU kan zaɓen 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi.

    Mu hadu da ku gobe da safe don kawo muku wasu sababbi.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton EU kan zaɓen 2023

    Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da rahoton Tarayyar Turai (EU) game da sakamakon babban zaɓen 2023 da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban ƙasar.

    Cikin rahoton nata, ƙungiyar ta ce sunan hukumar zaɓen Najeriya INEC ya ɓaci, musamman saboda gazawarta wajen ɗora sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a intanet a lokacin da ta yi alƙawari tun da farko.

    Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta bayyana rahoton a matsayin "maras kan-gado da aka haɗa shi ta hanyar dogaro da abubuwan da suka faru a rumfunan zaɓe ƙasa da 1,000 cikin 176,000 da aka kaɗa ƙuri'a" ranar zaɓen na watan Fabrairu.

    "Babban zaɓe na 2023, musamman na shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya lashe, shi ne mafi inganci da zaman lafiya da aka taɓa yi a Najeriya tun shekarar 1999," in ji Dele Alake, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman.

    Kazalika, ya ce babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da EU ko wata ƙungiyar ƙasar waje ta gabatar da za ta yi fatali da ingancin zaɓen na watan Fabrairu, yana mai cewa sauran ƙungiyoyi kamar na rainon Ingila, Commonwealth, da Ecowas, da NBA sun yabi adalci da yadda aka gudanar da shi.

    Sai dai har yanzu jam'iyyun adawa na PDP da Labour na ci gaba da ƙalubalantar sakamakonsa a gaban kotu.

  3. Kalli wasu daga cikin sabbin rigunan ƙungiyoyin Premier na bana

  4. Yadda wadatar kuɗi ke haifar da tsadar sadaki a Indiya

  5. Nan da sati biyu za mu buɗe asibitin Hasiya Bayero - Abba Gida-Gida

    Gwamnatin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta sake buɗe Asibitin Yara na Hasiya Bayero da ke tsakiyar birnin cikin kwana 14 masu zuwa.

    Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake karɓar baƙuncin Sarkin Gaya Aliyu Ibrahim lokacin da ya kai wa gwamnan gaisuwar Sallah a yau Lahadi.

    "Na yi amfani da damar na faɗa wa sarkin da al'umma cewa za mu sake buɗe Asibitin Yara na Hasiya Bayero nan da mako biyu masu zuwa don amfanin jama'a," in ji shi ckin wani saƙon Twitter.

    An rufe asibitin ne bayan tsohuwar gamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta haɗe shi da asibitin Isiyaka Rabiu da ke kan titin Gidan Zoo, wanda shi ma na yara ne, amma a tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa.

    Sai dai sabuwar gwamnatin NNPP ƙarƙashin Abba na zargin tsohuwar gwamnatin da sayar wa wani ɗan kasuwa da asibitin. Hakan ta sa aka karɓe kuma aka gyara tsohon ginin da zimmar ci gaba da ayyuka a ciki.

    • Yadda rusau ke ƙara jefa mutane cikin fargaba a Kano
    • Abu huɗu da Muhuyi zai binciki gwamnatin Ganduje a kai
  6. Liverpool ta ɗauki Dominik Szoboszlai daga RB Leipzig

  7. Magajin gari ya auri kada a Mexico

    Magajin garin San Pedro Huamelula da ke ƙasar Mexico ya auri kada.

    Victor Hugo Sosa ya auri kadar ce don ɗabbaka tsohuwar al'adar da iyaye da kakanninsa suka shafe shekara 230 suna yi.

    Al'ummar yankin na San Pedro Huamelula sun yi imanin cewa aure tsakanin mutum da kadan zai kawo alkairai kamar damuna mai albarka da kyakkyawan amfanin gona.

    Bikin ya gudana a ranar Juma'a a gaban mutane.

  8. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu 02/07/23

  9. Dole ne mu ɗauki matakin bai-ɗaya don kare Ƙur'ani - Ƙasashen Musulmi

    Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta nemi a ɗauki matakin kauce wa sake ƙona Ƙur'ani, 'yan kwanaki bayan wani ya ƙona kwafin littafin mai tsarki a Sweden.

    Ƙungiyar mai mamba 57 ta gana a birnin Jeddah na Saudiyya don lalubo martanin da za su mayar kan ƙona Ƙur'anin da Salwan Momika, ɗan asalin Iraƙi mai shekara 37, ya yi bayan ya tattaka shi a ƙofar wani masallaci a birnin Stockholm.

    'Yan sanda ne suka ba shi kariya kafin ya aiwatar da aniyar tasa, wanda ya ce ya yi hakan ne don ya nuna 'yancinsa na faɗar albarkacin baki.

    A yau Lahadi, Organization of Islamic Countries (OIC) ta shawarci ƙasashe mambobinta "su ɗauki matakin bai-ɗaya don guje wa afkuwar wulaƙanta Ƙur'ani", kamar yadda wata sanarwa da suka fitar bayan taron ta bayyana.

    "Dole ne mu ci gaba da tunasar da ƙasashen duniya game da aiwatar da dokokin ƙasa da ƙasa da gaggawa, waɗanda suka haramta nuna duk wata ƙiyayya ga addinai."

    Lamarin ya jawo zanga-zanga a faɗin duniya, inda ƙasashen Musulmi kamar Daular Larabawa da Moroko da Kuwait da Iraƙi suka kira jakadan Sweden don nuna ɓacin ransu.

  10. Ina makomar David de Gea a Manchester United ?

  11. Tinubu ya kama hanyar komawa Abuja

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kama hanyar zuwa Birnin Tarayya Abuja don ci gaba da harkokin mulki bayan shafe kwana biyar na hutun Babbar Sallah.

    Kafin ya bar filin jirgin sama na Murtala Muhammad, Tinubu ya kalli faretin girmamawa da dakarun sojan Najeriya suka shirya masa.

    Ya isa filin jirgi bisa rakiyar Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu.

    Yayin hutun Sallar, shugaban ya je gaisuwar sallah wajen sarakunan gargajiya na Ijebu, da Egba, da Eko a jihar Ogun da kuma Legas.

    Kazalika, Shugaban Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ziyarce shi ranar Asabar.

  12. Macron zai gana da jami'an gwamnatinsa don magance zanga-zanga

    Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron zai gana da manyan jami'an gwamnatinsa da maraicen yau Lahadi domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen zanga-zangar da ke gudana a faɗin ƙasar.

    A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce Mista Macron zai gana da firaminista Elisabeth Borne, da ministan cikin gida Gérald Darmanin da ministan shari'a Eric Dupond-Moretti domin tattauna batun.

    An dai shafe kwanaki aƙalla huɗu ana gudanar da zanga-zanaga a faɗin ƙasar bayan da wani ɗan sanda ya harbe wani matashi mai shekara 17 a birnin Paris.

    Inda aka yi ta ƙona shaguna da motoci da makarantu da lalata gine-ginen gwamnati.

    Kakar matashin ta yi kira da a kwantar da hankula kan rikicin da ya ɓarke bayan kashe jikanta nata.

    "Ba ma son su lalata shagunan mutane, ko motoci da makarantu" kamar yadda Nadia ta shaida wa gidan talbijin na BFM.

    Kakar yaron ta koka kan yadda ta ce masu zanga-zangar ke “fakewa da batun Nahel, dan haka muna son a kwantar da hankula”.

  13. 'Yan bindiga sun kashe Fasto tare da yin garkuwa da masu ibada a coci

    Wasu 'yan bindiga sun afka Cocin 'Redeemed Christian Church of God' da ke jihar ogun da ke kudu maso yammacin ƙasar, lokacin da ake tsaka da ibada, inda suka kashe Fasto tare da yin garkuwa da masu ibada bakwai.

    Jaridun ƙasar sun ambato kwamandan rundunar tsaron sa kai ta 'So-Safe Corps' Soji Ganzallo ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Lahadi da safe.

    Ya ce dakarunsa sun samu nasarar kuɓutar da mutum bakwai tare da kashe mutum guda daga cikin maharan.

    Cikin wata sanarwa da rundunar tsaron ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalain ƙarfe 12 na rana.

    Inda suka afka wa Coci tare da yin garkuwa da mutum bakwai bayan sun kashe Faston.

    Sanarwar ta ce an umarci jami'an tsaron sa kan na 'So-Safe Corps' da su kuɓutar da mutanen ba tare da raunata su ba, daga nan ne kuma jami'an suka bi sawunsu, inda suka samu nasarar kubutar da mutanen tare da kashe ɗan bindiga guda.

    Mista Ganzallo ya ce jami'an rundunarsa tare da haɗin gwiwar 'yan sanda sun ƙaddamar da farautar sauran maharan da suka tsere domin kamo su.

  14. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

  15. Shugaban Senegal zai fayyace matsayinsa kan takarar shugabancin kasar a karo na uku

    A gobe Litinin ne shugaban ƙasar Senegal Macky Sall zai fayyace matsayinsa kan sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku a zaɓen 2024.

    Shugaba Sall ya bayana haka ne a lokacin wata ganawa da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin ƙasar waɗanda ke mara masa baya domin sake tsayawa takarar.

    Shugaban zai fayyace matsayin nasa ne cikin wani jawabi da zai gabatar wa ƙasar ranar Litinin 3 ga watan Yuli.

    Shugabannin ƙananna hukumomi 472 ne daga cikin 558 ke goyon bayan takarar tasa a zaɓen 2024 da ke tafe, da ake ganin za ta ƙara haifar da rikici a ƙasar.

    Shugaba Macky Sall ya yi kiran neman haɗin kai a gaban magoya bayansa, sannan ya ce zai fayyace matsayinsa dangane da sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen da za a yi cikin watan Fabrairun 2024.

    A ƙarshen watan Mayu ne Mista Sall ya ƙaddamar da taron tuntuɓa na ƙasa da aka shafe mako uku da rabi ana gudanarwa, wani abu da 'yan adawa suka ƙaurace wa, inda suka buƙace shi da ya yi watsi da aniyarsa ta sake tsayawa takara a karo na uku.

    Magoya bayan shugaban na kallonsa a matsayin ɗan takararsu a zaɓen 2024.

    Babban abokin hamayyarsa Ousmane Sonko, wanda ke samun goyon bayan matasa da talakawa, ba zai tsaya takarar ba, bayan da aka same shi da laifin ɓata wa wani minista suna tare da ɓata tarbiyyar matasa.

    Matakin da ya ce haɗin baki ne domin abin da ya kira 'kawar da shi a siyasance'.

  16. Garin da ba a yunwa a Indiya

  17. Saudiyya ta tsare sama da mutum 17,000 da suka yi yunƙurin hajji ba tare da izini ba

    Hukumomin Saudiya sun kama tare da tsare mutum 17,615 da suka yi yunƙiurin yin aikin hajjin ba tare da izini ba.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ambato sShugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin bana Lt. Gen. Muhammad Al Bassami na bayyana haka, yama mai cewa 9,509 daga cikinsu mutane ne da suka saɓa ka'idar bizar aiki da ta zaman ƙasar.

    Ya ce an kama mutum 33 da ake zargi da jagorantar mutanen ba tare da izinin hukumomin kasar ba.

    Al-Bassami ya ce hukumomin ƙasar kuma sun tisa ƙeyar mutum 202,999 da suka yi yunƙurin shiga ƙasar don gudanar da aikin hajjin ba tare da izini ba.

    Shugaban kwamitin tsaro na aikin hajjin ya kuma yaba wa askarwan ƙasar bisa jajircewa da ya ce sun yi a lokacin gudanar da wanna gagarumin aiki cikin ƙwarewar aiki da basira.

    Dokokin Saudiyya sun tanadi cewa duk mutumin da ke zaune a ƙasar, dole ne ya nemi izinin hukumomi idan yana son gudanar da aikin hajji.

  18. Isra'ila ta kai hari ta sama kusa da birnin Homs a Syria

    Rahotonni sun ce Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a kusa da birnin Homs, wanda ke hannun gwamnatin Siriya.

    Kafofin yaɗa labaran Syria sun ce makaman da aka harbo ta sama sun ratso ta sararin samaniyar ƙasar Lebanon sannan suka sauka a kusa da birnin na Homs tare da haddasa ɓarna.

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai harin,tana mai cewa ramuwar gayya ce kan harin makamin harbo jirgin sama da aka harba cikin ƙasar daga Siriyar.

    A 'yan watannin baya-bayan nan isra'ila na zafafa kai hare-hare zuwa sansanonin sojin saman Siriya.

    Isra'ila ta ce tana kai hare-haren ne da nufin hana Iran shigar da makamai zuwa makwabtanta Siriya da Lebanon.

  19. Bambancin da ke tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa a Najeriya

    Shin kun san bambancin da ke tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa a Najeriya? wannan ce tambayar da Isah Zakari ya aiko wa BBC Hausa a cikin shirinmu na Amsoshin Takardunku na wannan makon, wanda Badamasi Abdulƙadir Muktar ya gabatar,

    Barista Mainasara Kogo babban lauya ne a Najeriya ya kuma ce majalisar dattawa majalisa ce da ta ƙunshi wakilai daga mazaɓu 109, inda kowacce jiha ke da 'yan majalisar dattawa uku, yayin da babban birnin tarayyar ƙasar Abuja ke da ɗan majalisar dattawa guda ɗaya.

    A ɓangare guda kuma a majalisar wakilai ana amfani da girman ƙasa da yawan jama'ar wajen fitar da gundumomin 'yan majalisar, kamar yadda Barista Kogo ya bayyana.

    ''Wannan ne ma ya sa wani lokaci za ka ga an haɗa kananan hukumomi guda biyu, ko uku a matsayin gundumar dan majalisa ɗaya, wani lokaci kuma ƙaramar hukuma ɗaya ma za ta samu wakili guda, kasancewar tana da yawan jama'ar da ta kai samun matsayin gundumar ɗan majalisar wakilan'', in ji Lauya Kogo.

    Sannan wani bambancin shi ne na shekarun 'yan majalisar, kamar yadda barista Kogo ya bayyana.

    Ya ce ɗan majalisar dattawa kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce sai wanda ya kai shekara 35 zuwa sama ne zai zama Sanata, amma a majalisar wakilai daga 25 ne zuwa sama.

    Dangane da hurumin aiki kuwa Barista Kogo ya ce duka majalisun biyu aikinsu kusan irin ɗaya ne, musamman ta fuskar yin dokoki da amincewa da kasafin kudi.

    Babban abin da ya haɗa su shi ne yin dokoki, domin kuwa abu ba zai zama doka ba, dole sai duka majalisun biyu sun amince da shi, kamar yadda Barista Kogo ya bayyana.

    Ya ƙara da cewa duk abin da majalisar wakilai za ta yi, to da dattawa ma za ta yi shi, amma kuma majalisar wakilai ba za ta iya duk aikin da majalisar dattawan ke yi ba.

    ''Alal misali majalisar dattawa ce kaɗai ke tantance ministoci da sauran naɗe-naɗen da shugaban kasar zai yi, sannan ita ke amincewa da naɗin manyan hafsoshin tsaro, da jakadun ƙasashen waje'', kamar yadda Lauyan ya bayyana

    ''Manyan hukumomin irin su EFCC da sauran hukomomi dole sai majalisar dattawa ta tantance, sannan ta amince da waɗanda shugaban ƙasar zai naɗa a matsayin shugabanninsu, amma ba majalisar wakilai ba'', in ji Barista Kogo.

  20. An zargi Shell da cinikin gas da Rasha bayan sanar da ficewarsa daga ƙasar

    Wata kungiyar kare muhalli ta Birtaniya ta zargi kamfanin mai na Shell da ci gaba da cinikin gas da Rasha sama da shekara guda bayan sanar da ficewarta daga ƙasar.

    Kungiyar mai suna Global Witness ta ce bincikenta ya gano yadda kamfanin Shell ya riƙa taimaka wa Rasha wajen fitar da gas ta teku a shekarar da ta gabata, sannan har yanzu suna sayen tankoki maƙare da gas.

    Wani mashawarcin shugaban ƙasar Ukraine ya yi zargin cewa wannan kasuwanci shi ke taimaka wa Rasha da kuɗaɗen yaki, inda ya nemi kamfanin na Shell da ya yi amfani da kuɗaɗen da ya samu ta wannan hanya wajen sake gina Ukraine.

    To sai dai kamfanin na Shell ya ce sayen man da ya yi daga Rasha tsohon kwantiragi ne da suka cimma tun kafin wannan lokaci, wanda kuma ba zai yiwu su karya yarjejeniyarsu ba.