Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mun yi imani lokaci ya zo da Najeriya za ta samu zaman lafiya - Ribadu

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Direbobin tankokin dakon mai za su fara yajin aiki a Ghana

    Kungiyar direbobin tankokin dakon man fetur a Ghana ta ce za ta fara yajin aiki a yau Litinin saboda rashin kyawun hanyoyi.

    Direbobin na so ne gwamnati ta gyara hanyoyi a yankunan Tema, Takoradi da Buipe.

    Sun nuna damuwa kan hadurran da ke tattare da safarar man fetur a kan hanyoyin marasa kyau.

    Kungiyar yan kasuwa ta Liquified Petroleum Gas Marketers Association ta yi gargadin cewa za a iya samun karancin man LPG a kasar idan har aka shiga yajin aikin.

  2. Alhazan Najeriya shidda sun rasu sakamakon bugun zuciya a Saudiyya

    Alhazan Najeriya shida sun rasu a Saudiyya, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin bugun zuciya.

    Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajji, Dr Usman Galadima ya tabbatar wa BBC da hakan a cikin wata tattaunawa.

    Galadima ya ce mahajjatan da suka rasu sun hada da biyu daga jihar Osun, daya kuma daga Kaduna da Filato.

    Ya ce ya zuwa yanzu maniyyata 15,860 suka yi jinya sanadiyyar cutuka daban-daban, wadanda suka hada da mura da gyambon ciki da hawan jini da kuma cizon sauro.

    Ya kara da cewa sama da wasu mahajjata 100 an tura su asibitoci a kasar Saudiyya.

    Ya kara da cewa wasu alhazan Najeriya 30 da aka tabbatar da cewa suna da matsalar tabin hankali an kai su asibitocin Saudiyya kuma za su yi aikin hajji saboda “yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.”

  3. Ƴansanda sun 'buɗe wuta' kan ofishin jam'iyyar adawa a Saliyo

    Dan takarar shugabanci kasa a babbar jam'iyyar hamayya ta Saliyo ya zargi sojoji na harbi a hedikwatar jam'iyyarsa.

    Samura Kamara na jam'iyyar APC ya ce harbin da aka aikata a birnin Freetown kokari ne na aikata kisa.

    Akwai mutum guda da ya samu mumunan rauni.

    Ana dai cikin yanayi na fargaba yayinda ake dakon sakamakon zaben Saliyo na ranar Asabar.

    'Yansanda sun ce hayaki mai sa hawaye suka harba domin tarwatsa dandazon mutanen da suka taru a wajen ofishin jam'iyyar adawar.

    Bangarorin hamayya da shugaba Julius Maada Bio dukka na ikirarin kasancewa a gaba wajen lashe zaben. Kasashen duniya da ke sa ido kan zaben sun roki a kwantar da hankula yayin da ake cigaba da kirga kuri'u.

  4. Assalamu alaikum

    Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku biyo ni Aisha Babangida a wannan rana ta Litinin don sanin halin da duniya ke ciki.

    Sai Ku kasance da mu.