Mun yi imani lokaci ya zo da Najeriya za ta samu zaman lafiya - Ribadu

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Ba dole ne sai ɗalibai mata sun sa siket ba - Kotun Ƙolin Amurka

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa wata makarantar North Carolina ba za ta bukaci dalibanta mata su sanya siket ba.

    Wata kotun tarayya da ke Amurka ta gano a shekarar da ta gabata cewa makarantar ta take hakkin dalibanta mata da tsarin mulkin kasar ya ba su tare da ka’idojinta inda suka jiɓanci yanayin kayan. makaranta.

    Makarantar Charter Day da ke birnin Leland, ta daukaka kara kan hukuncin har zuwa babbar kotun kasar.

    Alkalan sun ki amincewa s saurari karan ba tare da sun yi wata ƙarin bayani ba..

    Tuni dai an sauya yanayin kayan makarantar inda aka bai wa mata damar sanya wando.

    A cewar takardun kotu, Baker Mitchell, wanda ya kafa makarantar, ya ce an yi amfani da siket ɗin ne don ci gaba da tabbara ta ''mazantaka'', yana mai bayyana kalmar a matsayin "ka'idar ɗabi'a inda ake ɗaukar mata a matsayin mutane masu rauni wanda ya kamata maza su kula da su tare da mutunta su''

    Sai dai wasu gungun iyayen sun kalubalanci manufar, inda suka ce ta jefa ‘ya’yansu mata cikin nakasu idan aka kwatanta da takwarorinsu maza.

    Da take rubuta ra'ayi mafi rinjaye, babbar alkalin kotun Barbara Milano Keenan ta ce tsarin kayan makarantar na iya sai yara mata cikin wani hali ta hanyar gaskanta wadansu abubuwan da ba haka su ke ba, kuma hakan na "iya haifar da mummunan sakamako ga 'yan mata."

  2. Ƴan sanda sun tarwatsa gungun masu lalata layin dogo

    ...

    Asalin hoton, Nigeria poilice

    Rundunar 'yan anda jihar Kaduna ta bayyan cewa ta bankado wani gugun bata gari da ke lalata layin dogo a yankin Sanzwan da ke garin Zonkwa a karamar hukumar Zango Kataf.

    A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'in hulda d jama'a na rundunar DSP Mohammed jalige, rundunar ta ce bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a ranar 22 ga watan Yuni, 2023 da misalin karfe goma da rabi na dare, sun yi nasarar fatattakar gungun barayin tare da kama motar da suka zo da ita wacce ke shake da karafunan layin dogo..

    Sanarwan ta ƙara da cewa duk da ba a kama waɗanda ake zargin ba rundunar na cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yaba wa jami’an da suka dakatar da ayyukan ’yan fashin yayin da ya bukaci jama’a da su cigaba da samar da sahihan bayanai a kan lokaci don taimakawa 'yan sanda wurin gudanar da ayyukansu.

    ....

    Asalin hoton, Nigeria poilice

    ...

    Asalin hoton, Nigeria poilice

  3. Najeriya ta ba da hutun idin Babbar Sallah.

    ...

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Laraba 28 da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan babbar Sallah na shekarar 2023.

    Bukin sallar Eid Kabir bukin ne da al'ummar musulmi a fadin duniya ke gudanarwa kowace shekara.

    Bukin na da mahimmanci a addinance kuma musulmai daga birane na kokarin komawa gida domin gudanar da bukuwan sallar tare da ƴan uwa da abokan arziki.

    Ana yanka rauguna kamar yadda addinin musulunci ya tanada tare da kuma taruwa a filin idi domin gabatar da sallah da safe.

  4. An kama wani ɗan sanda bisa zargin yunƙurin kashe abokin aikinsa

    ...

    Rundunar 'yan sandar jihar kaduna ta bayayna cewa an damke wani ɗan sanda mai suna Sufeto Moses Paul bisa zargin ƙoƙarin kashe abokin aikinsa sufeto Simnawa Paul har lahira a ranar 16 ga watan junin shekaran nan..

    A wata sanarwa da da ta fito daga ofishin mai magana da yawun rundunar DSP Mohammed Jalige, rudunar ta ce lamarin da ya faru a lokacin da 'yan sandan ke bakin aiki a sansanin 'yan sanda da ke kafanchan inda Sufeto Moses Paul ya shake abokin aikinsa da igiya.

    Ta ƙara da cewa, wasu jami’an ‘yan sanda da ke kusa ne suka ceto sufeto Simnawa bayan kukansa ya jawo hankalinsu.

    Binciken da aka riga aka gudanar ya nuna cewa Moses Paul ya yi yunkurin kwace bindigar abokin aikin nasa ne, amma har yanzu ana kan gudanar da cikakken bincike kafin a kai ga hukunta wanda ake zargin.

  5. Prigozhin ya ce bai yi tattaki don hambarar da shugabancin Rasha ba

    ...
    Bayanan hoto, Shugaban Dakarun Wagner, Yevgeny Prigozhin

    Shugaban dakarun Wagner Yevgeny Prigozhin ya bayyana cewa bai kai wa Putin hari ba a lokacin da ya ayyana dakarunsa za su yi tattaki zuwa Moscow, yana mai cewa: “Ba mu yi tattaki don hambarar da shugabancin Rasha ba.

    A cikin sakonsa na bidiyo na mintuna 11, ya ce: "Manufar tafiyar ita ce kauce wa lalata Wagner da kuma yin la'akari da jami'an da ta hanyar ayyukansu na rashin da'a sun tafka kurakurai masu yawa".

    Ya ce Wagner ya yi nadaman "kawo cikas a harkokin jirgen sama na Rasha" kuma sun juya ne "don gujewa zubar da jinin sojojin Rasha."

  6. Mun yi imani lokaci ya zo da Najeriya za ta samu zaman lafiya - Ribadu

    ...

    Asalin hoton, Nuhu Ribadu/Twitter

    Mallam Nuhu Ribadu, mataimakin babban sufeton 'yan sanda (mai ritaya) a hukumance ya karɓi aikin Mashawarcin Tsaron Ƙasa a Najeriya daga Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

    Yayin wata ganawa ranar Litinin a Abuja, Ribadu bayan kama aiki, ya yi alƙawarin zage damtse don cika burin da 'yan Najeriya ke da shi da kuma tabbatar da tsaron ƙasar daga duk wani nau'in rashin tsaro kama daga ayyukan ta'addanci da 'yan fashin daji da satar mutane don neman kuɗin fansa da sauransu.

    “Za mu daidaita al'amuran ƙasar nan, za mu tabbatar da tsare ƙasar nan kuma mu tabbatar da zaman lafiya a Najeriya saboda mun yi imani lokaci ya zo da ƙasar nan za ta ci moriyar zaman lafiya da dawo da kwanciyar hankali da zaman doka kamar dai kowacce ƙasa a duniya,” Ribadu ya ce a cikin jawabinsa.

    “Tsaron ƙasa, al'amari ne da ake ci gaba da ginawa. Za mu yi nazari a kan ƙoƙarin da aka rigaya aka yi kuma mu ɗora a kai.

    “Shugaban ƙasa ya ɗauki babban nauyi na tabbatar da tsaron duk wani taku na ƙasar mu. Za mu yi aiki da duk wani mai ruwa da tsaki don tabbatar da ganin an cika wannan buri.

    “Wannan gagarumin aiki na tabbatar da tsaron ƙasarmu, nauyi ne a kan duk ɗan Najeriya da ma dukkan abokan ƙawancen Najeriya,” ya faɗa a cikin wata sanarwa daga ofishin Mashawarcin tsaron ƙasar.

    ...

    Asalin hoton, Nuhu Ribadu/Twitter

    Tun da farko an naɗa Ribadu, wanda shi ne shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na farko a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin tsaro.

    Sai dai bayan 'yan kwanaki, sai Shugaba Bola Tinubu ya yi wa dukkan manyan hafsoshin tsaron ƙasar murabus tare da naɗa wasu a gurabensu ciki har da Mallam Nuhu Ribadu wanda aka ɗaga darajarsa zuwa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro

    ...

    Asalin hoton, Nuhu Ribadu/Twitter

  7. Bio na kan gaba a zaben shugaban kasan Saliyo

    ...
    Bayanan hoto, Shugaban saliyo, Julius Maada Bio.

    Sakamakon kuri'un zaben shugaban kasar Saliyo da aka fara kirgawa - wanda ke da kuri'u daga kashi 60% na rumfunan zabe - ya nuna cewa Julius Maada Bio ne ke kan gaba.

    Hukumar zaben kasar ta ce yana da kashi 56% na kuri’un da aka kada inda abokin hamayyarsa Samura Kamara na jam’iyyar All Peoples Congress (APC) ya samu kashi 42%.

    Dan takara na bukatar sama da kashi 55% na kuri’un da aka kada, kafin a tabbatar da nasaransa a zagayen farko.

    A baya dai APC ta yi korafi kan yadda hukumar zaben kasara ta gundanar da zaben.

    Zaben na ranar Asabar ya gudana cikin yanyi na fargaba sakamakon tarzonmar da aka yi ta samu a lokacin yakin neman zabe.

  8. Ma'aikatan Binuwai na murnar samun albashi karon farko cikin wata bakwai

    ...
    Bayanan hoto, Gwamnan Jihar Binuwai, Rev. Fr. Hyacinth Alia

    Ma’aikata a jihar Benue sun nuna matuƙar farin ciki bayan sun karbi albashin wata daya daga gwamnatin jihar.

    Jaridar Daily Trust ta rawaito wasu ma’aikatan gwamnati a Makurdi, babban birnin jihar, na cewa albashin ya fara shiga asusun ajiyarsu ne tun ranar Lahadi bayan sun kwashe wata takwas ba tare da an biya su ba.

    Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta kasa reshen jihar Binuwai, Terungwa Igbe, ya tabbatar da cewa an biya ma’aikatan gwamnati albashin wata daya.

    Amma a halin da ake ciki wasu rukunin ma'aikata da suka haɗar da malaman makaranta da ’yan fansho sun ce har yanzu ba su ga albashinsu ba.

    Mafi yawan malaman da aka zanta da su, sun bayyana cewa su ma, suna sa ran cewa za a biya su nan ba da jimawa ba.

  9. Wata ƴar jaririya ta mutu bayan mota ya buge ta a wani asibiti

    ...

    Asalin hoton, FAMILY PHOTO

    Wata jaririya ƴar wata takwas ta rasu kwanaki hudu bayan da wani mota ya buge ta a wani asibiti.

    An dauke Mabli Cariad Hall ta jirgin sama daga Asibitin Withybush da ke Pembrokeshire zuwa Cardiff bayan da aka buge shi tare da wani mai tafiya a kasa, ranar Laraba.

    Direban motar ƙirar BMW fara da hatsarin ya rutsa da shi ya samu raunuka marasa lahani kuma yana kwance a asibiti.

    Mabli ta kasance "kyakkyawa, mai murmushi da kasancewa mai farin ciki", wani abokin dangi ya fada cikin karramawa.

    An kai ta asibitin yara na Bristol Royal amma ta mutu sakamakon raunukan da ta samu ranar Lahadi.

    Tuni dai aka sallami fasinjan da ke cikin motar BMW da sauran mai tafiya a kasa da suka yi hatsarin daga asibiti.

    Abokin dangi Sinéad Morris ya fada a shafukan sada zumunta cewa "cikin takaici, dole ne na sanar da Mabli ta sami "rauni mai tsanani da ba za a iya jurewa ba".

    "Duk da tsawon kwanakin karfin halin da Mabli ta yi, ta mutu cikin lumana a hannun Gwen da Rob a farkon ranar Lahadi, 25 ga Yuni, 2023."

    Ms Morris ta ƙara da cewa dangin suna son "bayyana matukar godiyarsu ga kwazon kwararrun likitoci da suke da hannu ajen kulawa da Mabli".

    Wata gidauniyar tara kuɗi ta tara ma dangin Mabil £20,000.

  10. Mayakan Wagner za su ci gaba da zama a Mali da CAR - Lavrov

    Wagner

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi magana game da makomar mayakan Wagner da ke aiki a Afirka.

    Abin da aka fi maida hankali a kai tun bayan tashin hankalin da aka yi a karshen mako da ya shafi Wagner da shugabansa Yevgeny Prigozhin ya kasance kan Rasha da Ukraine.

    Sai dai sojojin hayan na da hannu a kasashen Afirka da dama - ciki har da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Mali, inda ake zarginsu da aikata ta'asa da laifukan yaki.

    An yi tambayoyi da dama kan makomar wadancan turawan na Afirka, wadanda mutane da yawa ke ganin suna wakiltar Rasha ba bisa ka'ida ba.

    Amma da yake magana a tashar gwamnati ta RT , Mista Lavrov ya ce za a ci gaba da gudanar da ayyukan Wagner, in ji kamfanin dillancin labaran AFP.

    Dakarun Wagner "suna aiki ne a matsayin masu ba da horo. Wannan aikin, ba shakka, zai ci gaba,'' n ji ministan.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa, tawayen da aka soke ba zai sauya alakar Rasha da "abokan hadin gwiwa da abokai ba."

  11. Sudan ta Kudu ta karɓi 'yan gudun hijira 10,000 da suka tsere daga Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Sama da mutane 10,000 ne suka yi rajistar zama ‘yan gudun hijira a Sudan ta Kudu bayan da suka tsere daga rikicin Sudan, in ji ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD Ocha.

    Yayin da baki daya, mutane 130,000 suka tsere zuwa Sudan ta Kudu tun bayan barkewar fadan a watan Afrilu, yawancinsu 'yan Sudan ta Kudu ne da ke komawa gida.

    Ocha ya ce ‘yan gudun hijira na baya-bayan nan na ci gaba da tabarbarewar al’amura yayin da ake hasashen adadinsu zai ci gaba da karuwa yayin da ake ci gaba da gwabza fada.

    Ocha ya kara da cewa daga cikin wadanda suka isa wurin sun haɗa da yaran da suka rabu da ƴan uwan su, tsofaffi, nakasassu, masu buƙatar jinya na gaggawa, mata da sune masu riƙe gida da kuma mata masu juna biyu.

    Yawancin baƙin da suka iso sun hadu da tashe-tashen hankula da cin zarafi kamar kwace da wawure dukiyar kasa, ciki har da lokacin da suke tafiya Sudan ta Kudu.

    Idan aka yi la'akari da sauran makwabtan Sudan, Masar - mai 255,000 - da Chadi - mai 120,000 - sun dauki mafi yawan 'yan gudun hijirar da ke tserewa daga tashin hankali.

  12. Alhazan Jamhuriyar Nijar sun koka kan rashin isasshen wurin kwana a Mina

    Nijar

    Wasu alhazai daga jamhuriyar Nijar sun koka kan rashin isasshen wurin kwana tun da suka isa Saudiyya.

    Duban alhazai ne na ƙasashe daban-daban ke zama a tsakiyar rana kan titunan Mina ba su samu shema ba.

    Matsalar dai kamar yadda hukumomin Saudiya suka bayyana ta samo asali ne daga yawan jama'ar da suka je aikin hajjin na bana.

    Alhazan Jamhuriyar Nijar sama da 1,500 ne ba su samu shemomin ba.

    Nijar
    Nijar

    Wasu daga cikin Alhazan Jamhuriyar Nijar sun ce suna fatan Hukumomi su dubi wannan al'amari kuma su gyara shi saboda ama'a suna cikin matsala.

  13. Ƙarin Haraji a Kenya 'kuskure ne' - Ƴan adawa

    Kenya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    'Yan adawar Kenya sun bayyana ƙarin harajin da shugaban ƙasar William Ruto ya sanya wa hannu a matsayin "kuskure", in ji kamfanin dillancin labaran AFP.

    Tuni ta gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a bana kuma tana barazanar sake yin zanga-zangar.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa madugun 'yan adawa Raila Odinga yana cewa

    "Matsayinmu ya kasance cewa kudirin dokar kuskure ne kuma gwaji ne da 'yan Kenya ba za su iya ba."

    "Mun yi fatan cewa Ruto zai yi kira a sake duba ta kafin sanya hannu."

    Daga cikin sauye-sauyen da majalisar ta amince da shi a makon jiya, akwai rubanya harajin sayar da man fetur daga kashi 8% zuwa 16%, da kuma sabon harajin gidaje.

    Sabbin matakan dai sun harzuka wasu magoya bayan shugaban, inda a lokacin yakin neman zabensa da ya yi nasara, ya bayyana kansa a matsayin wanda zai sanya ido kan buƙatun talakawa.

  14. 'Abin da ya sa na tuba da shan miyagun ƙwayoyi'

  15. Amnesty ta yi Allah-wadai da kisan wanda aka yi wa zargin saɓo a Sokoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tabbatar an gurfanar da wadanda suka kashe wani mutum a jihar Sokoto bisa zargin kalaman ɓatanci, a gaban kuliya.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta yi Allah-wadai da kisan, ta kuma buƙaci gwamnati da ta binciki lamarin wanda ta bayyana a matsayin ‘mai ban tsoro’.

    A cewar sanarwar, “Ƙaruwar kashe-kashen batanci na buƙatar ganin hukumomi su tashi tsaye wajen tabbatar da doka da mutunta haƙƙoƙin bil’adama, wadanda suka hada da ‘yancin yin addini, ra’ayi da fadin albarkacin baki.”

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito cewa Ahmad Rufa'i mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Sakwato ya ce, a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni ne wasu fusatattun matasa suka kashe mutumin mai suna Usman Buda, bisa zargin sa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu.

    ASP Ahmad Rufa’i, ya ƙara da cewa da isar su waɗanda suka ƙona shi suka tsere daga wurin tgare da barin mutumin, inda ya rasu bayan an kai shi a asibiti.

    A martanin da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya mayar, "ya yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankulansu da bin doka da oda a kowane lokaci."

  16. An fara aikin hajji gadan-gadan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau Litinin ce ranar farko da Musulmai da ke aikin hajji suka fara aiwatar da manyan rukunan ibadar, wadda ɗaya ce daga shikashikan Musulunci, bayan da suka isa Mina da sanyin asubahi.

    Mahajjatan za su kwana a Mina, kafin su kama hanya zuwa filin Arafa bayan sallar Asubahi a ranar Talata.

    A ranar Laraba kuma, mahajjata za su gudanara da jifar Jamra, da yanka dabbobin hadaya, da kuma ɗawafi kafin daga baya su koma Mina inda za su kwashe kwana uku.

    Mina dai wani yanki ne da ke tsakanin birnin Makkah da kuma Muzdalifa.

    Sama da mutum miliyan 1.6 ne suka isa Saudiyya daga ƙasashe 160 domin gudanar da aikin hajjin na bana, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

  17. Ana caccakar Obama a Indiya kan kalamansa na kare haƙƙin Musulmai

  18. Ɗalibin da ya tafi aikin Hajji a ƙafa daga Pakistan

    Hajj

    Asalin hoton, Reuters

    Wani matashi mai suna Osman Arshaas ɗan ƙasar Pakistan ya yi tafiyar kilomita 4000 domin gudanar da aikin Hajjin bana.

    Ya tafi Makka da ƙafa, ya bar Pakistan, ya wuce Iran zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa kafin ya isa Saudiyya.

    Tafiyar ba ta zo da sauƙi ba ga Arshad, ya fuskanci ƙalubale da dama musamman ta fuskar yanayi.

    "Kowane musulmi yana da burin zuwa Makka wata rana, domin ziyartar dakin Ka'aba," in ji Osman.

    Ya kara da cewa, “A lokacin tafiyata, na kan kwana a duk wani masallaci ko otal da na gani, amma yawanci ina kwana a kan tanti".

  19. Bangarori biyu na ikirarin samun nasara a zaben Saliyo

    Saliyo
    Bayanan hoto, Masu kada kuri'a sun kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da na kananan hukumomi a ranar Asabar

    Ana ci gaba da kidaya kuri'u a sakamakon zaben shugaban kasar Saliyo kwanaki biyu bayan kammala zaben.

    Ba a dai bayyana wanda ke kan gaba a zaben shugaban ƙasa tsakanin shugaba mai ci Julius Maada Bio da babban abokin hamayyarsa Samura Kamara, amma tuni bangarorin biyu suka ce sun lashe zaben.

    Masu sa ido kan zaben dai sun buƙaci jama'a su kwantar da hankalinsu su jira sakamakon zaɓe a hukumance.

    Sai dai akwai fargabar cewa ba za a bayyana sakamako ba cikin hanzara.

    Tawagar Tarayyar Turai ta bukaci hukumar zaben da ta samar da “ta yi gaskiya wajen tattara sakamakon” don kwantar da hankali.

    Dole ne wanda ya yi nasara a zaben ya samu kashi 55 cikin 100 na kuri’un da aka kada, in ba haka za a je zagaye na biyu a zaben.

  20. Matar da mijinta ya mutu a hatsarin jirgin karkashin teku 'ta tsallake rijiya da baya'

    Christine Dawood
    Bayanan hoto, Christine Dawood

    Matar da mijinta da kuma ɗanta suka mutu a cikin sunduƙin Titan a ƙoƙarin tafiya yawon buɗe ido karkashin teku a makon da ya gabata, ta shaida wa BBC cewa da ita aka yi niyyar tafiyar.

    Titan

    Asalin hoton, FACEBOOK/CHRISTINE DAWOOD

    Bayanan hoto, ...

    Christine Dawood, ta ce gurbinta ne ta bai wa ɗanta mai shekara 19, Suleiman.

    Ta ce tun lokacin da ta samu labarin abin da ke faruwa ta fitar da rai, ta sanar da 'yan uwanta cewa tana cikin shiri kawai.

    Titan

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ....

    Suleiman ya mutu tare da mahaifinsa, Shahzada a iftila'in tarwatsewar jirgin, tare da wasu maza uku, a kokarin ziyartar tarkacen jirgin Titanic da ke can kasan teku.

    Jami'an tsaron kan teku na Amurka, sun ce fatansu shi ne wannan bincike ya inganta tsaro a harkokin da suka shafi tekuna a duniya.