Kashi ɗaya cikin uku na arziƙin Najeriya na iya zama kuɗaɗen bashi - DMO

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Rufewa

    To, masu bibiyarmu a nan ne muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke gabatar muku. Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.

    Sai ku tara gobe Juma'a don samun wasu labarai da rahotannin daga sassan duniya. A madadin duka sauran abokan aikina, ni Mukhtari Adamu Bawa ke muku fatan alheri.

    Amma kuna iya ci gaba da duba labaran da muka rigaya muka wallafa muku a ƙasa!

  2. An kaddamar ta motoci masu amfani da kati a Abuja

    ...

    An kaddamar da motocin haya na zamani masu amfani da kati a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

    Kamfanin nairexi ya kaddamar da wannan tsari wanda zai fara aiki a abuja kafin ya fadada zuwa wasu jahohin arewacin kasar, a halin yanzu kamfanin ya fara sufuri ta hanyoyin zamani a birnin Abuja.

    Shugabannin kamfanin sun bayyana cewa sun kawo wadannan motocin ne domin nuna goyon bayansu da kuma bayar da gudunmuwarsu wajen cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke yi ta kokarin rage radadin da al’ummar kasar ke ciki sakamakon cire tallafin.

    ...
    ...
  3. An kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe a Sudan

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Ana ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen kaya a ofisoshin jakadanci na kasashen waje a Sudan, inda Aljeriya ta kasance kasa ta baya bayan nan da ta yi korofi.

    A ranar Laraba, ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta ce an kai hari gidan jakadanta da ke babban birnin kasar, Khartoum.

    Ta ce harin ya saba wa dokokin kasa da kasa, ta kuma yi kira ga mahukuntan Sudan da su hukunta wadanda suka aikata laifin.

    Zimbabwe ita ma ta yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancinta da kuma gidan jakadanta a birnin Khartoum, inda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya zargi dakarun RSFF da hannu a cikin harin.

    Livit Mugejo ya ce "Muna da rahotannin cewa galibin kadarorin kasashen ne aka kai wa hari. Wannan babban laifi ne, a yi amfani da yaki wajen wawushe kadarorin jami'an diflomasiyyarmu da ofishin jakadancinmu da ke can."

    A ranar Talata, Mauritaniya ta ce wasu mahara dauke da makamai sun kai hari ofishin jakadancinta da ke birnin Khartoum tare da wawashe kaya.

    Kafofin yada labaran Mauritaniya sun ce an sace akalla motoci uku da jakadan da ma’aikatansa ke amfani da su.

    Sojojin Sudan sun sha dora alhakin hare-haren kan ofisoshin diflomasiyya a kan kungiyar RSF, wacce ta musanta hannu cikin aikata laifin.

  4. Ambaliyar ruwa ta shafi 'yan Najeriya sama da miliyan 4 a 2022 - NEMA

    Flooding

    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta shafi 'yan Najeriya sama da miliyan hudu a shekarar 2022.

    Da yake jawabi a ranar Alhamis a garin Uyo yayin kaddamar da shirin matakan gargadin tunkarar bala’i ga al'ummar ƙasar, babban daraktan hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib ya ce a shekarar 2022, sama da mutane miliyan 4 ne ambaliyar ta shafa a Najeriya.

    Ya ƙara da cewa, ambaliyar ta yi sanadin mutuwar ‘yan Najeriya 665, sama da mutane miliyan 2 kuma sun rasa matsugunnai, baya ga cinye gidaje 355,986, ta kuma mamaye kadada 944,989 na gonaki.

    Shugaban ya bayyana cewa, domin duba yadda ambaliyar ruwa ta auku, hukumar tare da hukumar kula da yanayi (NiMet), da hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIHSA) sun tura ƙwararru zuwa jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

    Matakin in ji shi zai taimaka wajen tabbatar da tsarin samun gargadin zuwan ambaliyar ruwa cikin gaggawa kafin damuna ta gama kamawa.

    ...

    Asalin hoton, NEMA/Twitter

  5. Dalibai 12 sun suma lokaci daya a Mozambik

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kimanin dalibai goma sha biyu ne a arewacin Mozambik suka suma lokaci ɗaya yayin da ake karatu.

    Makarantar Sakandiren Pemba da ke lardin Cabo Delgado, ta tabbatar da cewa suman ya fi shafar 'yan mata ne a lokacin da ake karatu ranar Laraba.

    Jami’ai sun ce waɗanda abin ya shafa sun nuna alamu kamar waɗanda suka kamu da ciwon farfaɗiya.

    Sun ƙara da cewa a halin yanzu ɗaliban duk sun murmure kuma an ruwaito cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

    Babban likitan lardin, Edson Fernando, ya ce mai yiwuwa lamarin na da alaƙa da wani nau'in ciwon kai da ke haifar da rudani na motsin rai.

    Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun yawan suman ɗalibai a makarantun Mozambique ba, inda a shekarar 2010 da 2018 aka samu aukuwar irin wannan lamari a kudancin ƙasar.

    An yi kira ga masu magungunan gargajiya, masana ilimin halayyar ɗan'adam da kuma masana ilimin zamantakewa su gudanar da bincike a kan lamarin.

  6. Kashi ɗaya cikin uku na arziƙin Najeriya na iya zama kuɗaɗen bashi - DMO

    ...

    Asalin hoton, DMO

    Ofishin kula da basuka (DMO) ya gargadi gwamnatin tarayya game da karɓo ƙarin bashi, inda ya bayyana cewa kashi 73.5% na kudaden shigar ƙasar a bana za a yi amfani da su wajen biyan bashi.

    Ofishin kula da basukan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa bashin da ake bin ƙasar na iya kai wa kashi 37.1% na jimillar arziƙin da take samu daga abin da ta sarrafa a cikin gida wato GDP a bana, daga kashi 23% da aka samu a ƙarshen 2022.

    Ofishin ya danganta hasashen da ake yi na hauhawar bashin da sabbin basuka da aka ciwo daga ƙasashen waje da kuma wanda aka karbo daga babban bankin ƙasar.

    A watan jiya, Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da wasu maƙudan kuɗi da suka kai Naira tirliyan 22.7 (dala biliyan 50) daga babban bankin ƙasar, kwana 30 kafin ƙarewar wa'adin gwamnatin Buhari, da nufin ƙara kasafin kuɗi da kuma aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

    Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai dala biliyan 103 (Naira tiriliyan 46) ya zuwa Disamba 2022.

    Sabon shugaban kasa Bola Tinubu na fama da matsalar bashi, da karancin bunkasar tattalin arziki, da hauhawar farashi, da kuma tsadar rayuwa amma yana fatan yin sauye-sauyen da za su daidaita tattalin arzikin ƙasar.

  7. Kotun Switzerland ta wanke 'yan sanda a tuhumar kashe ɗan Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotu a ƙasar Switzerland ta wanke 'yan sanda shida da aka tuhuma da laifin kashe wani ɗan Najeriya mai shekaru 39, wanda ya samu bugun zuciya yayin da suka danne shi ƙasa a yunƙurin kama shi.

    Alkalan kotun sun ce ba za a iya tabbatar da cewa Mike Ben Peter ya mutu ne sakamakon matakin da 'yan sandan suka ɗauka ba.

    Lokacin da aka bayyana hukuncin, an yi ta ihun "abin kunya" a harabar kotun, yayin da wasu ke zanga-zanga a waje.

    Lauyoyin iyalan Mista Peter sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun yi amfani da karfi fiye da kima a lokacin da aka kama shi.

    Masu zanga-zangar sun ce batun na da yanayi irin na kisan George Floyd a Amurka cikin shekarar 2020.

  8. 'Yan majalisar dokokin Kenya sun amince da ninka harajin man fetur

    ...

    Asalin hoton, AFP

    'Yan majalisar dokokin Kenya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da ninka harajin da ake ɗorawa a kan kuɗin man fetur zuwa kashi 16%, lamarin da ka iya janyo hauhawar kayan masarufi.

    'Yan majalisar dokokin jam’iyya mai mulki ne suka jagoranci kaɗa ƙuri'ar ranar Laraba a kan ƙudurin, inda mutum 184 suka amince da batun a cikin sabon kudurin kudi, yayin da ‘yan majalisa 88 suka nuna adawa da shi.

    Gwamnati na neman hanyoyin tara kusan shilling biliyan 50 ($356m; £279m) na Kenya daga ƙarin harajin, inda ta ce hakan shi ne mafi dacewa a yunƙurin ƙasar na rage nauyin bashin da ke rataye a wuyanta.

    Sai dai, jagoran 'yan adawa a majalisar dokokin ya ce matakin zai zama tamkar mugunta ga al'ummar Kenya, ya kuma bayyana matakin ci gaba da batun harajin man fetur a matsayin "rana mafi ban takaici a tarihin Kenya".

    A wannan makon ne, majalisar dokokin Kenya ta yi ta nazari a kan wasu tanade-tanade da ke cikin kudurin dokar kudin wanda ke fuskantar adawa, tare da tafka muhawara kafin kaɗa kuri'a a kan gyare-gyare.

    Bayan harajin man fetur, wasu kudurorin da ke janyo ce-ce-ku-ce sun haɗar da harajin asusun gidaje da duk ma'aikatan da ke karɓar albashi za su biya, da kuma karin haraji a kan mutanen da ke da tasiri a shafukan sada zumunta.

  9. Majalisar Kano ta tantance kwamishinoni 17 a cikin 19 da gwamna ya aike mata

    s

    Asalin hoton, KANO ASSSEMBLY

    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da mutum 17 daga cikin sunaye 19 da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin amincewa da naɗinsu a matsayin kwamishinoni a jihar.

    Majalisar ta amince da sunayen ne a zamanta na ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Isam'il Falgore.

    An dai amince da mutum 17 daga cikin mutum 19 da gwamnan jihar ya aike wa majalisar, in ban da Sheikh Tijjani Auwal da Hajiya Aisha Soji, waɗanda ba su halarci majalisar ba, sakamakon tafiyarsu aikin Hajji.

    Bayan kammala tantance kwamshinonin, a yanzu hankali ya koma kan ma'aikatun da kwamshinonin za su jagoranta bayan an rantsar da su.

  10. Jami'an tsaro na farautar 'yan bindigar da suka kashe mutum 15 a Plateau

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya sun ce jami'an tsaro na neman 'yan bindigar da suka kai hare-hare kan wasu garuruwa biyu, tare da kashe a ƙalla mutum 15 a jihar.

    Rahotonni na cewa 'yan bindigar sun kashe wasu manoma shida a yankin Riyom, yayin da waso 10 suka rasa rayukansu a yankin Mangu ranar Talata.

    Maharan sun ƙaddamar da hari kan garuruwan biyu inda suka kashe mutane tare da cinna wuta kan gidaje masu yawa.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar Mista Gyan Bere ya shaida wa BBC cewa an shirya tawagar jami'an tsaro da ta ƙunshi sojoji da 'yan sanda domin kare garuruwan tare da farauto maharan.

    Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya gaji irin waɗannna hare-hare ne daga tsohuwar gwamnatin jihar.

    ''Gwamna na ganawa da shugabannin tsaro da jagororin al'umma domin magance matsalar da ake ciki, da kuma maido da zaman lafiya a faɗin jihar'', in ji shi.

    Mista Bere ya ce gwamnatin jihar ba ta kai ga gano waɗanda ke kai hare-haren ba.

    Sai dai kafofin yaɗa labaran ƙasar na ruwaito cewa hare-haren ramuwar gayya tsakanin makiyaya da manoma ne ke yawan haddasa irin waɗannan kashe-kashe a jihar.

    Rahotonni na cewa kusan mutum 200 ne suka mutu tun watan Mayu a rikice-rikice masu alaƙa da manoma da makiya.

  11. Gobara ta kashe ƙananan yara biyu cikin gini a Afirka ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, SAPoliceService/Twitter

    Yara biyu masu shekaru biyar da bakwai sun mutu a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu bayan da wata gobara ta tashi a wani gini da aka bar su ba tare da kula da su ba kuma aka kulle su a cikin wani gida.

    Gobarar wadda ta tashi a yankin Hillbrow ,ta fara ne da yammacin Laraba.

    Wani dan Jaridar Times Live ta Afirka ta Kudu ya wallafa wani bidiyo daga wurin da aka dauki hoton gobarar bayan da jami’an kashe gobara suka iso

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Shugaban yankin, Kabelo Gwamanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, inda ya yaba wa jami’an kashe gobara bisa kokarin da suka yi, ya kuma ce tsoffin gine-ginen Hillbrow ba su cika ka’idojin inganci da tsaro ba.

    "Wannan gidan ya kasance daya daga cikin gidajen da ke nuna ƙoƙarin da gwamnatin Johannesburg ke yi na ƙwato gine-ginen da aka sace daga masu zama ba bisa ƙa'ida ba da kuma masu aikata laifuka," in ji shi.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin ta ce ga dukkan alamu yaran sun mutu ne sakamakon shaƙar hayaƙi kuma daga baya aka gano gawarwakinsu a ƙone har ba a iya gane su.

    Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba, kuma ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike.

  12. Abu huɗu da Muhuyi zai binciki gwamnatin Ganduje a kai

  13. Amurka ta soki ɓangarorin da ke faɗa da juna a Sudan

    Shugabar hukumar raya ƙasashe ta Amurka USAID, ta soki ɓangarorin da ke faɗa da juna a yakin da ake yi a Sudan.

    Inda miliyoyin mutane ke cikin tsananin buƙatar taimakon, sakamakon rashin aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta da ake ta cimmawa.

    Yaƙin wanda ya ɓarke a tsakiyar watan Afrilu tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun RSF ya tilasta wa fiye da mutum miliyan biyu da rabi barin muhallansu.

    Kai tallafin abinci da sauran kayayyaki ga miliyoyin mutanen da yaƙin ya ɗaiɗaita na ƙara samun tasgaro.

    Hukumar raya ƙasashen ta Amurka na aiki kai tseye da kungiyoyin tallafi na ƙasar da ke bi gida-gida duk kuwa da yawan hare-haren boma-bomai da ake samu a wasu yankunan kasar.

    Shugabar ta USAID Samantha Power ta ce sojojin da ke yaƙi don ƙwace iko da ƙasar ba sa kula da abubuwan da suke ɓarnatarwa a kasar.

  14. Saudiyya ta samar da motoci marasa matuƙa don jigilar mahajjata

    c

    Asalin hoton, Getty Images

    Saudiyya za ta ƙaddamar da motoci marasa matuƙa masu amfani da lantarki, da za su yi jigilar mahajja a aikin hajjin bana.

    Hukumar kula da sufurin ƙasar ta ce ta ɗauki matakin ne domin zamanantar da kuma sauƙaƙa harkar sufuri a ƙasar.

    Matakin na daga cikin yunƙurin da hukumomin ƙasar ke yi don faɗaɗa harkokin sufuri musamman a lokacin aikin hajjin bana.

    Sabbin motocin masu sarrafa kansu na ɗauke da kyamarori da wasu abubuwa da za su sanya su yin aiki da kansu ba tare da wata matsala ba.

    Motocin kan tattara bayanai a lokacin da suke aiki, tare da yin nazari a kan bayanan, domin ɗaukar mataki.

    Manyan motocin waɗanda ke da kujeru 11, za su iya yin gudun kilomita 30 a cikin sa'a ɗaya, kuma batirinsu zai iya riƙe chaji na tswon sa'o'i 6.

  15. Tashe-tashen hankula na barazana ga babban zaɓen Saliyo

    gg

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu arangama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan babbar jam'iyyar adawar Saliyo All People's Congress(APC), lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum guda, tare da tilasta rufe kasuwanni a babban birnin ƙasar Freetown.

    Lamarin na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar mai zuwa..

    Mutane na ta yin tururuwar zuwa kasuwanni domin sayen kayan abinci, sakamakon fargabar ɓarkewar ƙarin rikici a birnin, kamar yadda wasu mazauna birnin suka shaida wa BBC.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito mai magana da yawun babbar jam'iyyar adawar ƙasar Sidi Yahya Tunis na cewa 'yan sanda sun kashe ɗaya daga cikin magoya bayan jam'iyyar a lokacin arangamar.

    Wani bidiyo da BBC ba ta tabbatar da sahihancinsa ba, ya nuna wani mutum na cikin rashin hayyaci, sakamakon harbinsa da aka yi a wuya.

    Shugaban rundunar 'yan sandan ƙasar Braima Jah ya ce 'yan sanda ba su yi harbi ba. inda ya zargi masu zanga-zangar da yin harbi har sau biyar, ''Biyu daga ƙaramar bingigar pistol, sannan uku daga bindiga ƙirar AK-47.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an kama mutum 66 kan rikicin.

    Rikicin ya ɓarke bayan da jam'iyyar adawar ƙasar ta zargi hukumar zaɓe da tafka kura-kurai a rajistar masu kaɗa ƙuri'a.

    Cikin jawabin da shugaban ƙasar Julius Maada Bio ya gabatar, ya sha alwashin ɗaukar matakin ba-sani, ba-sabo kan masu tayar da rikici a ƙasar.

    A wata sanarwar haɗin gwiwa da Birtaniya da Amurka da Ireland da Jamus da Faransa da ƙungiyar EU suka fitar, sun yi kira ga duka ɓangarorin su zauna cikin kwanciyar hankali.

    Zaɓen shi ne na biyar tun bayan ƙarshen yaƙin basasar ƙasar a 2002, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 50,000, tare da raba dubbai da muhallansu.

    Mista Bio na neman wa'adin shugabancin ƙasar na biyu kuma na ƙarshe, inda yake fafatawa da sauran 'yan takara, ciki har da na babbar jam'iyyar adawar ƙasar APC Samura kamara, wanda ya zo na biyu na zaɓen 2018.

    Mista Kamara na fuskantar shari'a kan zargin rashawa tun 2021, zargin da ya ce bi-ta-da-ƙulli siyasa ne kawai.

    Ana sa rana kusan mutum miliyan 3.4 ne za su kaɗa ƙuri'unsu ranar 24 ga watan Yuni a ƙasar da ke fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da kashi 43 cikin 100.

  16. Tinubu ya hallara a wurin taron harkokin kuɗi a Paris

    w

    Asalin hoton, Daddy D.O

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa dakin taron da za a gudanar da babban taron harkar kuɗaɗe da tallafawa ƙasashe masu rauni, da za a gudanar a birnin Paris.

    Shugaban ya samu tarbar ministar harkokin ƙasashen wajen Faransa da nahiyar Turai Catherine Colonna.

    ds

    Asalin hoton, Daddy D.O

    Taron shi ne na farko da shugaban na Najeriya ke halarta tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar ranar 29 ga watan mayun da ya gabata.

  17. Atiku na gabatar da shaidu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa

    d

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

    Kotun sauraron ƙararraƙin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta ci gaba da zaman saurarorin ƙorafin jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.

    A baya dai kotun ta ɗage zaman sauraron ƙararrakin zuwa yau Alhamis domin bai wa jam'iyyar damar gabatar da shaidunta.

    Jam'iyyar PDP da ɗan takarar tata Atiku Abubukar sun shigar da ƙara a gaban kotun domin kalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

    Hukumar zaɓen ƙasar INEC ce ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

    Matakin da jam'iyyun adawa ciki har da PDP da LP suka ce ba su gamsu da shi ba.

    Lamarin da ya sa jam'iyun da 'yan takararsu suka garzaya kotun suna neman ta soke zaɓen da ya bai wa Tinubu nasara a zaɓen.

  18. Ƙasashen duniya na ɗari-ɗari da Taliban – MDD

    Taliban

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Afganistan ta ce abu ne mai matukar wuya ƙasashen duniya su amince da gwamnatin Taliban matukar ta ci gaba da taƙaita ƴancin mata.

    Roza Otunbayeva ta shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa matakan da gwamnatin Taliban din ta dauka na iyakance damarmakin mata, ba su samu amincewa ba a wajen 'yan kasar.

    Ta ce a tattaunawar da ta sha yi da shugabanninsu, ta fito karara ta nuna musu irin matsalolin da suka haifar, da yadda suka jefa rabin al'ummar ƙasar cikin wahala, da lalata tattalin arziƙin ƙasar.

    Yanzu haka an haramta wa mata yawancin ayyuka, da kuma zuwa wuraren taruwar jama'a, kamar makarantu da wuraren shaƙatawa.

    'Yan Afganistan sun fuskanci matsalar jin kai mafi girma a duniya tun bayan da Taliban suka kwace iko da su kusan shekaru biyu da suka gabata.

  19. Adadin mutanen da suka mutu a gidan yarin Hoduras na hauhawa

    Gidan yarin Hoduras
    Bayanan hoto, ...

    Akalla mata 46 ne aka kashe a wata tarzoma a gidan yarin mata da ke Honduras.

    Hukumomin kasar na ci gaba da ƙokarin zaƙulo gawarwakin fursunonin, wadanda da yawansu suka kone kurmus a lokacin da wasu abokan gabar su suka haddasa gobara, wasu an harbe su ne, kuma wasu caka musu wuka aka yi

    Ana ci gaba da bincike domin gano yadda fursunonin suka yi nasarar shigo da makamai masu sarrafa kansu da adduna zuwa cikin gidan yari.

    Shugabar kasar Honduras, Xiomara Castro, ta ce an shirya tarzomar da sanin jami'an tsaron gidan yarin.

    Ta shirya daukar tsauraran matakai don magance tashe-tashen hankula a nan gaba.

    Dama an sha fama da rikicin gidan yari irin wannan a Hondurus.

  20. Mutum 31 sun mutu a wani gidan cin abinci

    Fashewar Gas
    Bayanan hoto, ...

    Wata fashewa a wani gidan cin abinci da ke birnin Yinchuan da ke arewa maso yammacin ƙasar China ta kashe mutane 31.

    Yanzu haka ƙarin wasu mutum bakwai na kwance a asibiti, cikin mawuyacin hali.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce yoyon iskar gas a gidan abincin ne ya haddasa fashewar a daren Larabar da ta gabata.

    Bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna mummunan yanayin lamarin a kofar shiga wurin cin abincin, inda ake iya ganin gawarwakin mutane warwatse.

    Shugaba Xi Jinping ya yi kiran a gaggauta bayar da kula gaa waɗanda suka jikkata tare da gano musabbabin hatsarin, domin ɗaukar matakan da suka dace.

    Tuni dai hukumomi suka kama mutum tara da ake zargi da hannu a fashewar.