'Yan Isra'ila sun ci gaba da kai harin maida martani bayan harbe-harbe da aka yi

Asalin hoton, EPA
An harbe wani Bafalasdine har lahira tare da raunata wasu da dama bayan da wasu 'yan Isra'ila mazauna yankin suka kai wani mummunan hari a yammacin gabar kogin Jordan da isra'ila ta mamaye.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa suna fargabar tsira rayukansu yayin da daruruwan 'yan isra'ila dauke da makamai suka kona gidaje da motoci a garin Turmusaya.
Daya daga cikin mutanen ya zargi sojojin Isra'ila da barin su ba tare da taimako ba na tsawon mintuna 45 yayin harin.
“Sun bai wa mazauna yankin damar yin hakan,” in ji shi.
Ana ganin cewa harin ramuwar gayya ne, ganin ya zo sa'o'i bayan jana'izar wani matashi dan shekaru 17 da haihuwa wanda ke cikin wasu 'yan Isra'ila hudu da wasu 'yan bindiga Falasdinawan suka harbe a wani gidan mai a ranar Talata.
Sojojin Isra'ila sun yi Allah wadai da harin da mazaunan suka kai, amma ba su amsa tambayoyi kan saurin da suka yi na kai agaji ko kuma yanayin matakin da suka dauka ba.
Ana ci gaba da fargabar barkewar wani mummunan tashin hankali a yammacin gabar kogin Jordan, bayan wani farmaki da sojojin Isra'ila suka kai a birnin Jenin a ranar Litinin da ta gabata, inda suka kashe Falasdinawa bakwai.















