Fiye da mutum 70 sun mutu a haɗarin jirgin ruwa a Girka
Akalla mutane 79 ne suka mutu sannan aka ceto sama da 100 a yayin da wani jirgin ruwa na kamun kifi ya nutse a kudancin ƙasar Girka.
Waɗanda suka tsira sun ce aƙalla mutum 750 ne suka makale a cikin kwale-kwalen, ciki har da ƙananan yara fiye da 100.
Gwamnatin ƙasar ta ce lamarin na cikin mummunan abu mafi girma da ya sami `yanci rani, ta kuma ayyana zaman makoki na kwana uku.
Hukumomin ƙasar sun ce ba su samu taimakon da suka buƙata daga ƙasashen duniya na ceto mutanen da lamarin ya shafa ba.
Sun ce a maimakon hakan, sai aka riƙa zarginsu da rashin yin abin da ya dace don taimakawa.
Wani jami'i a hukumar da ke kula da 'yanci rani a Girkan, ya shaida wa BBC cewa, an yi nasarar ceto mutum 104, sannan kuma bai tabbatar da rahoton ɓacewar wasu da dama ba.
Jirgin kwale kwalen ya taso ne daga Libya inda ya kife tare da nitsewa a ɗaya daga cikin wuri mafi zurfi a tekun Bahar Rum.