Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tinubu ya naɗa Nuhu Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan tsaro
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza
Kotu a Kenya ta buƙaci a yi wa masu azumin mutuwa gwajin ƙwaƙwalwa
Wata kotu a kasar Kenya ta yanke hukuncin mayar da mutane 64 da suka tsira daga wata kungiyar asiri zuwa cibiyar ceto inda ya kamata a duba lafiyar kwakwalwarsu sannan a ba su shawarwari.
Za a tuhume su da laifin yunkurin kashe kansu, wanda aka bayyana a matsayin laifi a Kenya.
Sai dai an tura wata 'yar kungiyar zuwa ɓangaren mata na wani gidan yari kasancewar ta ki ba 'yan sanda hadin kai kuma ta ce za ta ci gaba da kin cin abinci.
An yi zargin cewa shugaban kungiyar Paul Mackenzie shi ya umarce su da su kashe kansu da yunwa domin su shiga Aljanna cikin gaggawa.
Sama da gawarwakin mutane 300 ne aka tono daga kaburburan da ba su da zurfi a cikin wani dajin mai nisa da ke tafiyar sa'o'i biyu daga gabar teku. Wasu fiye da 600 sun ɓata.
Babbar kungiyar kare hakkin bil adama ta gwamnati ta yi kira ga gwamnati da ta yi watsi da zargin yunkurin kashe kansu da ake yi wa wadanda suka tsiran.
Yadda kwale-kwale ya kife tare da kashe sama da mutum 100 a Kwara
Gini ya danne masu ɗibar 'ganima' a wurin rusau a Kano
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa gini ya danne wasu matasa a wurin da aka gudanar da rusau kan gine-gine a sassan jihar, inda da dama suka jikkata..
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne yayin da ragowar gine-ginen da aka rusa a Otal din Daula da kuma Filin Idi suka ruguje, daidai lokacin da wasu mutane suke rububin wawashe dukiya a filayen.'
Sanarwar ta kara da cewa "Yayin da kwamishinan ƴan sandan jihar ke jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ransu da waɗanda suka jikkata, ya yi kira ga iyaye, da shugabannin al’umma da su gargaɗi yaransu da su guji waɗannan wuraren."
Kotu ta umarci ƴansanda su mayar da kayan da suka kwashe daga gidan Matawalle
Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Gusau ta umarci rundunar ‘yan sandan Najeriya da wasu hukumomi hudu da ke da hannu wajen kwashe motoci da sauran kayayyaki daga gidajen tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da su mayar da su cikin sa’o’i 48.
A ranar 9 ga watan Yuni ne ‘yan sanda tare da jami’an DSS da NSCDC suka kai samame a gidajen tsohon gwamnan a Gusau da Maradun inda suka yi awon-gaba da motoci da wasu kayan gwamnan da na iyalansa bisa umarnin wata karamar kotu.
Daga baya a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta kwato motoci 40 a lokacin samamen amma ta yi shiru kan sauran kayan da tsohon gwamnan ya yi zargin an kwashe.
Alƙalin kotun mai shari’a A.B Aliyu, ya umurci waɗanda ake ƙara da su mayar da dukkanin motoci da sauran kayan da suka kwashe, tare da bayani a rubuce kan dukkanin kayan, sannan su miƙa su ga kotu.
Kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da wadanda ake ƙarar da suka hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da sufeto janar na 'yan sanda, da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da hukumar DSS da kuma NSCDC daga ɗaukar wani mataki dangane da lamarin tare da dakatar da duk wani mataki da za a dauka har sai an saurari karar da ke gaban kotun a ranan 28 ga watan Yuni.
Messi ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a tarihinsa na tamaula
Shugaban Uganda ya musanta cewa yana cikin halin rai-kwakwai mutu-kwakwai
Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya yi jawabi ta intanet ga majalisar dokokin kasar, inda ya yi watsi da rahotannin kafafen sada zumunta da ke cewa yana fama da rashin lafiya kuma yana sashen kula na musamman a asibiti.
Shugaban, wanda ya kamu da cutar korona a makon da ya gabata, ya wallafa a ranar Laraba cewa ba shi da alamun cutar, ko da yake an ga alamun ƙwayoyin cutar a jikinsa a gwajin da aka yi masa.
Ya gode wa ‘yan kasar Uganda da suke yi masa addu’a tare da aikewa da sakonni domin neman ya samu sauki cikin gaggawa.
Wannan jawabin da ya yi ta intanet shi ne na farko, inda a ce ba ya fama da cutar ta korona da shugaban ya yi jawabi gaban majalisa da kansa a lokacingabatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2023-2024.
Ministan kudi Matia Kasaija, wanda ya gabatar da jawabin kasafin kudin, ya shaida wa majalisar cewa ana sa ran tattalin arzikin kasar zai ci gaba da murmurewa daga illar cutar korona.
Mista Museveni ya ce gwamnati za ta ci gaba da mayar da hankali kan ababen more rayuwa, masana'antu, da kara darajar kayayyakin amfanin gona don bunkasar tattalin arziki.
Za a ɗaure iyayen da suka kashe ɗansu ta hanyar azaba da ƙanƙara
Wata mata da mijinta ta za su sha ɗauri bayan wata kotu ta kama su da laifin kashe ɗanta mai shekara tara a cikin bahon wanka bayan shafe watanni ana cin zarafinsa.
Hukumomi sun iske yaron mai suna Alfie Steele ba ya motsi lokacin da suka isa gidan da ke yankin Droitwich, Worcestershire, a watan Fabrairun 2021.
Kotun Coventry Crown ta samu Dirk Howell, mai shekaru 41, da laifin kashe matashin yaron kuma da mahaifiyarsa, Carla Scott, da laifin kisa.
Bayan da aka shafe makonni ana sauraron ƙarar inda aka kawo bayanai masu ban tsoro game da abin da yaron mai shekaru tara ya fuskanta a cikin watanninsa na ƙarshe, alkalan kotun sun dauki sa'o'i 10 wajen sanar da matsayarsu.
Alfie ya fuskanci mugun horo kuma ya samu raunuka sama da 50 a jikinsa lokacin da ya mutu.
Ko da yake ba a tabbatar da ainihin abin da ya kashe yaron ba, shaidu sun nuna cewa ya mutu bayan da aka tilasta masa shiga cikin ruwan ƙanƙara.
Azabar da aka yi masa sun hada da duka, da tilasta masa tsayawa a waje tare da nutsar da kansa a cikin bahon wanka maƙare da ruwa mai tsananin sanyi.
Wasu makwabta sun ji shi yana ihu yayin da aka tilasta masa shiga bahon wankani, wasu kuma sun ce sun gan shi a tsaye “kamar gunki" da a cikin daren yayin da abokin zaman mahaifiyar tasa ke ta yi masa ihu.
Mahaifiyar Alfie ta sha kuka lokacin da ake kan hanyar kai ta gidan gyaran hali, amma abokin zaman nata bai nuna wata alama ta nadama ba.
Mahaifiyar da ta rasa 'ya'ya uku a jirgin da ya nutse da 'yan biki a Kwara
Afcon 2024: Tawaga takwas ta sami gurbin shiga kofin Afirka
Abdulkarim Chukkol ya karɓi Bawa a matsayin mai riƙon shugaban EFCC
Bayan dakatar da Abdulrasheed Bawa, a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Abdulkarim Chukkol ya zama shugaban riƙo na hukumar.
Kafin wannan lokaci, Abdulkarim Chukkol na riƙe da muƙamin daraktan gudanarwa a hukumar.
Sabon shugaban riƙon ƙwararre ne a harkar bincike kuma ya gwanance a ɓangaren bincike kan ayyukan zamba ta intanet da halasta kuɗaɗen haram.
Chukkol ya kammala karatun digiri a Jami’ar Maiduguri a shekarar 2000 sannan ya yi karatun difloma a fannin shari’a a Jami’ar Virginia da ke Amurka a 2011.
Jami`in binciken ya fara aiki da hukumar EFCC ne a shekara ta 2003.
Chukkol ya shiga cikin ayyukan bincike na ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da manyan hukumomi kamar hukumar bincike ta FBI da ke Amurka da kuma 'National Crime Agency' ta Birtaniya.
Ya taba zama shugaban ofishin EFCC shiyyar Fatakwal kafin ya koma babban ofishin hukumar da ke Abuja.
A ranar Laraba ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar ta EFCC, AbdulRasheed Bawa, inda ya ce za a gudanar da bincike kan wasu manya zarge-zarge da ake yi masa.
Hukumar tsaro ta DSS ta ce ta gayyaci Bawa zuwa ofishinta ne domin yi masa tambayoyi, sa'o'i kaɗan bayan dakatar da shi.
Tinubu ya naɗa Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban ciki har da Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.
Wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yaɗa labarai a fadar shugaban Najeriya ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da naɗe-naɗen da suka haɗar da Mista Dele Alake a matsayin mai ba da shawara kan harkar ayyuka na musamman, sadarwa da tsare-tsare.
Akwai kuma Mallam Ya'u Darazo a muƙamin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da hulɗa tsakanin gwamnatoci.
Haka zalika, Tinubu ya amince da naɗa Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan manufofin kuɗi.
Akwai kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin makamashi, inda Tinubu ya naɗa Misis Olu Verheijen.
Ƙarin masu bayar da shawarar har da Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kuɗin shiga.
An kuma naɗa Dr. Salma Ibrahim Anas a muƙamin mai ba da shawara ta musamman a fannin kula da lafiya.
Sai kuma Mista John Ugochukwu wanda aka naɗa mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana'antu, kasuwanci da zuba jari.
Yadda sabon tsarin canji na CBN zai shafi darajar naira
Tinubu ya ƙaddamar da majalisar kula da tattalin arzikin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
An kaddamar da majalisar ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima a zauren majalisar da safiyar ranar Alhamis.
A wani saƙo da Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na twitter ya ce an ƙaddamar da majalisar ne a zaurenta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.
Ƙwarya-ƙwaryar bikin ya samu halartar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume da gwamnonin jihohin ƙasar 36.
Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da majalisar, shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnonin su haɗa kai, wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da ababen more rayuwa, duba da manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
“Ni da ku duk muna buƙatar hakan, kan haka muka gudanar da yakin neman zaɓukanmu, har ma muka yi rawa a gaban jama'a don jaddada alƙawuranmu, don haka, ba mu da dalilin yin korafi kan haka. 'Yan Najeriya na nuna mana goyon baya. Suna son gyara kuma suna son hakan cikin gaggawa''.
Dakarun RSF sun yi Allah wadai da kisan gwamnan Darfur
Dakarun RSF masu sanye da kayan sarki a Sudan sun yi Allah wadai da kisan gwamnan yammacin Darfur Khamis Abbakar da aka yi ranar Laraba.
Tun da farko dai jami'an sojin ƙasar sun zargi dakarun na RSF da kisan gwamnan, wanda sa'o'i kafin kisan nasa aka ambato shi yana zargin dakarun na RSF tare da haɗin gwiwwar masu tayar da kayar bayan da ke ƙawance da su da aikata laifukan kisan kiyashi kan al'ummar ƙabilar Masalit.
To sai dai a wata sanarwa da RSF din ta fitar ta ce gwamnan ya mutu ne a hannun wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, duk kuwa da yunƙurin da RSF ta ce dakurunta sun yi domin kare gwamnan.
“Wasu mambobin ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya ne suka kai samame gidansa, lamarin ya suka sace tare da yin garkuwa da gwamnan inda suka yi masa kisan wulakanci da rashin tausayi'', in ji sanarwar.
Dakarun na RSF sun yi kiran a gudanar da bincike game da lamarin, ta kuma a shirye take wajen hukunta duk wani mambanta da aka samu da hannu a kisan gwamnan.
Mutuwar gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ƙaruwar rikicin ƙabilanci da zargin fyaɗe da ake yi wa fararen hula a yankin Darfur.
An kwashe sama da mutum 170,000 a Indiya da Pakistan saboda guguwa mai ƙarfi
Mutane fiye da 170,000 ne aka kwashe daga wuraren da wata mummunar guguwa za ta ratsa a Indiya da Pakistan kafin aukuwarta a ranar Alhamis.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa guguwar mai suna Biparjoy - wanda ke nufin "iftila'in guguwa" a yaren Bengali - na iya lalata gidaje da gonaki.
Ana sa ran guguwar za ta fara dira jihar Gujarat ta Indiya ranar Alhamis da yamma agogon ƙasar.
Hotuna daga gabar tekun jihar sun nuna ɓarkewar ruwan sama mai yawa da murɗa-murɗan igiyoyin ruwa da kuma haukacewar teku.
Ana sa ran guguwar za ta lafa a kusa da tashar jiragen ruwa ta Jakhau da ke tsakanin Mandvi a Gujarat da Keti Bandar cikin lardin Sindh na Pakistan.
Sojan Amurka ya amsa laifi kan yunƙurin taimakawa 'ƙungiyar 'yan ta'adda'
Namibiya za ta sayar da kadoji guda 40 don rage rikici
Kafofin yaɗa labaran Namibiya sun bayyana cewa, ƙasar za ta sayar da wasu kadaji guda 40 domin rage rikicin da ake samu tsakanin mutane da namun daji a yankunan Kavango da Zambezi, arewa maso gabas.
Ana sa ran masu sha'awar sayen dabbobi masu jan ciki za su gabatar da tayin su ga ma'aikatar muhalli nan da ranar 17 ga watan Yuli.
Mai magana da yawun ma'aikatar, Romeo Muyunda ya ce yawancin namun dajin Tanzaniya "suna rayuwa a gandun shaƙatawa na ƙasa", abin da ya sa mazauna yankunan ke "ci gaba da fuskantar hare-haren kadoji da ke auka wa mutane da dabbobinsu".
Dole ne masu saye su tabbatar cewa suna da wurin da ya dace da dabbobin kuma su ne za su biya kuɗin kama kadojin.
Masu neman fita da su zuwa ƙetare, dole ne su samu izini daga ƙasashensu.
Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi ɓullo da shirin rage raɗaɗi bayan cire tallafin mai
Majalisar Wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin da ta ɗauka na samar da matakan daƙile illolin cire tallafin man fetur a tsakanin ‘yan Najeriya.
Kiran ya zo ne bayan amincewa da wani kudurin da Aliyu Sani Madaki na jam'iyyar adawa ta NNPP daga Kano ya gabatar a zauren majalisar ranar Laraba.
Da yake gabatar da kudurin, ɗan majalisar ya tunasar cewa a ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur wanda hakan ya sa farashin litar mai ya ƙaru daga N194 zuwa sama da N500 a gidajen mai.
Ya ce tun a wancan lokacin ‘yan Najeriya ke ta fama da hauhawar farashin man fetur da kuma illar da ke tattare da haka musamman a kan kayan masarafi kamar abinci da ayyuka waɗanda duka farashinsu ya tashi sosai.
Ya ce akwai bukatar a samar da matakan kare hakkin ‘yan ƙasa tare da ba da fifiko wajen samar da kayan agaji domin daƙile ƙalubalen da suka taso daga cire tallafin man fetur ɗin, da kuma tabbatar da tsarin tattalin arziki mai ɗorewa da hada kan ‘yan Najeriya.
Majalisar ta ɗora wa kwamitin ƙwadago alhakin yin nazari a kan batun tare da bayar da rahoto don ci gaba da aiwatar da shawarwarin da aka bayar.
An kama shugabannin cocin Tanzaniya 'saboda tsare marasa lafiya'
Hukumomin ƙasar Tanzaniya sun kama wasu shugabannin coci guda biyu bisa zargin tsare marasa lafiya da dama yayin da suka yi alkawarin warkar da su ta hanyar addu'o'i da kuma dafa'in gargajiya.
An ajiye fiye da mutum 100 a wuraren da ake kira gine-ginen mutanen da (bukkoki masu gadon dakali) da aka yi a kusa da cocin wadda ke ƙauyen Nyamhinza, gundumar Misungwi, arewa maso yammacin Mwanza - ba tare da maganin asibiti ko abinci ba.
Wasu sun yi kusan wata ɗaya a wurin kuma an buƙaci su nemo wa kansu abinci har sai sun warke sosai.
An gano su ne bayan mutanen yankin sun sanar da ‘yan sanda cewa wasu mutane na mutuwa idan sun bar asibitoci, ciki har da wata mata da ta shiga cocin jim kadan bayan ta haifi tagwaye.
A ƙarshen makon jiya ma, ‘yan sanda sun mayar da marasa lafiyar zuwa asibitoci domin yi musu magani.
Yanzu haka suna bincike a kan yiwuwar mace-mace da kuma ko akwai gawawwakin da aka binne a kusa.