Yadda gwamnoni 28 suka sha ranstuwar kama aiki a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku yadda ake rantsar da sabon shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Da fatan za mu sake haɗuwa gobe da safe domin kawo muku wasu sababbi fil.

    Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  2. Tinubu ya taya Erdogan murnar cin zaɓen Turkiyya

    Erdogan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan murnar lashe zaɓe karo na uku.

    Tinubu wanda shi ma aka rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya a yau Litinin, ya ce nasarar Erdogan alama ce ta "yardar da ke tsakanin al'ummar Turkiyya da shugaban".

    "Ina yi masa fatan alheri kuma ina fatan za mu yi alaƙa mai cike da haɗin kai tsakanin ƙasashenmu," a cewar Tinubu cikin wani saƙon Twitter.

    Mista Erdogan zai shafe ƙarin shekara huɗu a kan mulki bayan ya shekara 20 yana jagorantar ƙasar da ke kusurwar Asiya da Turai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Muhimman alƙawuran da Tinubu ya ɗauka

  4. An rantsar da Francis Nwifurunke sabon gwamnan Ebonyi

    Enugu

    Jama'a sun taru a filin wasa na garin Pa-Ngele Oruta da ke jihar Ebonyi don shaida rantsuwar kama aiki da Francis Ogbonna Nwifuru ya yi a matsayin gwamnan Jihar Ebonyi.

    Mista Nwifuru ya yi nasara a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin jihar, inda ya gaji David Umahi wanda ya shekara takwas a kan mulki.

    'Yan jarida da jami'an tsaro da jami'an gwamnati sun yi cunkoso a wurin.

  5. Labarai da dumi-dumi, Mai gidan talabijin na AIT Raymond Dokpesi ya rasu

    Raymond Dokpesi

    Asalin hoton, @Atiku

    Shugaban kamfanin sadarwa na Daar Communications Raymond Dokpesi, ya rasu ranar Litinin.

    Rahotanni a Najeriya sun ambato iyalan mutumin mai shekara 71 na ba da sanarwar rasuwar tasa, amma ba su bayyana abin da ya yi ajalinsa ba.

    Gidan talabijin na AIT na ƙarƙashin kamfanin Daar Communications, wanda kuma ya mallaki gidan rediyon Ray Power.

    "Cikin alhini da ɓacin rai, muna sanar da rasuwar Chief Raymond Aleogho Anthony Dokpesi, wanda ya mutu ranar Litinin, 29 ga watan Mayu," a cewar sanarwar.

    Baya ga harkokin sadarwa, Dokpesi ɗan siyasa ne wanda ya taɓa neman takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP.

  6. Ina Atiku ya je a ranar rantsuwa?

    Atiku da Gwamna Fintiri

    Asalin hoton, @atiku

    Ɗan takarar adawa na jam'iyyar PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya halarci bikin rantsar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin gwamnan Adamawa.

    Da safiyar yau Litinin aka rantsar da Fintiri don jagorancin jihar, wadda ita ce mahaifar Atiku, karo na biyu bayan ya yi nasara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

    "Na bi sawun al'ummar Jihar Adamawa wajen taya Gwamna Fintiri da mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta murnar nasara da kuma rantsuwar kama aiki a karo na biyu," in ji Atiku cikin wani saƙon Twitter.

    A gobe Talata kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta ci gaba da zama a shari'ar ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu, wadda Atiku da PDP suka shigar duk da cewa an rantsar da shi a yau.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. An rantsar da Sanata Bala Mohammed a matsayin gwamnan Bauchi a wa'adi na biyu

    Sanata Bala Abdulkadir Mohammed

    Asalin hoton, Zainab Sabitu

    Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya sake kama mulki a matsayin gwamnan Jihar Bauchi a wa'adi na biyu bayan sake rantsar da shi yau a bikin da ya gudana a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi, babban birnin jihar.

    Manyan baki da magoya baya da kuma masu fatan alheri ga Kauran na Bauchi, ne suka yi tururuwa zuwa filin wasan domin halartar bikin.

    Sanata Bala ya kasance a matsayin gwamnan jihar tun 2019 a karkashin jam'iyyar PDP.

    Kafin sannan ya yi ministan babban birnin tarayyar Najeriyar Abuja daga 2010 zuwa 2015, da kuma Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu daga 2007 zuwa 2010.

    Sanata Bala Abdulkadir Mohammed

    Asalin hoton, Zainab Sabitu

  8. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma mahaifarsa, Daura

    Buhari a Daura

    Asalin hoton, Abubakar Dantsuntsu

    Bayan mika mulki ga Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya gaje shi a shugabancin Najeriya, tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa, Daura.

    Buharin ya tashi a jirgin saman shugaban kasa tare da mai dakinsa Aisha Buhari da wasu daga cikin ƴaƴansa da dangi da kuma ministan sufurin jirgin sama mai barin-gado Hadi Sirika, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan sun bar dandalin Eagle Square, inda suka nufi jihar katsina.

    Sabon gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Radda ne ya tarbi tsohon shugaban da tawagarsa a babban filin jirgin sama na Ummaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

    Jirgin ya sauka a Katsina da misalin 01:10 na rana, daga nan ne bayan hutu na wasu mintina sai Buharin da matarsa da kuma dansa Yusuf da wasu shugabannin hukumomin tsaro suka hau wani jirgin sama mai saukar ungulu inda suka nufi Daura.

    Buhari a Daura

    Asalin hoton, Abubakar Dantsuntsu

  9. An rantsar da Mai Mala Buni a matsayin gwamnan Yobe karo na biyu

    ..

    Asalin hoton, bb

    A yau Litinin 29 ga watan Mayu 2023 aka rantsar da gwamnan Jihar Yobe Mai mala Buni a matsayin gwamna karo na biyu.

    Buni wanda ya lashe zaben gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023 zai sake yin shekara hudu kan karagar mulki bayan shekaru hudu da ya riga ya yi daga shekaran 2019 zuwa 2023.

    ...
  10. An Rantsar da Sabon Gwamnan jihar Jigawa

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    An rantsar da sabon gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi wanda shi ne ya maye gurbin tsohon gwamna Badaru Abubakar.

  11. Alhaji Ahmad Aliyu ya kama aiki a matsayin sabon gwamnan Sokoto

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK

    Jihar Sokoto ta bi sahun wasu daga cikin jihohin Najeriya, da ma tarraya wajen rantsar da sabon gwamnanta Alhaji Ahmad Aliyu a yau Litinin 29 ga watan Mayu.

    An rantsar da sabon gwamnan na jam'iyyar APC da mataimakinsa Idris Muhammad Gobir, a bikin da aka yi a babban birnin jihar, Sokoto.

    A yau ne aka rantsar da sabon shugaban kasa a najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda ya gaji Muhammadu Buhari.

    Gwamnan na Sokoto ya kasance daya daga cikin guda 28 da aka rantsar yau a kasar mafi yawan jama'a a Afirka.

    Wasu daga cikinsu sababbi ne kamar shi wasu kuma suna wa'adinsu na biyu ne.

    Ahmad Aliyu Sokoto ya yi nasara ne a zaben gwamnan jihar da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023 inda ya kayar da dan takarar kujerar na jam'iyya mai mulki a lokacin PDP, Mallam Saidu Umar.

    Bayan cin kujerar gwamnan, jam'iyyar ta APC za kuma ta mamaye majalisar dokokin jihar ta 10, kasancewar jam'iyyar tana da kujeru 20, yayin da PDP take da kujeru goma kawai.

    Gwamnan jihar mai barin-gado Aminu Waziri Tambuwal na PDP, wanda ya kayar da Ahmad Aliyu a zaben 2019, ya yi nasara a zaben kujerar dan majalisar dattawa mai waklitar mazabar Sokoto ta Kudu inda ya kayar da mai rike da kujerar Abdullahi Danbaba Dambuwa na APC.

  12. An rantsar da Idris a matsayin sabon gwamnan Kebbi

    ...

    Asalin hoton, Twitter/@NasiridrisKG

    An rantsar da tsohon shugaban kungiyar malamai ta Najeriya NUT kuma tsohon mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Dr Nasir Idris a matsayin sabon gwamnan jihar Kebbi.

    Mukaddashin Alkalin Alkalan Jihar, Mai Shari’a Abubakar Umar ne ya rantsar da Idris tare da mataimakinsa Sanata Umar Abubakar a filin wasa na Halidu Abdu da ke Birnin Kebbi.

    Da yake jawabi ga al’ummar jihar, Gwamna Idris, wanda ya yaba da sadaukarwar da gwamnonin da suka gabata da kuma al’ummar jihar suka yi, ya ce ba zai dauki amanar da suka bari da wasa ba.

    “Ina so in tabbatar wa al’ummar Jihar Kebbi cewa gwamnatina za ta yi mulki ne da tsoron Allah, za ta yi mulki bisa maslahar jama’a ba bisa son rai ba. Za mu yi wa jama’a aiki ba tare da nuna bambanci ba,” inji shi.

  13. Tallafin man fetur ya tafi - Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce daga yanzu gwamnatinsa za ta soke batun bayar da tallafin man fetur a ƙasar.

    Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar, jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasa.

    Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta karkata kuɗaɗen ne zuwa wasu ɓangarorin ci gaban ƙasa.

    Haka nan sabon shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta zamo mai tuntuɓa da neman shawarwari ba wadda za ta rinƙa ƙaƙaba wa mutane abin da ba su so ba.

    Ya ce "Za mu tuntuɓa da tattaunawa amma ba za mu yi ƙarfa-ƙarfa ba."

    A cewarsa zai samar da gwamnati ce wadda za ta wakilci al'umma ba wadda za ta yi mulki kawai ba.

    Shugaban ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ciyar da ƙasa gaba.

  14. Dakta Dikko Umar Radda ya zama sabon gwamnan jihar Katsina

    Dakta Dikko Umar Radda

    Asalin hoton, DIKKO RADDA/FACEBOOK

    An rantsar da Dakta Dikko Umar Radda na jam'iyyar APC a matsayin sabon gwamnan jihar Katsina a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke cikin garin Katsina.

    Babban alkalin jihar Danladi Abubakar shi ne ya rantsar da gwamnan tare da mataimakinsa Faruk Jobe, a bikin da mai barin-gado Aminu Bello Masari da mataimakinsa Mannir Yakubu da sauran manyan baki suka halarta.

    Daga cikin manyan bakin akwai gwamnan jihar Maradi ta Nijar, Abubakar Shuaibu, da kuma tsohon gwamnan jihar ta Katsina Ibrahim Shehu Shema..

    Sabon gwamnan na Katsina shi ne tsohon shugaban hukumar bunkasa kananan da matsakaitan sana'o'i ta Najeriya, SMEDAN.

    Sannan ya kasance tsohon shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Masari, kuma ya shugabanci karamar hukumar Charanchi a jihar ta katsina.

  15. Bidiyon yadda shugaba Buhari ya kama hanyar Daura

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Bayan miƙa mulki ga sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kama hanya domin komawa mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina.

    Muhammadu Buhari ya tafi ne tare da matarsa, Ai'sha Buhari da sauran muƙarrabai.

    Tsohon shugaban ƙasar ya kwashe shekara takwas yana mulki, daga shekara ta 2015 zuwa 2023.

    Dama dai Muhammadu Buhari ya sha bayyana cewa zai koma mahaifarsa Daura da zarar ya sauka daga shugabancin ƙasar.

  16. Dandamalin rantsar da Abba Gida-gida ya rufta

    Taron rantsar da Abba kabir Yusuf

    Asalin hoton, Channels

    Dandamalin da aka rantsar da sabon gwamnan jihar Kano Injiniya Abba kabir Yusuf ya rufta a daidai lokacin da ake bikin.

    Lamarin ya faru a lokacin da sabon gwamnan wanda ake wa lakabi da Abba Gida-gida yake kai tare da matimakinsa da kuma mukaddashin babban mai shari'a na jihar wanda ya jagoranci rantsar da sabon gwamnan da mataimakin nasa, sai dai babu wanda ya ji rauni a cikinsu.

    Sabon gwamnan yana shirin barin dandamalin ne bayan rantsar da shi sai kawai ya fufta inda nan da nan jami'an tsaronsa suka kakkare shi ciki har da kwamishinan ƴan sanda na jihar Ahmad Gumel.

    An katse bikin ta yadda sabon gwamnan bai iya duba faretin masu kayan sarki ba, saboda cincirundon magoya baya da suka yi wa filin wasa na Sani Abacha cikar-kwari ciki da waje.

  17. Inuwa Yahaya ya fara aiki a Gombe a wa'adin mulkinsa na ƙarshe

    ..

    Asalin hoton, OTHERS

    Inuwa Yahaya ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin Gwamnar jihar Gombe, a yau Litinin.

    Gwamna Yahaya ya lashe zaben gwamna karo na biyu ne bayan takara tsakaninsa da jam'iyyun adawa.

    Shi ma mataimakin gwamnan jihar Gombe, Dr Manassah Daniel Jatau ya sha rantsuwa.

    ...

    Asalin hoton, OTHERS

    Inuwa Yahaya ya zama gwana a karo na biyu
  18. Hotunan yadda Tinubu ya sha rantsuwar kama aiki

    ...
    ...
    ...
    ..
  19. An rantsar da Siminialayi Fubara a matsayin gwamnan jihar Rivers

    An rantsar da Siminialayi Fubara a matsayin gwamna da Farfesa Ngozi Nma Odu a matsayin mataimakiyar gwamna a jihar Rivers.

    An gudanar da bikin rantsarwar a filin wasa na Yakubu Godwin cikin ruwan sama kamar mai karfi.

    Babban alkalin jihar, Mai shari’a Simeon Amadi ne ya rantsar da su.

    Siminialayi Fubara ya karbi mulki daga hannun Nyesom Wike a matsayin zababben gwamnan jihar Rivers na hudu tun 1999.

    Tsofaffin Gwamnonin Jihar Rivers tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a 1999 sun hada da:

    Dr Peter Odili: 1999 zuwa 2007

    Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi: 2007 zuwa 2015

    Nyesom Wike: 2015 zuwa 2023

  20. Dauda Lawal ya zama sabon gwamna a Zamfara

    Zamfar Gov

    Asalin hoton, Abdul Balarabe

    Dauda Lawal ya zama sabon gwamnan jihar Zamfara bayan ya sha rantsuwar kama aiki a Gusau babban birnin jihar.

    Ya karbi mulki daga wurin tsohon gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle.

    An yi bikin ne a filin baje koli da ke Gusau, a birnin jihar Zamfara.

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamna Dauda ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi.

    ....

    Asalin hoton, OTHER

    Shi ma mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mallam Mani Muni ya sha rantsuwa.

    Sabon gwamnan zai soma aiki ne a yayin da jihar ke fama da matsalar tsaro ta 'yan bindiga wadanda ke kashe mutane tare da sace wadansu domin karbar kudin fansha.