An yi kuskure a lissafin kuɗin makaman da Amurka ta aika wa Ukraine
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ba ta kiyasta kudin alburusai da makamai masu linzami da ma sauran kayan yakin da aka aika Ukraine daidai ba tana mai cewa sun kai na biliyoyin daloli.
Ta ce an samu kuskuren hakan ne saboda ma'aikatar ta kimanta tsoffin makaman da aka dauko a dakin ajiya a matsayin sabbi.
Kuskuren da aka samu zai bai wa gwamnatin Amurka damar kara aikewa da wasu makaman ba tare da bukatar karin wasu kudade daga majalisar dokokin kasar ba.
Amurka dai ta aike da makaman da kudinsu suka kai na fiye da dala biliyan 21 ga Ukraine tun shekarar 2021.