Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Asabar - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.
Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Asabar - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni masu daga Sudan na cewa tsananin faɗa ya sake ritsawa da fararen-hula a yankin Darfur.
Wata mai magana da yawun hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Norway Matilde Vu, ta bayyana birnin El Geneina a matsayin wuri mafi muni da haɗari, tana mai cewa akwai ƙarancin kula da mazauna yankin.
Ta ce akwai ɗaruruwan mutane da aka ƙona wa muhallansu a gaban su lamarin da ya jefa su cikin matsanancin tashin hankali da fargaba.
Sudan dai ta faɗa kazamin rikici sakamakon faɗan da ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da kuma dakarun RSF.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta ce sama da mutane miliyan ɗaya ne rikicin Sudan ya raba da muhallansu.

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin ƙasashen Larabawa sun yi farin ciki da dawowar shugaban Syria Bashar Al'assad cikinsu a taron da suke gudanarwa a Saudiyya.
Shugaba Bashar Al-Assad ya nemi sabon babin haɗin kai tsakanin ƙasashen a jawabinsa na farko a irin wannan taro tun bayan dakatar da Syria daga kungiyar sama da shekaru 12.
A lokacin buɗe taron, Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman ya yi maraba da dawowar shugaba Assad cikin kungiyar yana mai fatan cewa hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a Syria da yankin baki-ɗaya.
An dakatar da ƙasar Syria daga kungiyar ƙasashen Larabawa ne domin mayar da martani ga murkushe masu zanga-zangar neman dimokraɗiyya a farkon yakin basasar da aka kashe dubban mutane.

Asalin hoton, PA Media
Bayan zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane uku bisa alaƙa da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka gudanar a Iran, ƴan ƙasar da ke zama a Birtaniya sun taru a gaban ofishin Firaministan ƙasar da ke tsakiyar birnin Landan, inda suke son a dakatar da batun zartas da irin hukuncin a Iran.
Masu zanga-zangar riƙe da alluna, sun buƙaci gwamnatin Birtaniya da ta duba batun ƴancin ƴan Iran wajen ganin an yi watsi da ɗabi'ar zartas da hukuncin kisa.

Asalin hoton, Lagos Police
Hukumomi a Najeriya sun tsawaita tsare mawakin nan mai suna Seun Kuti, ɗa ga Fela Kuti, da karin kwanaki huɗu. Za a ci gaba da tsare shi har zuwa ranar 22 ga Mayu.
An kama shi ne a ranar Litinin da ta gabata bisa zarginsa da cin zarafin wani ɗan sanda.
Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ne ya bayar da umarnin a tsare shi a ranar Asabar, amma mista Kuti ya yanke shawarar miƙa kansa a farkon makon nan.
Kakakin ‘yan sandan ya ce an Kuti, mai shekaru 40 a cikin wani bidiyo yana cin zarafin ɗan sanda sanye da kaki.
Kafin kama shi, Kuti ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ɗan sandan ya yi yunkurin kashe shi da iyalansa, amma bai bayyana yadda aka yi ba.
Mawakin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zai ba da "cikakken haɗin kai" ga duk wani bincike da za a gudanar kansa.

Asalin hoton, Nigeria Police Force/Twitter
Yan sanda a Kano sun ce sun kama wata mata mai shekara 35 da ake zargi da daba wa wata yarinya wuƙa a karamar hukumar Kumbotso na jihar.
Cikin wata sanarwa da kakakin ƴan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce matar mai suna Fatima ta ɗauki yarinyar ce zuwa wani gida da ba a kammala ginawa ba, inda ta daba mata wuƙa a wuya da ciki sannan ta gudu ta bar ta a wurin.
Kiyawa ya ce an kuma kama mijin matar, inda ya yi iƙirarin cewa tana da matsalar kwakwalwa tare da cewa bai san wajen da take ba, inda daga bisani kuma aka cafke ta a ranar Alhamis a maɓoyarta a kauyen Dungulmi a karamar hukumar Dutse na jihar Jigawa.
Ya zuwa yanzu dai ƴan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a ranar Lahadi 14 ga watan Afrilun, 2023.
Matar da ake zargi dai ta amsa aikata laifin da ake tuhumarta da shi, inda ta ƙara da cewa ta daba wa yarinyar wuƙa ne don ramuwa, saboda a cewarta mahaifin yarinyar yana bai wa mijinta shawarar cewa ya ƙara aure.

Asalin hoton, Getty Images
Mai shari`a, Mohammed Yunusa na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, ya soke takarar zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti da ɗaukacin `yan takarar jam`iyyar Labour a jihohin Abia da Kano.
Kotun ta yanke hukuncin cewa fitowar su ba ta dace da tanadin dokar zaɓe ta 2022 ba.
An miƙa kwafin hukuncin da kotun ta yanke ga menema labarai a ranar juma`a.
A ƙarar da mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar kan jam`iyyar Labour da kuma hukumar zaɓe ta INEC, kotun ta ce jam`iyyar Labour ta kasa miƙa rajistar zaman mambobinta ga hukumar ta INEC cikin kwanaki 30 kafin zaɓukan fidda gwani, abu kuma da ya sa tsarin ya zama mara inganci.
Ya ce jam`iyyar ba ta bi tanade-tanaden dokar zaɓe ba, ba za a iya cewa tana da ɗan takara a zaɓe ba, kuma ba za a iya bayyana wanda ya lashe zaɓe ba.
Don haka ya bayyana cewa kuri`un da aka bai wa Alex Otti ba su da amfani.

Asalin hoton, Gwamnatin Najeriya/Twitter
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin sabuwar Akanta Janar ta ƙasa.
Wannan na kunshe ne cikin wata wasikar da shugabar ma'aikata ta tarayya Dakta Folasade Yemi-Esin ta fitar a ranar Juma'a a Abuja.
Ta ce Buhari ya amince da naɗin na take.
Ms Oluwatoyin Sakirat ta fito ne daga karamar hukumar Ikenne na jihar Ogun, an kuma haifeta a ranar bakwai ga watan Maris ɗin 1965.
Kafin naɗinta, ta kasance darektar kuɗi a ofishin shugabar ma'aikata ta tarayya.
Oluwatoyin za ta karɓi ragama daga tsohon Akanta Janar Ahmed Idris wanda shugaba Buhari ya kora bisa zargin sa da sata da kuma zamba-cikin-aminci ta kimanin Naira biliyan 109.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce wasu mutane da ake zargin mayaƙa sun kashe wani injiniya da ma'aikata uku a gandun dajin Virunga da ke ƙasar.
Cibiyar kula da gandun dajin a Kongo ta ce wasu mutane ɗauke da bindigogi, waɗanda ake kyautata zaton cewa mayaƙan Mai Mai ne, sun far wa ayarin motocin ma'aikatanta a safiyar ranar Talata.
Gandun dajin Virunga ya kasance daɗaɗɗe a Afirka, inda ake samun na'uin dabbobi daban-daban kamar su gwaggon biri da sauransu.
Ya kuma kasance wurin maɓoyar mayaƙan Mai Mai.
Ƴan bindiga sun ɗauki tsawon gwamman shekaru suna addabar yankin gabashin Kongo.

Asalin hoton, Aisha Buhari/Twitter
Mai ɗakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce a ganinta babu buƙatar shugabannin Najeriya su fita waje don neman lafiya bayan kaddamar da kaddamar da asibitin fadar shugaban ƙasa wanda ya laƙume kuɗi naira biliyan 21.
Aisha Buhari ta bayyana haka ne lokacin da bi sahun shugaba Muhammadu Buhari da sauran muƙarabban gwamnati wajen kaddamar da asibitin da ke cikin fadar shugaban ƙasa a Abuja a ranar Juma'a.
Matar shugaban ƙasar Najeriyar ta faɗa wa manema labarai cewa ta bijiro da batun ganin an samar da asibitin ne shekara shida da suka gabata, bayan ɗaukar tsawon lokaci da mijinta ya yi a waje domin neman lafiya.
Ta tabbatar da cewa ganin an samar da asibitin a yanzu, shugabannin ƙasar da iyalansu ba sa buƙatar fita waje neman lafiya, sai dai su kawo ƙwararrun likitoci domin taimaka wa takwarorinsu na ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Babban hafsan sojojin Sudan Laftanar-Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kori mataimakinsa kuma kwamandan dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti.
Dukkanin Janar Burhan da Hemedti sun yi aiki a matsayin shugaba da mataimakin majalisar mulkin soji, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban 2021.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Janar Burhan ya naɗa tsohon madugun 'yan tawaye Malik Agar a matsayin mataimakinsa.
Mista Agar memba ne na Majalisar mulkin sojin ƙasar.
Ya umurci sakatariyar majalisar mulki da hukumomin jihar da su gaggauta aiwatar da wannan umarni.
A watan da ya gabata ne hafsan sojojin ya rusa dakarun RSF tare da ayyana mayakan a matsayin ‘yan tawaye bayan da aka gwabza faɗa tsakanin dakarun da ke gaba da juna.
Tuni dai ƙasar ta faɗa cikin tashin hankali da ya janyo mutuwar mutane da dama da kuma raba da yawa da muhallansu.

Asalin hoton, other
Gwamnati jihar Assam ta kaddamar da wani kwamitin kwararru mai mambobi huɗu a karkashin shugabancin wani tsohon alkali domin ɗaukan matakin haramta auren mace fiye da ɗaya.
Kwamitin kwararrun zai yi nazari ko majalisar dokokin jihar na da ‘yancin haramta irin wanna auren ko a'a.
A cewar gwamnatin jihar ta Assam, ta ce kwamitin zai fitar da rahoto kan lamarin bayan watanni shida.
Sanarwar da ministan jihar ya fitar ta tayar wa Musulmi ‘yan asalin Bengal da ke zama a yankin hankali.
Gwamnatin Assam, gwamnati ce ta jihar Assam a ƙasar Indiya.
Ta na da gwamna wanda shugaban ƙasar indiya ke naɗa wa, kuma a halin yanzu shi ne Gulab Chand Kataria.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine, ya kai ziyarar ba-zata a taron ƙasashen Larabawa wanda ke gudana a Saudiyya
Hakan na zuwa ne kafin batun tafiyarsa zuwa Japan inda ƙasashe Masu Karfin Tattalin Arziki suke gudanar da babban taronsu.
Wannan na cikin yunƙurin Ukraine na neman goyon bayanta daga ƙasashe musamman waɗanda ke ƙawance da Rasha.
Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa Syria ce kawai ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga mamayar Rasha, kuma wannan ne lokaci da na farko da Shugaba Bashar al-Assad ke halarar taron tun bayan da aka kori Syria daga kungiyar shekaru 12 da suka gabata.
Ƙarfin ikon da Saudiyya ke da shi a gabas ta tsakiya ya yi tasiri a mamayen da Rasha ke yi a Ukraine.
Saudiyya dai ta soki matakin ƙasashen yamma na ƙaƙaba wa Rasha takunkumi duk da cewa tana ɗasawa da ƙasashen.

An kai wata dattijiya ƴar Australia mai ciwon mantuwa asibiti a cikin mawuyacin hali bayan ƴan sanda sun ɗosana mata na’ura mai amfani da wutar lantarki da ya sa rayuwarta cikin hadari.
An kira ƴan sanda ne zuwa wani gidan kula da gajiyayyu bayan sun sami labarin cewa wata mata mai shekara 95, mai suna Claire Nowland na ɗauke da wuka irin ta cin abinci.
Ƴan sanda biyu tare da ma’aikatan gidan sun yi yunƙurin kwantar wa matar da hankali, inda a dalilin haka ne suka jona mata na'urar mai 'shokin' har sau biyu.
An jogana mata na'urar ce a gadon bayanta da kuma ƙirji, a inda kanta ya fashe kuma jini ya taru mata a kwakwalwa sakamakon faduwar da ta yi.
Iyalinta sun shaida wa BBC cewa tana cikin mawuyacin hali kuma ba a sa ran cewa za ta rayu.
Lamarin ya janyo ɓarkewar zanga-zangar tir da matakin, wanda ake ganin bai dace ba.
Shugabar ƴan sanda ta New South Wales ta ce ta fahimci yadda mutane ke ji a zukatansu kuma ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.

Asalin hoton, OTHER
Wani Mutum mai shekaru 40 ya kutsa a guje ta ɗaya daga cikin manyan ƙofofin shiga fadar Vatican a cikin wata mota sai dai an kama shi a lokacin da ya ci karo da shingen bincike.
Wannan lamari ya faru ne a ƙofar Santa Ana da kimanin karfe takwas na safiyar yau.
Rahotanni sun ce masu gadin sun yi yunƙurin hana mutumin shiga, daga nan ne ya ja baya sannan ya dawo ya afka cikin shingen binciken.
Sanarwar da fadar Vatican ta fitar ta ce, a kokarin tsayar da motar, masu gadin sun harbi gaban motar.
An kai mutumin asibiti domin samun kulawa sai dai bayanai sun ce yana cikin 'mummunan yanayi na tabun hankali'.

Hukumomi a Iran sun zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane uku bisa alaƙa da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka gudanar a ƙasar a bara, kamar yadda ma`aikatar shari`a ta ƙasar ta bayyana.
An yanke wa mutanen uku hukuncin ne bisa zarginsu da hannu a harin da ya kashe jami`an tsaro uku a Isfahan, a watan Nuwamba.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty international ta ce an yi musu shari`a ba bisa ƙa`ida ba tare da zargin an azabtar da su.
An rataye wasu ƴan zanga-zangar huɗu tun watan Disamba.
An bayar da rahoton cewa an yanke wa wasu da dama hukuncin kisa ko kuma an tuhume su da aikata manyan laifuka.
Zanga-zangar dai ta mamaye duk faɗin jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan mutuwar wata mata baƙurɗiya mai shekaru 22, Mahsa Amini, a hannun ƴan sanda bayan zargin ta da sanya hijabi ba daidai ba.
Mutanen uku da aka zartar wa hukunci a ranar juma`a- Majid Kazemi mai shekaru 30, da Saleh Mirhashemi mai shekaru 36, da kuma Saeed Yaqoubi mai shekaru 37- an kama su ne bayan zanga-zangar da aka yi a tsakiyar birnin Isfahan a ranar 16 ga watan Nuwamba, inda aka harbe wasu jami`an rundunar `yan sandan farin kaya ta Basij guda biyu tare da wani ɗan sanda.
Majiyoyi sun shaida ma ƙungiyar kare haƙƙin bil`adama cewa an tilasta wa mutanen amsa laifinsu ne, sannan aka azabtar da su tare da tilasta musu yin kalaman ɓatanci waɗanda suka zama tushen laifukan da ake tuhumarsu da su .
An yi zargin cewa masu yi musu tambayoyi sun ajiye Kazemi a kife, suka nuna masa faifan bidiyo na yadda suke azabtar da dan uwansa, inda suka yi masa kisan gilla tare da yi masa barazanar kashe sauran `yan uwansa.

Asalin hoton, Getty Images
Mayakan Boko haram guda 511 da iyalansu sun miƙa wuya bayan farmakin baya-bayan nan da sojojin Najeriya suka kai a yankin arewa maso gabashin kasar.
Mayakan sun hada da maza 99 da mata 161 da kuma kananan yara 251, kuma sun mika wuya ne a bangarori daban-daban da ke yankin.
Wannan bayanin na kunshe ne a wata sanarwa da daraktan yada labarai na cibiyar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Musa Danmadami ya fitar a ranar Alhamis.
"Dakarunmu sun kuma yi nasarar ceto wata daga cikin ‘yar makarantar mata ta Chibok a inda adadin mayakan boko haram da ISWAP guda 511 su ka mika wuya tare da iyalen su da su ka hada da maza 99 da mata 161 da kuma kananan yara 251, kuma sun mika wuya ne a bangarori daban-daban da ke yankin” a cewar sanarwar.
Ya ce a wani farmaki da aka kai, "sojoji sun kashe mayakan boko haram da na ISWAP guda 26, suka kama masu taimaka musu guda 25, da kuma wani mai leken asiri."

Asalin hoton, Getty Images
Dubun dubatar `yan Sudan da suka tsere daga fadan ƙasar sun maƙale a garin Halfa da ke arewacin ƙasar, suna jiran tsallakawa zuwa makwabciyar ƙasar Masar, a cewar wata tashar rediyo.
Tashar ta ce motocin bas 30 dauke da `yan gudun hijira na isa Halfa a kullum daga sassa daban-daban na ƙasar Sudan.
Ta kara da cewa yanzu haka, `yan gudun hijirar sun zarce yawan mazaunan garin.
Gidan rediyon ya ce "dubban mutane" na taruwa a gaban karamin ofishin jakadancin Masar a kullum, suna fatan a ba su takardar biza, wadda akwan kwashe makwanni kafin a samu.
Mutane da yawa da ba su iya samun biza a Halfa ba sun zaɓi zuwa Port Sudan don neman bizar a ofishin jakadancin Masar da ke can.
Rediyo Dabanga ya bayyana cewa garuruwan Sudan da dama na fuskantar ƙaruwar marasa lafiya sakamakon karancin kayan masarufi.

Asalin hoton, TWITTER/@PoliceNG
Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Anambra ta ce ta samu nasarar ceto mutum biyu waɗanda aka sace a harin da aka kai kan tawagar ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, a jihar Anambra.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar, Ikenga Tochukwu ya ce an ceto mutanen biyu ba tare da wata jikkata ba.
Sai dai bai bayyana sunayen waɗanda aka ceto ɗin ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin domin samun cikakken bayani.
A ranar Talata ne wasu ƴan bindiga suka yi wa kwambar motocin da ke ɗauke da ma’aikatan kwantar-ɓauna, inda suka kashe mutum bakwai, ciki har da ma’aikata uku.
Maharan sun kuma tafi da wasu daga cikin ma’aikatan sannan suka ƙona motocin.