Masar ta kafa sharuɗɗan kwashe ɗaliban Najeriya ta ƙasarta

Wannan shafi ne da zai riƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ma'assalam!

    Masu bibiyarmu a wannan shafin namu na Kai Tsaye da yake kawo muku rahotanni daga Najeriya da maƙwabtan ƙasashe da ma sauran sassan duniya, a nan za mu dakata a yau.

    Idan Allah Ya kai mu, za mu sake dawowa gobe Talata domin ci gaba da kawo muku wasu rahotannin.

    Nabeela Mukhtar Uba, amadadin abokin aiki - Haruna Ibrahim Kakangi nake cewa mu kwana lafiya.

  2. An raunata ƴan sandan Faransa fiye da 100 a gangamin ranar ma'aikata

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar cikin gida a Faransa ta ce kimanin ƴan sanda 108 ne suka jikkata sanadin arangamar da ta kaure a sassan ƙasar inda masu zanga-zanga ke nuna fushinsu kan sauye-sauyen da aka yi wa tsarin pensho.

    Gerald Darmanin ya ce ba kasafai aka cika samun irin haka ba - ƴan sanda da dama su ji rauni. Ya ƙara da cewa an kama mutum 291 yayin tashin hankalin.

    Dubban jama'ar ƙasar ne suka shiga gangamin ranar Ma'aikata domin nuna adawarsu da sauye sauyen da Shugaba Emmanuel Macron ya yi.

    Akasarin gangamin an yi shi lami lafiya amma an samu wasu masu tsatsauran ra'ayi da suka riƙa wasan wuta. Ƴan sanda kuma sun mayar da martani ta hanyar wulla hayaƙi mai sa hawaye da yi musu feshin ruwa.

    Zuwa yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka ji rauni ba.

    Wannan ne gangami na baya-bayan nan da aka yi kan ɗaga shekarun fara karɓar pensho daga 62 zuwa 64. Ƙungiyoyin ƙwadago na son a janye matakin.

  3. NAFDAC na gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron rahoton Khalifa Shehu Dokaji

    Hukumar kula da ingancin abinci a Najeriya, ta NAFDAC, ta ce tana gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie da ƙasashen Taiwan da Malaysia ke samarwa, bayan gano sinadarin Ethylene Oxide da ke haddasa cutar kansa a cikin ta.

    Shugabar hukumar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta ce kawo yanzu jami’an hukumar da ke kula da dakin gwajegwajen na ingancin abinci sun dukufa wajen bin matakai na faɗaɗa bincike kan sinadarin.

  4. Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Morocco

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyoyin ƙwadago daban-daban a Morocco sun gudanar da gangamin ranar Ma'aikata a birnin Rabat domin nuna adawa da tsadar rayuwa.

    Hauhawar farashin kayayyaki a Morocco ta janyo ƙarin farashin kayan masarufi.

    Ɗaruruwan ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga zanga-zangar lumanar da aka yi a tsakiyar babban birnin ƙasar.

    Masu gangamin sun yi ta rera waƙoƙi kan nuna fushinsu ga tsadar kayayyaki, wasu kuma na neman a hamɓarar da gwamnati.

    Wasu masu zanga-zangar sun yi kira ga Firaminista Aziz Akhannouch da ya yi murabus.

  5. 'Ba mu da tabbacin abin da zai faru da mu idan muka isa Port Sudan'

  6. 'An kashe mutane fiye da 500 a Kudancin Kaduna cikin shekara 6'

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ƙungiyar ci gaban al'ummar Atyap a jihar Kaduna, Mista Samuel Achi ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yanzu, an kashe mutum 518 sannan dubbai sun tsere, an kuma ɗaiɗaita ƙauyuka 20 yayin da aka ƙone wasu ƙauyukan 18 a Kudancin Kaduna.

    Shugaban ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a yau a Samaru Kataf. Ya ce vhare-haren da ake ci gaba da kai wa sun yi kamanceceniya da waɗanda aka kai a 2019 kuma wasu ɓatagari ne suke kai wa waɗanda kuma ya kamata a ce hukumomin tsaro sun hukunta su.

    Jaridar Punch ta rawaito Mista Achi na "kira ga al'ummarmu da su kare kansu daga duk wasu hare-hare," in ji shi inda ya ce an kai maƙura.

    Da yake kokawa kan zargin da ake cewa sojoji na da hannu, Mista Achi ya ce sojojin da aka tanada domin tabbatar da tsaro a yankin, ba sa yin wani abu na kawo sauƙi.

  7. An yi zanga-zangar neman karin albashi a Iraki

    ...

    Asalin hoton, OTHER

    Dubban ma'aikatan gwamnati a kasar Iraki sun gudanar da zanga-zanga a brinin Baghdad domin neman karin albashi daga gwamnatin kasar.

    Wani mamba a kwamitin shirye-shiryen zanga-zangar a birnin Bagadaza, Mustafa Al-Zorfi ya bayyana wa BBC cewa, zanga-zangar ta yau an gudanar da ita ne domin a tunzura majalisar ministocin kasar.

    Ta kada kuri'a kan shawarar da kwamitin da a ka kaddamar a bara ya bayar na a yi wa ma'aikata karin albashi.

    Al Zorfi ya ce, gwamnati ta yi alkawarin kaɗa ƙuri'a kan dokar ƙarin albashin a zaman da za ta yi gobe Talata.

    Ya kara da cewa za su dauki wadansu matakai da su ka hada da yajin aiki idan har gwamnati ba ta kaɗa ƙuri'a kan dokar ba.

  8. Ana ci gaba da luguden wuta a birnin Khartoum

  9. Zan biya ma'aikata isasshen albashi - Tinubu

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU

    Bayanan hoto, Bola Ahmed Tinubu

    Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin biyan ma'aikatan ƙasar albashin da zai ba su damar yin rayuwa ta mutunci da biyan buƙatun iyalansu.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na tuwita domin murnan Ranar ma'aikata ta duniya, Tinubu ya yi iƙirarin cewa zai haɗa hannu da ma'aikatan ƙasar domin a yaƙi talauci da rashin haɗin kai da banbance-banbancen addini a al'umma domin tabbatar da ci gaban Najeriya baki daya.

    Ya yi bayanin cewa inganta rayuwan ma'aikata na ɗaya daga cikin muhimman alƙawuran da ya yi yayin da yake yaƙin neman zaɓe kuma ya bayar da tabbacin ɗaukar matakai domin ganin ya cika wannan alƙawari.

    Tinubu ya nemi haɗin kan ɗaukacin 'yan najeriya,domin a cewar sa dole ne a ɗauki tsauraran matakai domin a tabbatar ma'aikatan Najeriya sun sami ƙarin walwala.

  10. Masar ta gindaya sharuɗɗan kwashe ɗaliban Najeriya ta cikinta

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/ABIKE DEBIRI

    Masar ta ce za ta yarda a kwashe ɗaliban Najeriya da ke tsere wa faɗan da ake yi a Sudan ta ƙasarta ne kawai idan Najeriyar ta cika wasu tsauraran sharuɗɗa.

    Jakadan Najeriya a Masar, Nura Abba Rimi ne ya tabbatar wa BBC da wannan bayanin.

    Najeriya dai na da ɗalibai sama da 500 waɗanda suka maƙale a bakin iyakar ƙasar ta Masar, suna jiran izinin shiga domin kwashe su zuwa gida.

    A baya ƙasar Habasha ta hana ɗaliban Najeriya bi ta ƙasarta domin tsere wa faɗan na Sudan, wani abu da ya janyo suka daga ɓangarori da dama.

    Ambasada Nura Abba Rimi ya ce sharuɗɗan da ƙasar ta Masar ta gindaya su ne:

    • Dole sai Najeriya ta bayyana tsarin da ta yi na jiragen da za su sauka a ƙasar domin kwashe ɗaliban.
    • Girman jiragen saman da za su yi jigilar.
    • Tabbatar da cewa za a zarce da ɗaliban kai-tsaye daga bakin iyakar ƙasar zuwa filin jirgi da aka yarje
    • Cikakken jerin sunayen mutanen da za a kwashe ta ƙasar da kuma lambar fasfo ɗinsu na tafiye-tafiye.
    • Cikakkun takardun tafiya.
    • Kasancewar jami'an gwamnatin Najeriya a wuraren kwashe ɗaliban.
    • Da kuma motocin safa da za su kwashi ɗaliban daga bakin iyaka zuwa filin jiragen sama.

    ƙasashen duniya dai na ci gaba da rige-rigen ganin sun kwashe ƴan ƙasarsu daga Sudan, bayan ɓallewar faɗa tsakanin dakaru masu mubaya'a ga manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu.

  11. Wani jirgin ƙasa na dakon mai ya yi haɗari a Rasha

    ..

    Asalin hoton, TWITTER

    Gwamnan yankin Bryansk, Alexander Bogomaz ya ce wani abin fashewa ya tashi a kan titin jirgin ƙasa na Bryansk zuwa Unecha, mai tazarar kilomita 60 daga Ukraine.

    Lamarin wanda ya faru da kimanin ƙarfe goma na safe, agogon Moscow, ya sanya taragan jirgin dakon man guda bakwai sun kauce daga kan hanya, in ji Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Rasha.

    Yankin wanda ke makwabtaka da ƙasashen Ukraine da Belarus yana fuskantar ayyukan zagon kasa tun bayan da Rasha ta fara mamaye a Ukraine.

    Rahotanni sun ce jirgin na dauke da kayan albarkatun mai da katako. Ba a samu rahoton jikkata ba.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda taragan da ke ɗauke da mai suka faɗi a rigingine, inda hayaƙi da toka suka turnuƙe.

  12. Masar ta hana ɗaliban Najeriya daga Sudan shiga ƙasarta

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/NIDCOM_GOV

    Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen ƙetare ta ce hukumomin Masar sun ƙi buɗe kan iyakarsu ga ɗaliban Najeriya waɗanda ke guje wa rikicin da ke faruwa a Sudan.

    Sai dai hukumar ta ce yanzu haka akwai jirgin sojin Najeriya da ke girke a birnin Aswan, kuma a cewar ta, jirgin ba zai baro birnin ba sai ya ɗauki ɗaliban na Najeriya.

    Har yanzu dai Najeriya na fafutikar ganin yadda za ta iya kwaso dubban ɗalibai da sauran al’ummarta daga Sudan inda faɗa ya ɓarke a makon jiya.

    Bayanai na cewa wasu ɗaliban na kan hanyarsu ta zuwa kan iyakar Sudan da Saudiyya, inda ake sa ran za su tsallaka zuwa cikin ƙasar kafin a kwashe su zuwa gida.

    Faɗa ya ɓarke ne tsakanin ɓangarorin dakaru masu biyayya da manyan jami’an sojin Sudan biyu.

    Tuni ƙasashe da dama suka kwashe al’ummarsu domin gudun kada yaƙin ya rutsa da su.

  13. Ba za mu janye sababbin kuɗi daga hannun mutane ba – CBN

    Sababbin takardun kuɗin Naira

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Bayanan hoto, Sababbin takardun kuɗin Naira

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa bankin na ƙoƙarin yanke shawarar janye sababbin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da 1,000.

    A wata sanarwa da bankin ya fitar ta hannun mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labarunsa, AbdulMumin Isa, bankin ya bayyana raɗe-raɗin a matsayin ‘maras tushe.’

    Bankin ya ce a halin yanzu za a ci gaba da amfani da tsofaffi da sababbin kuɗaɗen kamar yadda suke.

    Haka nan ya ƙara da cewa bankin na ci gaba da karɓar takardun sababbin kuɗaɗen daga kamfanin buga takardun kuɗi na ƙasar.

    Ya ce kamar yadda aka sanar a baya za a ci gaba da amfani da kuɗin har zuwa 31 ga watan Disamba, lokacin da za a janye su daga hannun al’umma.

  14. Ma'aikatan Najeriya sun shiga tasku lokacin mulkin Buhari - NLC

  15. Turkiyya ta kashe 'shugaban IS'

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya ce sojojin leƙen asiri na Turkiyya sun gano tare da kashe shugaban IS, Abu Hussein Al-Qurashi.

    A wata hira a kafar yaɗa labaru mallakar gwamnatin Turkiyya Mr. Erdogan ya ce an kashe Al Qurashi ne a Syria ranar Asabar kuma ya ce sojojin leƙen asirin na Turkiyya sun jima suna farautar sa.

    Rahotanni sun ambato majoyiyin tsaro na Syria na cewa sojojin Turkiyya sun kai samame a garin Jandaris da ke arewacin ƙasar a daren Asabar inda aka riƙa jin ƙarar fashewar abubuwa.

    Bayan wannan bayanin dai Erdogan bai yi ƙarin haske kan kisan ba, sannan babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da mutuwar Al-qurashi.

  16. Rasha ta yi ruwan wuta kan Ukraine da asuba

    ...

    Asalin hoton, SERHIY LYSAK

    A karo na biyu cikin kwana uku, dakarun Rasha sun ƙaddamar da hari kan yankunan ƙasar Ukraine da sanyin asubahi.

    Mutum ɗaya ya mutu a Kherson sanadiyyar harin yayin da mutum 25, ciki har da yara suka samu raunuka a birnin Dnipropetrovsk.

    Dakarun Ukraine sun ce shingen kariyar ƙasar ya kaɓo 15 daga cikin makaman roka da Rasha ta harbo.

    Ɗaya daga cikin manyan wuraren da aka yi niyyar kai wa harin shi ne birnin Pavlohrad da ke kusa da Dnipro – wani jami’in Rasha ya ce harin ya faɗa kan wata cibiyar kai hare-hare ta Ukraine.