Ƙasashe suna rububin kwashe mutanensu daga Sudan
An kwashe ƙarin jami'ai da ma'aikatan jakadancin ƙasashen duniya da dama daga Khartoum, babban birnin Sudan, a yayin da sojojin gwamnati da dakaru masu kayan sari na RSF ke ci gaba da gwabza yaƙi.
Faransa da Jamus da Kanada da Sifaniya da kuma Italiya na cikin ƙasashen baya-bayan nan da suka sanar da cewa sun kai jami'an nasu tudun-mun-tsira.
Sai dai kuma sauran fararen hula na ƙasashe, sun ce suna fuskantar wahala a yunƙuri da suke yi na fita daga Sudan.
Wakilin BBC ya ruwaito cewa a bayyane take abu ne mai matuƙar wahala ƙasashe su iya tsarawa tare da kwashe mutanensu a cikin motoci saboda ana faɗa ne a tsakiyar babban birnin ƙasar.
Ana ta samun kirare-kirayen neman agajin gaggawa daga ɗalibai waɗanda akasarinsu 'yan ƙasashen Afirka da Asiya ne da kuma Gabas ta Tsakiya.