China na ci gaba da holen makaman yaƙi a kusa da Taiwan
A rana ta uku a jere, sojin China na holen manyan makaman yaki yayin da suke ci gaba da atisayen soji a kusa Taiwan.
Aikin da a fakaice suka kira 'Operation Joint Sword', na gwajin yadda za a kai hare-hare ta sama da ka iya fadawa Taiwan.
Bayanai sun ce duk wasu alamu na girke soji sun tabbata a kusa da Taiwan, kama daga makaman roka da ke cin dogon zango, makaman lalata makamai masu linzami da sauransu sun nuna take-taken China a yankin.
China ta fara atisayen soji a kusa da Taiwan, sa'o;i kadan da dawowar shugabar Taiwan Tsai Ing-wen, daga ziyarar da ta kai Amuika da kuma ganawa da kakakin majlisa Kevin McCarthy.