Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan sanda na neman amaryar da ta yi harbi da bindiga lokacin bikinta

Wannan shafi ne da zai rinƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Girke-girken Ramadan: Yadda ake yin "cilantro soup"

  3. Buhari zai tafi Saudiyya a ziyararsa ta karshe a matsayin shugaban ƙasa

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Saudiyya ranar Talata a wata ziyara ta karshe da zai kai wata ƙasar waje a matsayin shugaban ƙasa.

    Shugaban zai shafe kusan mako guda daga ranar 11 ga watan Afrilu zuwa 19 ga wata.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar, ta ce Muhammadu Buhari zai kuma gudanar da aikin Umrah yayin ziyarar tasa.

    Sanarwar Mallam Garba Shehu ta kuma ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan mukarraban gwamnatinsa a wannan ziyara zuwa Saudiyya.

  4. Ana ci gaba da zanga-zanga a Habasha kan yunkurin soke dakarun yankin Amhara

    Zanga-zanga ta ɓarke a yankin Amhara na ƙasar Habasha a rana ta biyar a jere kan nuna adawa da yunkurin gwamnati na soke dakaru na musamman a yankin.

    Masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi ta hanyar saka duwatsu, inda suka yi ta ƙona tayoyi domin hana sojoji wuce wa.

    Masu zanga-zangar na tsoron cewa matakin gwamnatin ƙasar zai janyo a riƙa kai musu hare-hare daga wajen makwaɓta.

    Yawancin larduna a Habasha na da dakaru na musamman da ke kula da iyakokinsu da kuma faɗa da ƴan tawaye.

    A makon da ya gabata ne, gwamnati ta sanar da cewa tana son haɗe dakarun na musamman zuwa sojojin tarayya ko kuma cikin ƴan sanda domin haɗin-kan kasa.

    Matakin ya janyo gagarumar zanga-zanga a birane da kuma garuruwa da ke faɗin yankin.

    Hakan kuma ya janyo saka dokar takaita zirga-zirga ta takaitaccen lokaci a birnin Gondar mai ɗimbin tarihi, inda aka ruwaito artabu tsakanin masu zanga-zanga da sojoji a garin Kobe, kusa da iyaƙa da yankin Tigray.

    A ranar Lahadi ne firaministan Habasha, Abiy Ahmed ya sha alwashin zartas da matakin da ya ɗauka ko da hakan zai janyo wata matsala.

  5. Bam ya hallaka mutum huɗu a Pakistan

    Akalla mutum hudu ne suka mutu sannan 15 suka jikkata a wani harin bam da aka kai birnin Quetta da ke lardin Balochistan na ƙasar Pakistan.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, harin ya nufi kan wata motar ƴan sanda a kasuwar birnin Quetta wadda ke cike da cunkoso.

    Wani jami'in ɗan sanda mai suna Azfar Mehsar a faɗa wa AFP cewa binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa harin ya faku ne bayan ɗora wani abin fashewa kan wata babur.

    Wasu ƴan sanda biyu na cikin waɗanda harin ya rutsa da su haɗe da wata yarinya ƴar shekara biyar.

    Sai dai babu wata kungiya da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin kawo yanzu.

  6. Abin da ya kamata a rinƙa yi a cikin goman ƙarshe na Ramadana

  7. Korona ta kashe ƙarin mutum 39 a Iran

    Ma'aikatar Lafiya ta ƙasar Iran, ta ce korona ta kashe ƙarin mutum 39 a cikin kwana guda da ya gabata, inda mutum 940 kuma suka kamu da cutar.

    Alkaluman ma'aikatar lafiyar ƙasar sun nuna cewa kimanin mutum 145, 652 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

    Ma'aikatar ta kuma ce ya zuwa yanzu mutum 7,599,828 ne suka kamu da cutar tun bayan ɓarkewar ta, inda ta ce cutar ta fi muni a birane 18 na ƙasar.

  8. Ɗan bindiga ya buɗe wa mutum biyar wuta a Amurka

    Mutum biyar ne suka mutu yayin da wasu guda shida suka jikkata a wani harin bindiga a birnin Louisville da ke jihar Kentucky na Amurka.

    Ƴan sanda sun ce harin ya afku ne a wani banki da ke cikin birnin.

    A wani taron manema labarai da ƴan sanda suka kira bayan afkuwar lamarin, sun ce an ɗauki mutum shida da suka jikkata, ciki har da wani jami'in tsaro, zuwa asibiti don yi musu magani.

    Cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da ɗan bindigar da ya kai harin.

    An umarci jama'a da su ƙauracewa wajen da lamarin ya faru.

    Wani hoton bidiyo da aka ɗauka a yankin, ya nuna jami'an soji kewaye a yankin da aka kai harin.

  9. Birtaniya za ta daina ɗaukan likitoci daga Najeriya

  10. Ƴan sanda na neman amaryar da ta yi harbi da bindiga lokacin bikinta

    Ƴan sanda a jihar Uttar Pradesh da ke Indiya na neman wata amarya wadda ta harba bindiga a lokacin bikin aurenta.

    Wani faifain bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda matar ta yi harbi sau huɗu a sama, lokacin da take zaune a kusa da angonta.

    Ƴan sandan yankin sun ce amaryar ta yi ɓatan-dabo tun bayan faruwar lamarin.

    Harba bindiga lokacin bukukuwan aure domin nuna murna a jihohin arewacin Indiya ba baƙon abu ba ne, sai dai yakan haifar da asarar rayuka a lokuta da dama.

    A shekara ta 2016 wata kotu a jihar ta Uttar Pradesh ta buƙaci a rinƙa yin bincike kan duk wani bikin aure da aka harba bindiga.

    Wani ɗan’uwan amaryar ne ya naɗi bidiyon harba bindigar sannan ya watsa shi a shafin sada zumunta.

  11. China ta kammala atisayen gwajin makamai a kusa da Taiwan

    China ta kammala atisayen da ta kwashe kwana uku tana yi na holen makamai a kusa da Taiwan.

    China ta fara atisayen ne a ranar Asabar bayan shugabar Taiwan, Tsai Ing-wen ta gana da kakakin majalisar wakilan Amurka a California.

    Bayan kammala atisayen, ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce ba za ta daina ƙarfafa ɗamararta ta yaƙi ba.

    Atisayen dai bai kai girman wanda China ta gudanar bayan ziyarar Nancy Pelosi ba a bara.

    Taiwan na ɗaukan kanta a matsayin ƙasa mai zaman kanta, yayin da China ke kallon ta a matsayin wani ɓangare na ƙasarta da ke ƙoƙarin ɓallewa, wanda kuma take ganin za ta iya maido shi ko ta halin ƙaƙa.

    A yau Litinin, China ta sanar cewa ta kammala atisayen makaman nata cikin nasara.

    Taiwan ta ce ta tsinkayi jiragen ruwan yaƙi na China guda 12 da jiragen saman yaƙi 91 a kusa da ita a ranar ta Litinin.

  12. An haramta wa limamai karanta Ƙur’ani daga wayar hannu a lokacin sallolin dare

    Ma’aikatar waƙafi da harkokin addinin Musulunci ta Kuwait ta haramta wa limamai karanta Alƙur’ani daga wayoyinsu na hannu a lokutan nafilfilun dare na watan Ramadana.

    Jaridar Al Rai ta ruwaito cewa bayanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da ta samu sa hannun ƙaramin minista mai kula da harkar masallatai, Salah Al Shilahi.

    Sanarwar ta ƙarfafa wa limamai gwiwa da su riƙa amfani da haddarsu ta Ƙur’ani a lokutan sallolin Tarawihi da Tahajjud, kasancewar su (limaman) misali ne ga sauran al’umma.

    Ta ƙara da cewa ya kamata kowane limami ya yi muraji’ar karatunsa yadda ya kamata gabanin jan sallah a maimakon karantowa daga cikin waya.

  13. Abin da ya kamata a rinƙa yi a cikin goman ƙarshe na Ramadana

    A cikin jerin bayanai da muke kawowa kan azumin Ramadana, Sheik Nuru Khalid ya yi mana bayani kan ayyukan da mai azumi ya kamata ya mayar da hankali a kai yayin da aka shiga kwanaki goma na ƙarshen watan Ramadana.

  14. Ƴan fashi sun halaka sojojin Nijar biyar

    Rahotanni na cewa sojojin Jamhuriyar Nijar guda biyar ne suka rasa ransu a jihar Agadez yayin da suke yi wa ayarin masu haƙar zinare rakiya.

    Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba ne suka kai wa ayarin harin, sannan suka yi awon-gaba da zinaren.

    Shugaban karamar hukumar Arlit, Noura Mallam Sani ya tabbatar wa BBC cewar akwai wasu sojojin da suka samu raunuka baya ga waɗanda suka rasa rayukan nasu.

    Matsalar masu fashi da makami a kan masu haƙar zinare a ƙasar ta Jamhuriyar Nijar dai ta daɗe tana ci wa al'umma tuwo a ƙwarya.

    Sai dai hukumomin ƙasar na cewa suna bakin ƙoƙarin su wajen shawo kanta.

  15. An saki tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa da aka sace

    Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sako tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa a Najeriya, Onje Gye-Wado, bayan sace shi da suka yi a ranar Juma'a.

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar, Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan ga manema labaru a ranar Litinin.

    Nansel ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya kwashe kwana biyu a hannun ƴan bindiga, waɗanda suka sako shi a cikin dare, ranar Lahadi, bayan matsi daga jami'an ƴansanda masu neman inda yake.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai wasu mahara suka yi awon-gaba da Gye-Wado bayan kutsawa cikin gidansa da ke ƙauyen Gwagi a jihar ta Nasarawa.

    Inda daga baya jami'an tsaro suka ce sun bazama domin gano inda ake garkuwa da shi.

  16. Na yi nadamar umurtar ƙaramin yaro ya tsotsi bakina – Dalai Lama

    Jagoran wata ɗarika ta addinin Bhudda, da ke Indiya Dalai Lama ya nemfi afuwa bayan da wani faifan bidiyo ya nuna shi yana tambayar wani yaro ko zai tsotsi harshensa.

    Ofishin Dalai Lama a cikin wani sako ya ce yana son neman afuwar yaron da iyalansa saboda abubuwan da furucin nasa ya haifar.

    Bidiyon dai ya nuna lokacin da Dalai Lama yake sumbatar yaron a baki.

    Ofishin Dalai Lama ya ce “Mai girma yakan so yin wasa da mutanen da ya haɗu da su, koda a bainar jama’a ne kuma ko a gaban masu ɗaukan hoto. Ya yi nadamar abin da ya faru.”

    Bidiyon dai ya janyo tofin-alla-tsine , inda mutane da dama a shafukan sada zumunta suka ce abin bai dace ba.

    Da alama dai lamarin ya faru ne a ɗakin bauta na Dalai Lama da ke birnin Dharamshala na ƙasar Indiya a ranar 28 ga watan Fabarairu, lokacin da Dalai Lama ya gana da wasu ɗalibai 120 waɗanda suka kammala samun horo.

    Gidauniyar da ta shirya samun horon ne ta wallafa hotunan a shafukan sada zumunta, inda a ɗaya daga cikin bidiyon da aka wallafa aka ga Dalai Lama yana rungumar yaron.

    Daga nan ne ya miƙa wa yaron kumatunsa domin sumbata, sannan ya ƙara sumbatar shi a leɓɓansa alhali yana riƙe da hannuwansa.

  17. Ƴan sanda sun tarwatsa ƴan fashin daji a Zamfara

    Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta ce jami'anta sun tarwatsa wani yunƙurin ƴan bindiga na kai hari a wani ƙauye da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe.

    Haka nan jami'an sun samu nasarar hallaka ƴan bindigan guda biyu.

    A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Mohammed Shehu, ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, inda aka yi artabu tsakanin jami'an ƴan sandan da kuma maharan.

    Sanarwar ta ce baya ga waɗanda aka kashe, wasu maharan sun tsira da munanan raunuka.

  18. Yesu zai iya dawowa a kowane lokaci daga yanzu - Rabaran Mati

  19. ‘Ya kamata limamai da fastoci su daina cusa wa mabiya ƙiyayya’

    Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce wasu ƴan barandan siyasa na barazana ga tarihin Najeriya da na al’ummarta.

    A cikin wani saƙon taya murna na bukin Easter da Sarkin Musulmin ya aika wa shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, ya ce lamarin ‘aiki ne na Shaiɗan, wanda makircinsa mai rauni ne.’ Kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana.

    A cikin jawabin nasa, wanda ya samu sa hannun Mataimakin shugaban Majalisar Ƙoli ta Lura da Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Farfesa Salisu Shehu, Sarkin ya buƙaci shugaban na CAN ya haɗa hannu da Ƙungiyar ta Musulunci wajen ganin an rage yadda limamai da fasto-fasto ke cusa wa mabiyansu ƙiyayya ta siyasa da kuma munanan kalamai.

    Daga ƙarshe mai alfarma Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar Easter tare da addu’ar ci gaban Najeriya.

  20. Masu zanga-zanga na matsa wa gwamnati lamba a Tunisa

    Daruruwan masu zanga-zanga ne suka cika titunan birnin Tunis na Tunisiya, domin matsa wa gwamnati lambar sako wasu fitattun 'yan adawa 20, waɗanda ba su ga-maciji da shugaban ƙasar, Kais Saied.

    Tun a watan Fabrairu da ya wuce ne aka kama mutanen.

    Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ce babbar jam'iyar adawa ta National Salvation Front ce ta shirya zanga-zangar.

    Masu boren sun zargi shugaba Saied da tursasa 'yan kasa da salon mulkin danniya.

    A watan Yulin 2022 ne ya kori daukacin majalisar ministocinsa, tare da rushe majalisar kasar baki daya.

    Sai dai shugaba Kais ya ce wadanda aka kama din 'yan ta'adda ne, da suke barazana ga tsaron Tunisia.