Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta umarci INEC ta bayar da damar amfani da katin zaɓen wucin-gadi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Yawan mutanen da suka mutu ya kai shida a hatsarin jirgin ƙasa na Legas

  2. 'Yan bindiga sun kashe mutum shida tare da yin garkuwa da 50 a Neja

    'Yan bindiga sun kashe akalla mutum shida, ciki har da wata mata a ƙananan hukumomin Rafi da Wushishi na jihae Neja.

    Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutane sama da 50 tsakanin ranakun Talata da Laraba.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun yi wa al'ummomin Yakila da Hana-wanka da kuma Kundu ƙawanya har zuwa wayewar garin Laraba.

    Sai dai mazauna garuruwan sun ce daga baya dakarun sojin sama ta Najeriya sun kawo musu ɗauki, inda suka ɗauki sa'o'i da dama suna artabu da 'yan bindigar kafin su fatattakesu.

    Har ila yau, mazauna garin sun ce an kashe wasu ne lokacin da ake artabu tsakanin 'yan bindigar da kuma sojoji.

    Sun kuma ce an ɗauki gawarwakin waɗanda aka kashe zuwa Minna babban birnin jihar a safiyar ranar Laraba.

    Jihar Neja dai na cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar 'yan bindiga da kuma ta masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, inda sanadiyyar hakan mutane da dama sun rasa rayukansu da kuma ɗaiɗaita da yawa.

  3. An yi wa birnin Kharkiv luguden wuta cikin tsakar dare

    Jami'ai a Ukraine sun ce an shafe daren jiya ana ruwan makamai masu linzami a sassa daban-daban na kasar ciki har da birnin Kharkiv da yankin Odesa.

    Tun da fari an ji karar makamai masu linzamin a yankuna 13 na Ukraine.

    Bayanai sun ce gwamnan Kharkiv Oleg Synegubov, ya sanar cewa hare-hare ta sama 14 sun rusa wani ginin farar hula, da mummunan lalata ababen more rayuwa.

    Shi ma gwamnan Odesa Maksym Marchenko, ya ce an samu barna ba kadan ba, amma dai babu wanda ya rasu ko jikkata.

  4. Majalisar dokokin Faransa ta amince da tsawaita shekarun yin ritaya

    Da tsakar daren jiya majalisar dokokin Faransa ta kada kuri'ar amincewa da kara shekarun yin ritaya da shekara biyu, bayan makwannin da aka dauka ana zanga-zanga kin amincewa da matakin.

    'Yan majalisar da jam'iyyar Conservative ta mamaye, sun cimma wa'adin daren Lahadi na daukar matakin karshe kan sabuwar dokar da za ta kara tsawaita wa'adin ritaya ka dukkan ma'aikata na fannoni da dama a Faransa zuwa shekaru 64.

    Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron, ta ce ana bukatar yin sauyin domin ci gaba da tafiyar da tsarin biyan kudin fansho.

    Amma wani dan majalisa daga jam'iyyar adawa ya ce matakin ya mayar da Faransa baya da kusan shekaru 40.

    A ranar Laraba masu zanga-zanga sun janyo tsaikon motocin dakon mai, da jiragen sama da na kasa da kantunan sayar da kayan masarufi, har da tashar ruwa sakamakon toshe hanyoyi da suka yi.

  5. Barkan mu da safiyar Alhamis!

    Wannan shafin zai rinƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.