Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kunna fitilu domin ci gaba da zaɓe a wasu sasssan Najeriya

Wannan shafi zai rinƙa kawo uku abubuwan da ke faruwa game da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Yusuf Yakasai, Abdullahi Bello Diginza and Nabeela Mukhtar Uba

  1. BVAS na bayar da matsala a wasu sassan Maiduguri

    Yayin da harkokin zaɓe ke ci gaba da gudana a wasu sassan Najeriya lami lafiya, wasu ɓangarorin suna fama da matsaloli da dama.

    Kama daga rashin isar jami'an INEC a kan lokaci zuwa na rashin tsaro kamar a abin da ya faru a jihar Gombe.

    Sai dai matsalar da ake fsukanta a Maiduguri babban birnin Jihar Borno ta sha ban-ban da ta sauran jihohi.

    A Maidugurin matsalar na'urarar tantance masu kaɗa ƙuri'a ita ce ta ƙi aiki yadda ya kamata.

    Kazalika ana fuskantar rashin fitowar masu zaɓe kamar yadda mai turo wa BBC bayani daga Maiduguri, Adamu Aliyu Ngulde ya tabbatar wa BBC.

  2. Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri'arsa a Daura

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuria'a mazaɓarsa da ke garin Daura da ke jihar Katsina.

    Shugaban wanda ya fito da misalin ƙarfe 9:30 na safe ya kaɗa ƙuri'ar tasa ne tare da mai ɗakinsa A'isha Buhari.

    Muhammadu Buhari na kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas a wannan shekara, inda ake sa rana zai miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

  3. An samu jinkirin kai kayan zaɓe a wasu mazaɓu a Bauchi

    Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa an samu jinkirin kayan aiki a mazaɓar Madachi, a Kofar Fada da ke Ƙaramar hukumar Katagum.

    A mazaɓar Shagari da ke tsakiyar Bauchi ita ma ana fuskantar wannan matsala ta rashin kai kayan aiki a kan lokaci.

    Hakan abin yake a ƙofar gidan yari, kan kusurwar fada da sauran wasu wurare.

  4. An ware wa tsofaffi da masu ciki layi na daban a Oyo

    An fara kaɗa ƙuri'a a mazabar Iwo da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo.

    Tun da sanyin safiya ne masu kaɗa ƙuri'a suka isa rumfunan zaɓen domin kaɗa kuri'unsu.

    Yankin na cikin inda aka fara kaɗa kuri'a a kan lokaci a kusan faɗin Najeriya, ma'ana ba su samu jinkiri ba kamar yadda aka samu a wasu wurare da dama.

    Tun da fari an raba layukan masu zaɓen biyu domin sauƙaƙe komi, Layin farko na dattijai da mata masu ciki da kuma masu buƙata ta musamman.

    Layi na biyu kuma matasa ne masu jini a jika da kuma lafiyayyun mutane koda suna da shekaru.

  5. ICPC ta kama wani mutum da kuɗi 'da zai kai wa wani ɗan siyasa'

    Hukumar ICPC reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wani mutum ɗauke da kuɗi da suka kai naira miliyan biyu, ciki da sababbi da kuma tsofaffin kuɗin da aka sauya.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ta kama mutumin ne mai suna Hassan Ahmad da waɗannan kuɗaɗe duk da ƙaranci kuɗi da ake fama da shi.

    "An kama shi da naira dubu ɗari tara na sababbin kudin da aka sauya, yayin da sauran naira miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya suka kasance na tsofaffin kuɗi.

    "An shirya kuɗin ne cikin irin jakar nan ta buhu, kuma tuni mutumin ya amsa laifinsa ya na cewa kudin zai kai su jihar Gombe ne ga wani ɗan siyasa.

  6. Atiku ya kaɗa kuri'arsa

  7. Har yanzu jami'an INEC ba su kai kayan aiki a mazaɓar Tinubu ba

    Rahotanni da ke fitowa daga mazaɓar Etoi a ƙaramar hukumar Uyo na cewa har yanzu ana jiran jami'an hukumar INEC su isa wuraren zaɓen.

    Wannan ce dai mazaɓar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya kaɗa ƙuri'arsa a ciki.

    Duk da cewa masu zaɓe sun isa runfunan tun ƙarfe shidan safe amma sun ce har yanzu ba su ga ko ma'aikacin INEC ɗaya da ya iso wajen aikin ba.

    Akwai rumfunan zaɓe da BBC ta ziyarta a yankin, dukkansu suna fama da irin wannan matsalar suma.

  8. Ba za mu fara aiki ba sai an biya mu alawus, in ji ma'aikatan INEC

    Wasu ma'aikatan wucin-gadi na hukumar zaɓe a Najeriya sun ce ba za su fara aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a ba har sai an biya su wasu alawus-alawus ɗinsu.

    Ma'aikatan na Mazaɓar Ɗorayi Karama a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar, sun ce suna neman alawus ne na horaswar da INEC ɗin ta ba su.

    Wakilin BBC Hausa a Kano Zahradden Lawan ya ce yanzu haka masu zaɓe na can sun yi cirko-cirko suna jiran ikon Allah.

    Jihar Kano na da masu kaɗa ƙuri'a fiye da miliyan biyar, abin da ya sa jihar ta zama ɗaya daga cikin wuraren da 'yan takara suka fi kewayawa domin neman ƙuri'u.

  9. An fara kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓen Peter Obi

    An fara kaɗa ƙuri'a a mazaɓa ta 019, gundumar Amatutu ta 2, a garin Agulu da ke jihar Anambra, inda nan ne rumfar zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Peter Obi.

    Peter Nedum, mai shekara 81 shi ne mutum na farko da ya kaɗa ƙuri'arsa.

    Duk da barazanar tsaro da ake fuskanta a yankin kudu-maso-gabashin Najeriya, da alama mutane da dama sun fito domin kaɗa ƙuri'a.

  10. An samu jinkirin fara tantance masu kaɗa ƙuria'a a mazaɓar Atiku Abubakar

    Jinkirin da aka samu na isowar jami'an INEC a mazabar Ajiya inda nan ne ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, zai kada kuri'asa, a jihar ta Adamawa ta sa an samu ɗan jinkiri wurin fara tantance masu kaɗa ƙuri'a.

    Duk da cewa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta ce za a fara zaɓen ne da ƙarfe 8:30 na safe, jami'an zaɓen ba su iso ba sai kimanin ƙarfe 8:15am.

    Hakan ne ya sanya ba a samu nasarar fara tantance masu kaɗa ƙuri'ar a kan kari kamar yadda aka tsara ba.

  11. An kai wa jami’an zaɓe hari a Gombe

    Wasu da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun kai wa jam’ian zaɓe na wucin-gadi da aka tura wata rumfar zaɓe da ke cikin garin Gombe.

    Rahotanni sun ce maharan ɗauke da sanduna da adduna sun ƙwace wa ma’aikatan wayoyi da jakkunansu da wasu kayan aiki.

    Haka nan an garzaya da wasu daga cikin ma’aikatan zaɓen zuwa asibiti bayan sun samu raunuka.

    Wakilin BBC Hausa na wucin-gadi a Gombe Halilu Mohammed Teli ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare kuma yawancin waɗanda aka kai wa farmakin matasa ne masu yi wa ƙasa hidima.

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Gombe ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce sun kama wasu daga cikin maharan sannan sun fara gudanar da bincike kan abin da ya faru.

  12. Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar LP Peter Obi ya fito kaɗa ƙuri'arsa

  13. Zaɓen Najeriya 2023: 'Ina so Najeriya ta koma kamar yadda take a baya'

    Salisu Atiku, mai shekara 19 na daga cikin na farko-farko da suka fito domin kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe ta Tukuntawa da ke jihar Kano.

    Wannan ne karon farko da zai yi zaɓe, kuma ya ce ya ƙagu ya kaɗa ƙuri'arsa.

    Ya ce "Magabatanmu na ba mu labarin yadda Najeriya take da daɗi a shekarun baya, abin da nake fata shi ne ƙasarmu ta koma kamar yadda take a baya, shi ya sa zan yi zaɓe."

  14. 'Ina fatan ba za a yi mana maguɗi ba'

    Wannan shi ne Alase Adesina, wanda ya zama na farko a layin zaɓe a mazaɓar at St Agnes da ke Alagomeji a Mainland Legas.

    Ya shaida wa BBC cewa ya fito ne domin ya zaɓi ra'ayinsa a wannan zaɓe, yana kuma jin kishin ƙasarsa a kan hakan.

    "Ina cikin farin ciki matuka, ina jin daɗi kuma yanzu ina jira in jefa kuri'ata ne kawai. Ina kuma fatan kada a yi mana maguɗi."

    Ya shafe sama da minti 30 yana jira gabanin a fara batun zuwan sauran mutane har a zo maganar kaɗa kuri'a.

  15. Masu kaɗa ƙuri'a na sammakon bin layin zaɓe a jihar Kano

  16. Miliyoyin ƴan Najeriya na zaɓen sabon shugaban ƙasa

  17. Dokar hana zirge-zirga a Najeriya ta fara aiki saboda babban zaɓe

    Dokar takaita zirga zirgar ababen hawa ta fara aiki a sassan Najeriya yayin da ya rage ƴan sa'o'i a fara kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar.

    Tuni aka rufe kan iyakokin kasar, sojoji kuma sun fara zirga zirga musamman a yankunan da ake da matsaloli da suka danganci tsaro.

    An kuma kai kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan zaɓen a ƙarƙashin sanya idon jami'an tsaro.

    Akwai ƴan takara shugaban ƙasa 18 a zaɓen na yau.

    Sai dai wakilinmu na wucin-gadi daga jihar Neja ya ce dokar hana zirga-zirgar ba ta fara aiki yadda ya kamata ba, sai dai ya haɗu da jami'an tsaro a ɗaiɗaikun wurare.

  18. Facebook live: Shirin Safe na musamman kan zaɓukan Najeriya na 2023

    Muna kawo muku shiri kan zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin tarayya kai-tsaye a shafinmu na BBC Hausa facebook. Ku latsa kan bidiyon da ke ƙasa domin kallo kai-tsaye:

  19. Muhimman bayanai kan zaɓen shugaban Najeriya da ƴan majalisar dokokin tarayya

    Al’ummar Najeriya miliyan 93 ne ke shirin kaɗa ƙuri’arsu a yau a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya.

    Hakan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya shafe shekara takwas yana mulkin ƙasar daga shekarar 2015.

    Ga jerin jadawalin bayanai kan zaɓen:

    Akwai ƴan takara 18 waɗanda ke neman kujerar shugaban ƙasa, sai kuma kujerar sanatoci 109, da na mamabobin majalisar wakilan tarayya 360.

    Ƴan takarar shugaban ƙasa huɗu ne suka fi shahara a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa.

    Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), mai mulki.

    Atiku Abubakara na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

    Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Political Party (NNPP).

    Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP).

    Kujerun da ake takara:

    Inda za a kaɗa ƙuri'a:

  20. Zaɓen Najeriya 2023

    Rana ba ta ƙarya!

    Masu bibiyar mu a shafin BBC Hausa barkan mu da asuba. Da fatan an wayi gari lafiya. Yau ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya na 2023 a Najeriya, kuma wannan shafi zai kawo muku dukkanin abubuwan da ke faruwa a faɗin ƙasar game da wannan zaɓe, da ma wasu abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu tsawon wannan yini a shafinmu na bbchausa.com, da sahufukanmu na facebook da tuwita da instagram a @bbcnewshausa da kuma YouTube.

    Haka nan za ku iya sauraron shirye-shiryenmu na rediyo waɗanda muka tsawaita su saboda wannan zaɓe.