Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Majalisar dokokin Najeriya ta buƙaci ƙarin wata shida kan wa'adin amfani da tsoffin kuɗi

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Abdullahi Bello Diginza

  1. Na yi wa 'yan Najeriya iya koƙarina - Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya mulki Najeriya da iyakar ƙokarinsa, inda ya ce bai ba wa 'yan ƙasar kunya ba.

    Shugaban wanda ya je jihar Bauchi a cigaba da ƴaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC na shugaban ƙasa da kuma na gwamna, ya bayyana hakane lokacin da ya kai ziyara gidan Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu.

    Buhari ya ce dubban mutane da suke fitowa su tarbe shi a duk inda ya je hakan na nuna ƙarara irin soyayyar da ake masa.

    "Ina so na faɗa cewa tsakanin 2003 zuwa 2011, na kai ziyara dukkanin ƙananan hukumomin Najeriya, sannan a 2019, lokacin da nake neman sake komawa kan mulki ƙaro na biyu, na ziyarci dukkanin jihohi a faɗin ƙasar, mutanen da naga sun fito tarba ta, abu ne da ba zan iya misaltawa ba saboda dandazonsu, a lokacin na yi alkawarin mulkar Najeriya da 'yan Najeriya da iyaƙar ƙokarina kuma zuwa yanzu na san na yi ƙokari,'' in ji shugaban.

    Tun da farko a jawabinsa, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman, ya ce abu mai kyau ne idan shugabannin siyasa suka nuna girmamawa ga Sarakuna da kuma masarautu ta hanyar kai musu ziyara.

    Ya godewa shugaba Buhari kan irin ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a Bauchi, inda ya ce aikin haƙo man fetur na Kolmani, wani bu ne da 'yan jihar da ma arewa maso gabas ba za su manta ba.

  2. An sake kai hari a Kudancin California

    Kwanaki biyu bayan kashe mutum 12 a harin bindiga a Los Angeles, an sake kai wani harin a Kudancin California.

    A harin na jiya yan sanda sun tabbatar da kashe mutum bakwai a wasu gonaki biyu da ke Half Moon Bay.

    Ana kyautata zaton cewa mutanen da aka kashen yan kasar Sin ne mazauna Amurka da ke aiki a gonakin.

    Wakilin BBC ya ce wani mutum mai shekaru 67 ya mika kansa ga yan sanda duk da kawo yanzu ba a gano me yasa ya yi harbin ba.

  3. Brazil da Argentina na shirin samar da takardar kuɗi bai ɗaya

    Ƙasashen Brazil da Argentina sun sanar da shirinsu na samar da takardar kuɗin bai ɗaya da zimmar haɓaka kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu na Kudancin Amurka.

    Shugaba Lula da Silva da takwaransa Alberto Fernandez sun fada a Buines Aires cewa suna son bullo da hanyar samun karuwar arziki ba tare da dogaro da saye da sayarwa ta amfani da dalar Amurka ba.

    Mr Lula kenan yake cewa abunda za mu mayar da hankali a kansa shi ne muga cewa ministocin kudinmu sun lalubo hanyar cin moriyar amfani da takardar kudin bai dayan.

  4. An dawo da wutar lantarki a biranen Pakistan

    An mai do da wutar lantarki a wasu manyan biranen Pakistan, kwana daya bayan dauke ta a duka fadin kasar.

    Ma'aikatar makamashin kasar ta ce duka tashoshinsu 1,100 sun dawo aiki.

    Shi ne karo na biyu a watanni uku da aka samu daukewar wutar lantarki a duk fadin Pakistan.

    Pakistan na fuskantar matsalar daukewar wutar lantarki saboda tsofaffin kayan aiki da suka shafe shekara da shekaru ba a canza su ba.

    Hakan ya sa muhimman wurare da ba sa yi ba bu wuta kamar asibitoci dogara da inji don gudanar da ayyukansu.

  5. Buɗewa

    Ma'abota BBC Hausa Ahmad Tijjani Bawage ke muku barka da hantsin Talata.

    Ku biyo mu domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya.