'Yan sandan Australiya sun ce wani mutum mai shekara 77 ya rasa ransa bayan da wata babba da jaka ta kai masa hari wadda ya ajiye yana kiwatawa a gidansa.
Wani dan uwan mutumin ne ya same shi da munanan raunuka a jiya Litinin a gidansa da ke Redmond, kilomita 400 da kudancin Perth.
Lokacin da ma'aikatan motar daukar marasa lafiya suka isa gidan mutumin domin agaza masa, babba da jakan ta hana su ba wa mutumin taimakon da ya kamata.
'Yan sanda sun ce an tilasta musu yin harbi kafin kai wa ga mutumin, inda ya rasa ransa lokacin da ake harbe-harben.
Wani mai magana da yawun 'yan sandan, ya fada wa manema labarai cewa suna da yakinin cewa babba da jaka ce ta farwa mutumin a ranar - wadda dabbar daji ce.
Australiya na da babba da jaka sama da miliyan 50 a cikin kasar, da za su kai nauyin kilogram 90 da kuma ke girma na tsawon mita 2.
Sai dai ba kasafai ake samun babba da jaka da ke farwa mutane ba - wanda wannan ne karon farko da aka samu labarin ta kai wa wani hari tun shekarar 1936.
Babba da jaka na da sassan jiki da ke raunata mutane kamar kaifin hakora da kafafu masu karfi, a cewar wani masani kan dabi'un babba da jaka, Graeme Coulson, a wata hira da ya yi da wani gidan rediyon Australiya.