Daular Larabawa ta lalata makaman da 'yan Huthi suka harba mata
Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da gano tare da lalata wasu makamai masu cin dogon zango da ‘yan tawayen Houthi na Yemen suka harba mata.
Ma’aikatar tsaro ta ce babu wanda ya ji rauni a aikin sannan ɓurɓushin makamai masu linzamin sun faɗi ne a wani yanki da ba mutane da yawa a wurin.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya isa ƙasar a ziyara irinta ta farko a hukumance.