CAN ta dakatar da shugabanta na Gombe saboda taya Pantami murnar zama Farfesa
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta dakatar da shugabanta na jihar Gombe Sunday Congo, saboda wasikar da ya aika wa ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Internet na Najeriyar Isa Pantami, inda a ciki yake taya shi murnar zama Farfesa.
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga Satumba, da sakataren kungiyar Daramola Bade ya sanya wa hannu, ya sanar da dakatar da Mista Congo saboda zargin wuce gona da iri.
Sanarwar ta ce an fitar da sanarwar ne ba tare da amincewar shugabancinta na kasa ba.
“Biyo bayan sakin saƙon taya murna ga Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Internet Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, mun aiko maka wannan wasika don sanar da kai cewa abun da ka yi ya haifar da damuwa a tsakanin 'ya'yan wannan kungiya''.
Ta ce “Wannan ba dai-dai bane, ka yi ne ba tare da wani izini ba', don haka ana umartarka da ka bar mukaminka nan take''.Inji wasikar.