Bankwana
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muke bakwana da ku, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya yarda. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a huta lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya
Imam Saleh and Umaymah Sani Abdulmumin
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muke bakwana da ku, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya yarda. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a huta lafiya.
Mazauna karamar hukumar Kankara na jihar Katsina sun shiga rudani sakamakon kwararar 'yan bindiga da ake zargi daga Zamfara suke shiga yankin.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa 'yan bindigar na tserewa ne daga dazukan Zamfara inda ake musu luguden wuta zuwa kauyukan Katsina.
Wani mazaunin kauyen Pawwa, ya shaidawa jaridar cewa 'yan bindigar su dasa shinge inda suke binciker mutanen da ke wucewa tsakanin titin Kankara zuwa Zango.
"Babban bukatarsu shi ne batun abinci da man fetur. Suna dauke da jarkoki suna karbar mai daga masu ababen-hawa da kwace duk wani abinci da suka gani."
Mazauna yankin dai na ta kokarin ankarar da mahukunta musamman jami'an tsaro kan hadarin da suke ciki.
Titin Kankara zuwa Tsamiyar Na Baushe, Unguwar Malali, Zango Pawwa zuwa Dansadau na da iyaka da Zamfara.
Kakakin 'yan sanda Katsina, SP Gambo Isah, ya shaida cewa babu mamakin hakan na faruwa amma batun a yanzu ba wanda zaa yanke hukunci ba ne.
Rahotanni daga Najeriya na cewa ana zargin wata mata da hallaka 'ya'yan kishiyarta uku ta hanyar saka masu guba a cikin shayi.
Lamarin ya faru ne a garin Patiskum na jahar Yobe da ke yankin arewa masu gabashin Najeriya.
A yanzu haka matar na hannun ‘yan sanda kuma tuni suka soma bincike kan lamarin.
Akwai kuma ɗa namiji daya da mace biyu kwance a Aassibiti suna jinya.
Maigidan matar Alhaji Haruna ya tabbatar da faruwa al'amarin a wani tattaunawa da BBC, sannan ya ce yanzu haka sun sanar da mahukunta domin daukan mataki.
Kakakin ‘yan sandar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da mutuwar yaran, kuma ya shaida cewa yanzu haka suna kan bincike.
Wata kotu a Najeriya ta umarci likitoci da su kawo karshen yajin aikin da suke su kuma koma bakin aiki ba da bata lokaci ba.
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ta shafe kimanin mako shida tana yajin aiki lamarin da ya haifar da koma-baya a asibitocin gwamnati.
Likitocin sun ce za su yi nazari kafin su dauki mataki.
Sun dai shiga yajin aikin saboda rashin biyansu albashi da wasu alawus alawus. Sun kuma bukaci a rika biyansu alawus kan irin hadarin da suke fuskanta yayin aiki.
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya yi hannun riga da gwamnoni sha shida na kudancin kasar, bayan taron da suka gudanar kan batun karbar harajin VAT.
Gwamna Umahi ya ce bai amince jihohi su karbi harajin VAT ba, sai dai gwamnatin tarayya ta ci gaba da karba, kana kuma ta bawa jihohi.
Ta wata mahanga, mutane na cewa yunkurin gwamnonin kudancin kasar, wani mataki ne na nuna gazawar jihohin da basu da karfin tattalin arziki a fili ne.
To amma masana tattalin arziki sun ce akwai bukatar jihohin kasar su sake karatun ta natsu.
A saurari rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman.
'Yan sama jannatin China uku sun dawo duniya bayan sun shafe kwana casa'in a tashar sararin samaniya ta Tiangong mallakin China, wanda ya kasance lokaci mafi tsawo da 'yan sama jannatin kasar su ka shafe a tashar.
Tashar talabijin mallakin gwamnatin kasar ta nuna ma'aikata na hanzarin isa wurin da kumbon da ya dawo da 'yan sama jannatin ya sauka a cikin hamadar Gobi.
China na shirin aikawa da wani ayarin 'yan sama jannatin har sau uku kafin karshen shekara mai zuwa domin su fadada tashar, wadda ake sa ran za ta ci gaba da zagaya duniyarmu har na tsawon shekara goma masu zuwa.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta China, Zhao Lijian ya ce yana alfahari bayan da ya kalli dawowar kumbon zuwa duniya a talabijin, kuma yana wa jaruman na sararin samaniya su uku maraba da dawowa gida.
Jam'iyyar APC da ke mulkin Najeriya ta ce babu wani mamba cikin sabbin mutanen da suka koma jam'iyyar da za a bawa tiketin takara kai-tsaye, ko da kuwa Goodluck Johnthan ne a zaben 2023.
A wata sanarwa da suka fitar ranar Juma'a, sakataren kwamitin riko na jam'iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe ya ce tattaunawarsa da Talabijin Channels a ranar Laraba ba ta shaida cewa za a bawa Jonathan takara kai-tsaye ba.
Sanarwar ta kuma kara da cewa dukkanin mambobin jam'iyyar za su samu gajiya da damamaki da kowa zai samu.
APC ta kuma ce dole kowanne dan takara ya bi tsari wajen neman takara da amincewa jam'iyyar ta tsayar da shi.
Manyan kamfanonin fasahar sadarwa biyu, Google da Apple sun sauke manhajar nan ta sa ido kan zaben kasar Rasha daga shagunansu na intanet a cikin kasar.
Makarraban Alexei Navalny, wato mutumin da ke adawa da gwamnatin Vladimir Putin sun bayyana bacin ransu, suna cewa ana toshe bakin al'ummar kasar ne domin hana su bayyana ra'ayinsu.
Wani cikin jami'an da su ka gudanar da yakin neman zaben Mista Navalny a shekarar dubu biyu da goma sha takwas ya ce fadar shugaban Rasha, Kremlin ta ce za ta fara kama ma'aikatan Google da Apple idan ba su sauke manhajar ba.
Wani makusancin kamfanin Google ya shaida wa BBC cewa tilas kamfanin ya sauke manhajar saboda hukumomin Rasha na barazanar muzgunawa ma'aikatansa.
Babban bankin Najeriya wato CBN ya ce yana neman mai shafin canji na AbokiFX, Oniwinde Adedotun ruwa a Jallo.
AbokiFX shafin ne da ke wallafa bayanai kan yanayin hada-hada da yada ake sauya kudaden ketare akan naira a kasuwanni bayan-fagge.
A lokacin da ya ke amsa tambayoyi a taron manufofin kudi karo na 280 a hedikwatar bankin da ke Abuja, gwamnan Bankin Godwin Emefiele ya ce mai shafin AbokiFX na gudanar da harkokinsa ta haramtacciyar hanya.
Ya ce za a gurfanar da shi kan jefa tattalin arzikin Najeriya cikin barazana.
A cewar gwamna Emefiele, Mista Oniwinde ya soma shafin AbokiFX a 2015, kuma tun daga wannan lokaci ya ke zagon-kasa ga tattalin arzikin kasa ta hanyar amfani da shafin ta mumunar hanya.
''Oniwinde tun daga inda ya ke rayuwa wato Landan, ya ke aikata muggan laifuka ga tattalin arzikinmu.''
A cewar Godwin CBN kadai ke da damar yanke hukunci kan darajar Naira, don haka ya sha alwashin kamo Oniwinde domin fuskantar shari'a.
Majalisar kasar Albania ta amince da kafa sabuwar gwamnati a kasar wadda firaminista Edi Rama ke jagoranta -- wadda kuma a karon farko -- ke da ministoci da yawancinsu mata ne.
Mutum goma sha biyu cikin ministoci goma sha bakwai mata ne -- cikinsu har da ministar kudi da ta harkoki da kasashen waje.
Gabanin majalisar ta kada kuri'a, Mista Rama ya ce yakin da ake yi da ma su nuna bambanci ga mata da kuma yadda ake cin zarafinsu bai kare ba, yana cewa da sauran aiki a gaba.
Wasu 'yan kasar sun soki firaministan, su na cewa yana amfani da batun kiyaye hakkin mata ne kawai domin dalilai na siyasa.
Majalisar Dinkin Duniya a Habasha ta ce sama da manyan motoci dari hudu da suka kai kayan agaji zuwa yankin Tigray da yaki ya shafa ba su dawo ba.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce motoci talatin da takwas ne suka dawo tun watan Yuli, abin da ke kawo cikas ga ayyukan jin kai.
Hukumomin Tarayyar Habasha sun ce 'yan tawayen Tigraya sun kwace manyan motocin.
'Yan kabilar Tigraya sun ce rashin man fetur yana hana dawowarsu.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu dari hudu da arba'in a Tigray suna rayuwa cikin yanayin yunwa.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sa hannu kan wani umarni da za ta ba da damar ƙaƙaba takunkumi kan mutane da ƙungiyoyin da ke ta da husuma tare da lalagta ayyukan tsaro a Habasha.
Sai dai ba a ambaci sunan kowa ba kawo yanzu.
Amma wannan ne gargaɗi mafi tsauri da gwamnatin Amurka ta yi wa masu cin zarafin bil Adama ko masu hana ayyukan agaji a Habasha.
Haka kuma, Shugaba Biden ya yi kira kan duka ɓangarorin da ke da hannu a rikicin yankin Tigray da ke arewaci da su yi sulhu.
Babbar kotun Afirka ta Kudu ta yi watsi da yunkurin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma na neman a soke hukuncin zaman gidan yari na watanni goma sha biyar da aka yanke masa.
Dan shekaru saba'in da tara a duniya, ya shaida wa kotun cewa hukuncin ya wuce gona da iri, kuma gidan yarin zai jefa lafiyarsa cikin haɗari.
Mista Zuma - wanda ke asibiti yana murmurewabayan yi masa tiyata - an daure shi saboda kasa bayar da shaida a binciken cin hanci da rashawa.
Ya musanta aikata ba dai-dai ba.
Tsare shi da aka yi a watan Yuli ya haifar da tarzoma wadda ta yi sanadin mutuwar sama da mutane dari uku.
Wata babbar kotu a jihar Oyo da ke a birnin Badun, arewa maso yammacin Najeriya ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya diyyar naira biliyan 20 ga matashin nan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, a matsayin diyyar barnar da jami'an tsaron farin kaya na DSS suka yi masa yayin wani sumame da suka kai gidansa.
Dan rajin awaren na yankin kudu maso yamamcin Najeriya na hannun hukumomin Benin a halin da ake ciki tun bayan tserewarsa lokacin da jami'an na DSS din suka dira a gidansa da tsakar dare.
DSS dai ta bayan kwashe tsawon lokaci tana musayar wuta da wasu mutane da ta tarar a gidan lokacin da jami'anta suka isa, ta samu nasarar kama tarin manyan makamai a gidan, wadanda aka mallaka ba bisa ka'ida ba.
Bayan tserewar Igboho din ne sai lauyoyinsa suka maka hukumar ta DSS da ministan shari'a na Najeriya a gaban kuliya, inda a madadinsa, suke neman a biya shi makudan kudade saboda take hakkinsa na dan kasa.
Jaridar Punch Nigeria ta ce a hukuncin da aka yanke a yau Juma'a alkalin kotun ya umarci a biya Igboho Naira Biliyan 20 a matsayin diyya, kasa da abun da lauyoyinsa suke nema tun da farko.
Tawagar masana kimiyya daga Oman sun fara binciken wani babban kogo a Yemen da aka fi sani da Rijiyar Barhout a karon farko.
Babban ramin yana cikin hamadar al-Mahra.
An dade ana alakanta wajen da abubuwan ban tsoro, har ta kai ga ana yi masa kirari da Jahannama.
Wasu labaran ma da aka rika bayarwa na cewa nan ne aka daure tarin aljanun duniya da dama.
Hotunan da masana kimiyyar suka fara aikowa sun nuna tarin macizai, da kwaɗi da da ƙudan zuma cunkus a makeken kogon, baya ga wasu irin halittu da tsayinsu ya zarce mita 9.
Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce 'yan Najeriya za su san sunayen masu dauakar nauyin ta'addanci a lokacin alokacin da ya dace.
Yana magana ne yayin wani shirin siyasa na tashar talabijin ta Channels jiya Alhamis.
Bawa, wanda ya fadi lokacin da yake jawabi a fadar shugaban kasar a jiyan, ya ce likitoci sun shaida masa cewa bashi da wata matsala, don haka a yanzu ya murmure.
''Makoshi na ne ya dan bushe, sai likitoci suka bukaci in sha ruwa sosai, daga baya kuma na wartsake ba wata matsala yanzu'' inji shi.
Wasu mazauna unguwar Birshin Fulani, da ke cikin garin Bauchi, sun tare hanyar Bauchi zuwa Dass suna zanga-zangar tabarbarewar tsaro a yankin.
A halin yanzu masu ababen hawa na nan jibge a kan hanya sakamakon lamarin.
Kusan makonni biyu da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin inda suka kashe mutane biyu, ciki har da wani babban ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Bauchi, Malam Abubakar Muhammad.
An kuma yi garkuwa da wasu mutane a harin.
Kwanaki kadan bayan faruwar lamarin ne aka kara sace wasu mutane.
A yau ne ƴan ƙasar Rasha za su soma jefa ƙuri'a a zaɓen ƴan majalisar ƙasar da za a shafe kwana uku ana yi.
Ana sa ran Jam'iyya mai mulki a ƙasar ta Russia Party wadda shugaba Putin ke ciki za ta lashe zaɓukan duk da halin da ƙasar take ciki na matsin tattalin arziki.
Ba a bar Ƴan adawa da dama da jam'iyyun siyasa ba su tsaya takara, haka kuma masu sa ido kan zaɓe na ƙasa da ƙasa kaɗan ne aka bari su sa idon.
Abin da za a fi mayar da hankali a kai shi ne adadin jama'ar da za su fita zaɓen da kuma ganin ko jam'iya mai mulki za ta samu rinjaye a zaɓen. Za a gudanar da zaɓen a rumfunar zabe da kuma ta intanet domin gudun yaɗa cutar korona
Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya daga 2015 zuwa 2019 ya koma babban jam'iyyar adawar kasar PDP.
Sani, wanda aka zaba a matsayin sanata a karkashin jam'iyyar APC bai samu damar komawa majalisar dattawa ba a shekarar 2019.
Rigimar da ke tsakaninsa da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ce ta tilasta masa ficewa daga jam'iyyar zuwa PRP, daga nan kuma ya koma PDP a yanzu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa kwanan nan sanatan ya bar PRP amma ya haye kan katanga.
Babban hadiminsa, Malam Suleiman Ahmed, ya ce, "Sanata Shehu Sani ya yanke shawarar komawa PDP, amma za a yi bikin karbarsa a hukumance ne nan da makonni biyu masu zuwa"
Ya ce Sani ya tabbatar da sauya shekarsa a ranar Alhamis, 16 ga Satumban 2021, lokacin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na PDP a Kaduna.