Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abba Kyari: Shugabannin duniya sun yi wa Buhari ta’aziyya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Jana'izar Abba Kyari

    A cewar Bashir Ahmad, mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen zumunta, za a yi jana'izar Malam Abba Kyari a yau Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada - na binne marigayi a ranar da ya mutu.

    Bashir ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter.

    Malam Abba Kyari ya rasu ne a daren Juma'a sakamakon cutar korona da ya yi jinya a Jihar Legas.

  2. Ko cutar korona ka iya tilasta dage zaben Amurka?

    Yayin da annobar cutar korona ke kara addabar tattalin arzikin Amurka, tana kuma fara kawo shakku game da zaben shugaban kasa, wanda za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

    Tuni aka katse zabukan fitar da gwani na jam'iyyu tare da rufe wuraren kada kuri'a, sannan 'yan siyasa suka shiga rikicin kwatar iko a siyasance a majalisa da kotuna.

    A watan Nuwamaba ne ake sa ran Amurkawa za su fita filin jefa kuri'a domin zabar shugaban kasa da wasu 'yan majalisa da kuma dubban mukamai a jihohi.

    Sai dai yadda ranar zaben za ta kasance - ko da ma an yi shi a ranar da aka tsara - ita ce tambayar da aka fara tayar da jijiyoyin wuya a kanta.

    Bisa tanadin kundin tsarin mulkin Amurka da aka yi tun shekarar 1845, ana gudanar da zaben shugaban kasa ne a duk Talata ta gaban kowacce Litinin din watan Nuwamba a cikin kowadanne shekara hudu - 3 ga Nuwamban 2020.

    Wannan ba zai sauyu ba sai Majalisar Wakilai da ta Dattawa sun yi zama na musamman sannan sai mafi rinjaye na majalisun biyu sun amince.

    Wakilin BBC Anthony Zurcher ya ce da wuya 'yan majalisar su yarda da wannan sauyi - jam'iyyar adawa ta Democrat ce ke da rinjaye a Majalisar Wakilai, yayin da jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump ke da rinjaye a Majalisar Dattawa.

  3. Ahmed Lawan da Mele Kyari sun yi ta'aziyya

    Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan ya yi addu'ar "Allah Ya ji kan Abba Kyari, Ya yafe masa kura-kurensa.

    Ahmed Lawan ya kara da cewa "Allah Ya sa Aljannatu Firdaus ce makomarsa," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    Shi ma shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC, Mele Kyari ya mika ta'aziyyarsa a shafinsa na Twitter, inda ya ce Abba Kyari "mutumin kirki ne kuma mai kaunar Najeriya".

    "Allah Ya yi masa rahama", a cewar Mele Kyari.

    Abba Kyari ya rasu ne a Jihar Legas a daren Juma'a bayan ya yi jinyar cutar korona.

  4. Idan ba ku san wane ne Abba Kyari ba...

    An haifi Malam Abba Kyari, wanda dan kabilar Kanuri ne, a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Ya yi karatun firamare da sakandare a jihar ta Borno, amma ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Warwick da ke Ingila a fannin halayyar dan Adam, wato Sociology a 1980.

    Kazalika ya sake kammala wani digirin a fannin Shari'a a Jami'ar Cambridge.

    A shekarar 1983, ya zama lauya bayan ya halarci makarantar koyar da aikin lauya ta Najeriya, wato Nigerian Law School.

  5. Salon aikin Abba Kyari...

    A matsayinsa na shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyara yana da ruwa da tsaki a kan kusan komai da ya shafi shugaban kasar.

    Shi ne mutumin da yake tsara komai game da ayyukan shugaban kasar, sannan yakan gana da akalla mutum 20 a kowacce rana, a cewar wasu ma'aikatan fadar ta shugaban Najeriya.

    Wani dan jarida da ke dauko rahotanni a fadar shugaban Najeriya, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa a kullum Abba Kyari yana gana wa da Shugaba Buhari akalla sau hudu.

    Kazalika yana ganawa da gwamnoni da ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati wadanda ke son gana wa da shugaban kasa.

  6. Atiku ya yi ta'aziyyar Abba Kyari

    Mutane na ci gaba da alhini tare da yin ta'aziyyar marigayi Abba Kyari, Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya, wanda ya mutu a daren ranar Juma'a.

    Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ce ya kadu da rasuwarsa tare da yi masa addu'ar "Allah Ya sa Aljnna ce makoma".

    "Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un. Na kadu da rasuwar Shugaban Ma'aikata, Abba Kyari. Allah Ya bai wa iyalansa hakuri, Ya yafe masa sannan Ya saka shi a Aljanna Firdaus. Ameen," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    Abba Kyari ya rasu ne bayan ya yi jinyar cutar korona a Jihar Legas.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a Umar Mikail ke muku barka da safiyar Asabar, da fatan kun tashi lafiya.

    Ku biyo mu domin samun bayanai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da ma duniya baki daya.