Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai kan yadda aka yi 'juyin mulki' a Zimbabwe

Ku kasance da shafinnan domin bayanai kai tsaye game da rikicin siyasar Zimbabwe.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan

  1. Tankokin yaki a titin Harare

    Da alamar sojoji suna sintiri a kan titunan babban birnin kasar Zimbabwe, Harare.

    Hotunan da aka dauka da safiyar Laraba sun nuna manyan tankokin yaki da sojoji suna karkatar da akalar ababen hawa ko kuma hana su wucewa.

  2. Shin wannan shafin Twitter na ZANU PF ne?

    Ana yada jita-jita kan waye ne yake sarrafa wannan shafin na Twitter, wanda yake ikirarin cewa na jam'iyyar Zanu-PF mai mulki ne.

    Shafin wanda ba a tantance shi a hukumace ba ya yi mubaya'a ga Emmerson Mnangagwa, mataimakin shugaban da aka kora.

  3. 'Sa ido kan abin da zai faru da Grace Mugabe'

    Editan BBC na Afirka ya ce yana da kyau a sa ido kan abin da zai iya faruwa da matar Robert Mugabe, Grace, wadda ya bayyana a matsayin 'ainihin makiyiyar' bangren Emmerson Mnangagwa , mataimakin shugaban da aka kora wanda Zanu PF ta sanar a matsayin shugaban riko a cikin wani jerin sakonnin Twitter.

  4. Jam'iyyar da ke mulkin Zimbabwe ta ce babu juyin mulki

    An wallafa wasu jerin sakonnin a wani shafin Twitter da aka ce na jam'iyyar ZANU PF mai mulki ne.

    Sakonnin sun ce ba juyin mulki aka yi ba. Sun ce mika mulki aka yi ba tare da zubar da jini ba. Sai dai babu tabbacin wane ne yake sarrafa shafin na Twitter.

  5. 'Lamarin na da alamun juyin mulki'

    Duk da bayanan da sojin kasar da jam'iyyar ZANU PF mai mulki ta yi, wakiliyar BBC Shingai Nyoka ta ce yanayin na da "dukkan alamun juyin mulki."

    "Akwai bude wuta da kuma tashin abubuwa masu fashewa a unguwanni da dama cikin dare, ciki har da wuraren da manyan jami'an gwamnati suke zaune da kuma inda gidan Shugaba Mugabe da kansa yake.

    "Sojin dai ta ce yana cikin halin lafiya kuma sun tabbatar da cewa zai kasance cikin tsaro.

    "Sun ki yarda cewa juyin mulki ne domin ba su karbi iko ba. Sun ce sun yi hakon mutane da ke kewaye da shi ne kuma za su mayar da shi shugabancin kasar da zarar sun kammala aikinsu."

  6. 'Mugabe Shugaba ne na suna kawai'

    Wani tsohon mai bayar da shawara ga madugun 'yan adawar Zimbabwe Morgan Tsvangirai, ya shaida wa BBC cewa shi ya yi imanin cewa ikirarin da soji ta yi na cewa ba ta yi juyin mulki ba ba gaskiya ba ne.

    "Sun ki su kira shi juyin mulki ne saboda sun san ba a son juyin mulki, za a yi Allah-wadai da shi," in ji Alex Magaisa.

    "Amma in ana maganar iko ne, a bayyane take cewa Shugaba Mugabe shugaba ne na suna kawai, kuma iko na tare da soji."

  7. Jam'iyyar hamayya ta MDC ta yi kira a koma tafarkin dimokradiyya cikin lumana

    Jam'iiyyar hamayya ta Zimbabwe, MDC, ta yi kira da a koma kan tafarkin dimokradiyya da tsarin mulki cikin lumana bayan 'karbe ikon sojin'.

    MDC, babbar jam'iyyar da ta kalubalanci jam'iyyar ZanuPF ta Mugabe a shekaru 20 da suka gabata, ta kuma ce tana fatan matakin sojin zai sa a kafa kasa mai bin tafarkin dimokradiyya mai dorewa, in ji kamfanin dillancin labaran Reuters.

  8. 'Masu laifi' kusa da Mugabe

    Sanarwar ta kara da cewa: "Muna hakon masu laifi kusa da shi[Mr Mugabe] wadanda suke aikata laifuka".

    Sanarwar ba ta ambaci wadanda aka yi hako ba, amman wata majiyar gwamnati da Reuters ta ambato ta ce ministan kudi, Ignatius Chombo, na cikin wadanda aka tsare.

    Babu tabbacin wanda yake jagorantar matakin sojin.

  9. Shin juyin mulki sojojin Zimbabwe suka yi?

    Rundunar sojin Zimbabwe ta karbe iko da babbar kafar yada labarai ta kasar, ZBC.

    A wata sanarwa, rundunar sojin ta ce ta dauki matakai ne kan masu laifi, amma ta musanta cewa abin da ta yin karbe mulki na soji ne daga hannun farar hula.

    Ta ce Shugaba Robert Mugabe yana cikin halin lafiya, amman ba ta fadi ina yake ba. Za mu kawo muku bayanai da dumu-duminsu.