Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon nan

An wallafa

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 22 ga Mayu zuwa Asabar 28 ga watan.

Kisan Harira da ƴaƴanta huɗu a Anambra

Ƴaƴan Harira da ƴan bindiga suka kashe a Anambra

Asalin hoton, HARIRA JUBRIL

Bayanan hoto, Ƴaƴan Harira da ƴan bindiga suka kashe a Anambra

Kisan Harira da ƴaƴanta huɗu a jihar Anambra kudancin Najeriya ya ja hankalin ƴan Najeriya mumman ƴan arewacin ƙasar.

A makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kai hari suka kashe mutum 12, ciki har da mace mai ciki wata tara, Harira Jibril da ƴaƴanta huɗu.

Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkaninsu mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawowa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

Mijin marigayiyar ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

"Na shiga tashin hankali, saura kaɗan na haukace - kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji," in ji Jibril Ahmed mijin matar.

A sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar bayan kisan Harira, shugaba Buhari ya yi da Allah-wadai da "kisan gilla da ake yi wa mutanen da ba su ji ba su gani ba" a Kudu maso gabashi da ma sauran sassan ƙasar.

Ya bayyana irin waɗannan kashe-kashe a matsayin "masu matuƙar ɗaga hankali", tare da gargaɗin masu aikata hakan da cewa su tsammaci tsattsauran martani daga jami'an tsaro.

APC da PDP sun fitar da ƴan takarar gwamna a jihohin Najeriya

Yan takarar gwamna

Manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya, APC da PDP sun fitar da ƴan takarar gwamna da na ƴan majalisar tarayya da jiha.

A ranar 26 jam'iyyar APC mai mulki ta yi zaɓen fitar da ƴan takarar mukamin gwamna a jihohin Najeriya

Zaben ya gudana lami lafiya a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma aka fuskanci turjiya daga wasu `yan takara.

A ranar 25 ga watan Mayun 2022 ne aka gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamnonin babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP inda aka yi gumurzu tsakanin ƴan takara da dama.

Duk da cewa an yi zabe a kusan duka jihohin, amma akwai wuraren da aka yi maslaha kamar Jihar Sokoto.

INEC ta tsawaita lokacin zabukan fitar da gwani

Inec

Asalin hoton, Inec

Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tsawaita lokutan zaɓe tare da kara lokacin zabukan fitar da gwani.

Wannan na zuwa yayin da jam'iyyar APC mai mulki ta dage lokacin gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa.

Hukumar INEC ta ce ta kara tsawaita lokacin ne bayan tattaunawa da shugabannin jam'iyyun siyasa 18 da aka yi wa rijista.

Kwamitin ba da shawarwari tsakanin jam'iyyu ne ya nemi a kara wa'adin mako guda ga jam'iyyun domin kammala zabukansu na fidda gwani.

Shugaban kwamitin Injiniya Yabagi Yusuf Sani ne ya nemi INEC ta dage ainihin lokacin da ta sanya na farko na ranar 3 ga watan Junin gobe.

Kotu ta ce Jonathan na da ƴancin yin takarar shugaban ƙasa

Jonathan

Asalin hoton, AFP

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Yenegoa babban birnin Bayelsa ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai iya takarar shugabancin ƙasar

A ranar Juma'a ne kotun ta zartar da hukuncin.

Sai dai Jonathan bai fitar da wata sanarwa ba da ke nuna cewa zai tsaya takara.

Ko a kwanakin baya sai da gamayyar kungiyoyi a arewacin Najeriya suka saya wa Jonathan tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar APC, duk da cewa Jonathan ɗin ya nesantar da kansa daga tikitin.

EFCC ta kama Rochas

Inec

Asalin hoton, Inec

A ranar 25 ga watan Mayu EFCC ta kama Rochas Okorocha a gidansa da ke Abuja, tana ikrarin cewa ya karya belin da aka bayar a kanshi tun da farko.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja kuma ta yi watsi da bukatar neman belin tsohon gwamnan na Jihar Imo.

Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya jagoranci zaman a ranar Juma'a, bayan sauraron bukatar lauyan Rochas, Ola Olanipekun.

Lauyan ya nemi kotun ta bayar da belin, na wani dan lokaci kuma na talala kafin a gabatar da binciken EFCC.

Ekwo ya ɗage zaman kotu zuwa ranar 30 ga watan Mayu, ranar da za a saurari kararsa da EFCC ta shigar.

Dala ta ƙara tsada

Dalar Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Dalar Amurka ta ƙara tsada idan aka kwatanta ta da nairar Najeriya, inda a karon farko a tarihi aka sayar da dala ɗaya a kan naira 610 a kasuwar bayan fage.

Sai dai duk da haka, dalar ba ta sauya farashi ba a hukumance a kan naira 419.

Amma ƴan ƙasar da dama da suka dinga ƙaroafi a kan hakan sun bayyana damuwa a kan yadda dalar ba ta samuwa a hukumace daga bankuna ko da mutum yana da sahihan takardun yin tafiya wata ƙasa, damar da gwamnati ta bayar za a iya ba mutum.

Mutane da dama da BBC Hausa ta zanta da su sun nuna matuƙar damuwa kan wannan hawa da dalar ta sake yi, sun kuma bayyana takaicin da suke ji na yadda dalar ba ta samuwa ta daɗin rai.

Kazalika mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta kan wannan tashin gwauron zabi da dala ta yi a kan naira a makon nan.

Lamarin tashin dala abu ne da yake taɓa kowa a ƙasar, saboda a kowane lokaci dalar ta tashi to sai an samu ƙaruwar farashin abubuwan yau da gobe ko da kuwa wanda ake kasawa a titi ne.