Gobara ta kashe jarirai sabbin haihuwa 11 a wani asibiti da ke Senegal

Shugaban Senegal Macky Sall

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Macky Sall ya ce gobarar ta tashi ne a sashen haihuwa da ke asibitin
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Senegal Macky Sall ya ce jarirai sabuwar haihuwa sha daya ne suka mutu sakamakon tashin gobara a wani asibiti da ke yammacin birnin Tivaouane.

Shugaba Sall ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa gobarar ta tashi ne a sashen haihuwa na asibitin Mame Abdou Aziz Sy Dabakh.

'Yan siyasa a Senegal sun bayyana cewa matasalar wutar lantarki ce ta haddasa tashin gobarar.

Magajin birnin, Demba Diop Sy, ya ce an yi nasarar kubutar da jarirai uku daga gobarar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

Mr Say ya shaida wa manema labarai cewa wutar ta yadu cikin gaggawa, yayin da jami'an kashe gobara ke wajen domin kashe ta.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato kafar yada labaran kasar na cewa ba a jima da bude asibitin ba.

A sakon ta'aziyya da Shugaba Macky Sall ya wallafa, ya taya iyalai da 'yan uwan jariran jimami, yana mai cewa "Ina yi wa iyaye da 'yan uwan jariran ta'aziyya, lallai lokaci ne mai matukar wuya."

"Wannan lamari mai tayar da hankali ne da bakin ciki kuma abin da ciwo," in ji Ministan lafiya Abdoulaye Diouf Sarr, wanda yake birnin Geneva domin halartar taron da Hukumar Lafiya ta Duniya.

Ya kara da cewa za a fara gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba, kuma ya katse ziyarar aikin da yake yi domin komawa gida Senegal ba tare da bata lokaci ba.

Gobarar dai ta janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta, kan halin da fannin lafiyar Senegal ke ciki.

Wani dan majalisa na jam'iyyar adawa, Mamadou Lamine Diallo, ya wallafa wani sako a shafinsa na Tuwita inda ya ke sukar gwamnati da cewa: "Tarin jarirai sun mutu a gobarar asibitin gwamnati… wannan abu ne da ba za a amince da shi ba".

A shekarar da ta gabata ma lamari irin wannan ya faru a wani asibiti da ke arewacin garin Linguère, inda jarirai hudu sabuwar haihuwa suka mutu a gobarar da ta ytashi a sashen haihuwa na asibitin. A wancan lokacin, magajin birnin ya ce matsalar wutar lantarki aka samu a na'urar sanyaya dakin haihuwar, kuma ita ce ta haddasa tashin gobarar.

Lamarin dai ya janyo an yi ta kiraye-kiraye ga gwamnati, kan mutuwar wata mata da ke nakuda mai suna, Astou Sokhna, wadda ta mutu bayan ta yi ta rokon likitoci su taimaka su yi mata tiyata sakamon shafe awa 20 ta na matsananciyar nakuda, daga karshe jaririn da ke cikinta shi ma ya rasu.